← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 108

Sashe 87

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

unda na jikinta sun baci." Yace."Bari na koma gidan yanzu." Hannunta ya saki da sauri ya fita daga dakin........Suna tsaye ita da rashida nurses din suka fito daga wani daki sun shirya baby tsaf da ita cikin kayan sanyi tana kamshin turare me dadi.....Hajja ta sanya hannu ta karbeta sai washe baki take tana musu godiya........daya daga cikin narses din ta tsaya kusa da Wasila tana mata magana......bude idanunta tayi tana kallon narse din da kyar tace."jiri ne kawai ke damuna sai bacci." Nurse din tace"To bari na taimaka miki muje toilet na gyara miki jikinki sai ki kwanta kafin Dr ya shigo." Daga kanta tayi narse din ta kama hannunta suka mike tsaye a hankali a hankali suka nufi toilet din dake cikin dakin.......ma dai-daicin ruwan dumi narse din ta hada mata ta zaunar da ita a jikin ruwan kana ta samu towel mai tsafta da wani ruwan d'umin tana dan danna mata jikinta.........Fitowa tay daga toilet din wanda yayi dai-dai da shigowarsa dakin hannunsa rike da ledoji Hajja tace"Yawwa kayan ne ko."? Yace."Sune Hajja ina take.'? ya fada yana rarraba idanunsa a dakin....Hajja tace "Tana bandaki." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya dan tsaya kusa da rashida yana le'ka fuskar babyn tashi.....Hajja ce ta karbi kayan hannunsa ta mikawa nurse din ita kuma ta kar'ba ta daukar mata riga da zani na atamfa da pants da audiga guda biyu, ta juya da sauri ta koma toilet din

Rashida ta mi'ka masa babyn tana murmushi tace"Yayana kamarku daya da yarinyar na dauka ma zata dauko kammanin anti na saboda wuyar data bamu kafin tazo duniya." Murmushi yayi ya karbi yarinyar yana kallonta yace."naji dadi da tayo kammanina rashida nima ai nasha wuya kafin na sameta."
Rashida na cike da farin ciki tace"Ubangiji Allah ya rayata ya bawa mamanta lafiya." Ya amsa da "ameen lokacin da yake kara bakinsa kunnan yarinyar yana mata hud'uba gami da kiran sallah.

Ganin nurse din ta fito da ita daga toilet din a kimtse gashi tana tafiya da kafafunta sai ya sauke ajiyar zuciya yana sake godewa Allah da ya sanya komai yazo cikin sauki.......Dr ne ya shigo yace." Yallabai zamuje yanzu a dauki jinin." Sai yay gaggawar mikawa rashida babyn dake hannunsa suka fita daga dakin tare da dr din.....Rashida da hajja suka nufi gadon da Wasila ke kwance suna sake yi mata sannu, kai kurrum take iya daga musu bakinta ya mutu murus har yanzu tana tuno irin bakar wuyar da tasha acikin awannin da suka gabanta, rashida ta dan zauna kusa da ita a hankali tace"Anti wasila baki dauki babyn ba." idanunta ta bude a hankali take kallon rashidan da babyn tayi murmushi a hankali tace "Rashida yarinyar na kama da babanta ko."? Rashida tasa dariya tana kallon Hajja tace" Eh mana nida hajja ma haka muka ce." Murmushi ta sakeyi ta rufe idanunta a hankali tace"Allah yayi mata albarka." Rashida da hajja suka amsa da "ameeen"

Bacci me nauyi ne ya dauketa wanda tana baccin dr yazo yayi aikinshi ya gama ya fita Amadu kam fita yayi harabar asibitin ya dinga kiraye kirayen waya yana shaidawa 'yan uwa da abokanan arziki karuwar da ya samu.

Karfe bakwai na safe Khalifa da matarshi suka shigo asibitin..........Khalifa ya dauki babyn ciki da farin ciki yake mata addua da fadin Afnan ta samu 'yar uwa dama kullum maganarta yaushe momynta zata siyo mata kanwa."
Hajja da rashida suka saka dariya ya kalli Wasila dake dan murmushi yace "Sannu Wasila Allah ya kara lafiya kin iya haihuwa gaskiya kin biya mu tunda kika iya haifo mai kama damu." Murmushi tayi cike da kunya ta sunkuyar da kanta kasa, hafsa ta zauna kusa da ita tana mata sannu da jiki hafsa tayi sha'awar yarinyar wasila taji inama itace ta haihu ita yanzu cikinta watanshi hudu da sauran lokaci.

Bayan sun koma gida misalin uku na rana sai ga mutanan garko Inna hajara da bitan da kuma matar kawu Habibu mai suna Saratu, mai allo ne yace maza maza suzo su gane masa abinda aka samu kafin yazo.......Su Wasila sunji dadin zuwansu sosai, nan inna hajara da bitan sukaga irin daular da Wasilan ke ciki dukaninsu mamaki suka shigayi babu shakka ba karamin mutum yarinyar ke aure ba, lalacewa sukayi gurin kalle kalle a gidan har gariba tayi gashi mai allo y

ace su koma da wuri, Aikuwa Wasila tace ba xasuyi tafiyar dare ba sai da su bari sai gobe.....Inna hajara tace"Wai ni jama'a gidanan ba'a ganin fad'uwar rana ne? nifa tunda na shigo gidanan nake ganin yanayi daya baka gane ya yanayin gari ya yake wai ashe har magariba tayi bamu sani ba oh."
Rashida ta dinga mata dariya tana fad'in "Nima lokacin da nazo gidan haka nayi ta sai da nasaba tukkuna nake ganewa idan lokacin sallah yayi zakiji kiran sallah ko kuma ki kalli agogo."
Ina hajara tace"Yo duk cikinmu waye ya iya agogo ai kina sake baki sanar damu lokaci ba." Wasila dake zaune kusa da bitan tana shayar da babynta nono tace"Nifa Inna ba zaku koma da wuri ba dukaninku zaku zauna sai anyi suna nayi ar'ba'in tukkuna."
Inna hajara tace"Ashe dai baki da hankali wasila yo ai idan wasu suka gamu rud'u rud'u sai su dauka kwadayi ne ya zaunar damu yanzu ma dan dare yayi ne shiyasa da tuni mun tafi." Wasila tace"Dan girman Allah inna ki zauna ko bitan ku taimaka min." Bitan tace"Idan banda abinki wasila wannan baiwar Allah na zaune tare dake tana iya bakin kokarinta a kanki ai idan muka zauna sai taga kamar mun raina kokarinta ne." Hajja dake kokarin 'karasowa inda suke tace"A'a bitan ni bazance komai ba wallahi ni kaina zanfi jin dadi ace wata daga cikinku ta zauna tare damu har yarinyar nan tayi ar'bain." Bitan tace"To sai dai ko Hajara amma dai sai abinda malam yace Hajja tace"malam ba zaice komai ba insha Allahu.

Koda Amadu ya dawo gidan ya tarar dasu Inna hajara sai yaji dadi sosai ya shiga har inda suke suka gaisa a mutunce yana tambayarsu mutanan gida da malm mai allo, sukace kowa lafiya lau malam yace ayi maka barka kafin yazo.....Yace."Insha Allah gobe zan sanya Garba yaje ya daukoshi domin yazo yaga abinda aka samu.

Kafatanin ma'aikatan gidan babu wanda bai shigo yaga baby ba, dukaninsu suna cikin farin ciki mussaman Garba da Abdulhadi aranar Amadu yayi musu kyatuttuka duk domin farin cikin da suka nuna bisa ga 'karuwar da ya samu.

Wasila taga gata da kulawa gurin Hajja da inna hajara babu abinda takeyi sai aukin bacci idan kuwa kaga baby a hannunta to nono zata sha yarinyar na tsakanin hannun Hajja da inna Hajara watarana kuma rashida itake rainonta idan tana gida......Malam da Kawu Habibu sunzo sunga baby sun sanya mata albarka sosai nan Amadu ke shaida musu sunan yarinyar Fad'imatu sunan mahaifiyarshi kenan.....Malam da kawu suka sanya mata albarka da adduar Allah ya sanya ta zama mai taimakon addinin musulunci.

Ranar suna Wasila ta fito tamkar wata amarya taci gayu sosai da wani uban les Hafsa ce ta dauko mata me make up tayi mata kwalliya sosai ta shiryata hannayenta da kafafunta sun sha jan lalle wanda yayi masifar kyau yayi jawur abun sha'awa, gold din dake jikinta kuwa abin kallo ne dan ana ya gobe suna ya shigo mata da kayan barka ita da baby set din akwatina shida shida makil da kaya iri daban daban wasu a dinke wasu kuma ba'a dinka ba ga uban gold kirar dubai da ya siya mata har kala uku yari da sar'ka da zobuna da abubuwan hannu ko ina na jikinta walwali yake yi.....Hafsa ta gayyaci kawayenta manya mata su kansu sai da suka raina kwalliyarsu ganin kwaliiyar mai jego din ta mussamance.......Zeey da Suhairat kam kasa zama sukayi a cikin gidan tsabar bakin ciki da yayi musu yawa ko wacce ta silale ta gudu ba tare da mutane sun fargaba.
Amadu kam tun da safe kafin ya fita da yaga kwalliyar matar tashi hankalinsa yay bala'in tashi ganin tamkar an 'bare ta daga leda tayi wani 'bul-'bul ta cika ta batse tayi uban kwarjini irin na jego sai daukar ido takeyi, kafin ya barta ta fita daga d'akinsa sai da ya latsata iya son ransa ya tsotsi bakinta ya tayar wa da kansa hankali mutuka, sai da taga yana kokarin shige gona da iri ne yasa tasa masa kuka tilas ya kyaleta jikinsa na kyarma ya shiga goge mata fuska wai baya so ta 'bata kwalliyarta, da kyar ta samu ta kufce daga hannunsa, aikuwa bata sake komawa dakin ba har ya fito tana jinsa suna magana dasu Hajja taki fitowa daga daki sai bayan ya fita daga gidan ne ta fito ta cigaba da hidima da mutananta.

******
Bayan suna da kwana biyu gida ya dawo normal
Chapter 87 · 0% Book details