← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 60

Sashe 57

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
```NA SADAUKARWA DA WANNAN PAGE AGAREKU SHAHARARRUN MARUBUTAN MU NA```
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
WANI SALO
```NAKUNE INA ALFAHARI DAKU MUSSAMAN```
*Aunty Fauza*
*Aunty batul Adam jattko*
*Aysha Sada Macika*
*Ummi Ontop*
*ummu nabil*
*Aysher Machika*
*Hauwa A Usman Jiddarh*
*Muneera*
*Halima mk*
*Sameena Aleeyou*
*Mommyn arfat*
*Fauxia MB*
*Mrs MaKAMA*
*Miss Ayusha*
*Ummin Fauzan*
*Meenat Yakasai*
*_Noor_*
*Aisha Hamza*
*maryam maishanu*
*Mrs
Mansoor
*UMMU FATIMA*
*Maimouna Matar Abdou*
*Ummin eeman*
*(110-111)* Zaune yake shi kadai a cikin parlour yana sana'arsa waton dannar waya kirane keta faman shigowa cikin dayar wayarsa da yasa aka kawo masa bayan anmishi wlcmbk amma gaba daya rabin hankalinsa yana kan qofar dakin ta, tindazu yake jiran fitowar ta amma shiru yakeji kuma shi a gaskiya bazai eya zuwa dakin ta b...
Alamun motsin qofa yaji za'a fito kafin ya dauke kansa daga kallon qofa yana cigaba da abinda yake.
Sam zee bata kula da yana cikin parlour ba tafito daga eta sai wani dan sekat qarami eya gwaiwa sai 'yar riga top kayan sun matuqar yimata kyau sai tafito tamkar wata 'yar baby tawuce tanafi qofar kiching tana tafiya tana rangaji kasancewar yanzunnan ta farka daga bacci bai eda sakin taba yunwar da take jine etace ta tadota brush kawai tayi tafito.
numfashin sa kusan daukewa yayi sakamakon ganinta da yayi ahaka abin yamatuqar bashi tsoro a zuciyarsa yake cewa wai meke faruwa da nine?
jin faduwar abu ne yasashi dawowa cikin hankalin kansa.
eta kuma zee lokacin da tafito daga kiching ne bayan ta dauko abinda zata buqata
zata nufe gurin dinning kenan edonta ya sauka akansa batasan sanda abunda ke hannuta yafado ya tarwatse ba, sam batasan yana cikin parlour ba shi yasa tafito a haka, ganin tsayuwar bayada Amfani yasa tayi cikin daki da saurinta.
shi kuma ganin haka da yayi mata yamatuqar tada mishi da hankali, shidai a rayuwar sa koda " za'a tsaresa da bindiga akan yanuna yanda siffar macce yake wllh sai dai akashe shi dan shi bazai iya fadar yanda siffar mace take ba saboda kokadan wannan bai damesa ba, byko cikin tsarin sa yaune karo na farko daya fara tantance yanda siffar mace yake, koma a gaskiya shi bazai eya jure rashin ganinta ba, shi yasa zuciyar sa keta saqa mishi tana engizashi akan ya daure yatafi dakin ta yasameta, haka kuwa a kayi cikin qarfin gwaiwa yamiqe tsaye zai tafi sai kuma cak" yaja yatsaya kafin yayi magana a zuciyar shi yace toh wai edan naje ma" mezance mata, tinda shidai eya rayuwar sa bai ta6a magana da wata mace ba, koda kuwa dai-dai dana 1 mint ne.
ganin da yayi zuwanshi shi yafi sauqi a gare sa, koda kuwa bay san abunda zai fadamata ba, amma haka ya daure yanufe dakin ta shi dai buqatar sa" ya koma ganinta a haka a yanda ya ganta tafito.
sau 4 yana niyar shiga cikin dakin sai Kuma yafasa yarasa yanda zaiyi da ransa yaji sanyi, cikin qarfin hali ya murda qofa a hankali ya shiga.
sai da zee ta tsorata lokacin da taji alamun an bude dakin ta saboda tasan mawuyacin abune taji 'yan bude dakin edan ba eta ba,
sororo tayi sakamakon ganin wanda ko amafarki bata ta6a tunanin ko tsammanin zaya shigo cikin dakin ta ba, sai gashi kodai gizaune yake mata" kasa motsawa tayi daga gurin da take " Arzikin ta daya ne lokacin da tashigo cikin daki kamar tasani ta dauke hijab dinta ta sanya sai gashi wanda bata ta6a tsammanin ganin sa dakin taba ta gansa aciki tambayar kanta take to meyake nema meya kawoshi gurinta?
6oye mamakin ta tayi tare da tamke fuskarta sosai babu alamun fara'a kokadan a fuskarta, kafin tace kai kuwa Malam meya kawoka daki na bako sallama Kumar ba ezini??
dikda tambayar ta sosa ransa sannan kuma uwa uba baizo yatarar da eta yanda yakeson ganinta ba, dik da haka bai nuna mata komy ba. Ellar niman guri da yayi a kan wata 'yar qaramar kujerar madubi ya zauna, sai da yadade yagama shaqar qamshin sa, sa'annan yace cikin taushin muryar sa...
Wllh a eya duk tsawun tunanina a rayuwata kokadan banta6a kawo tunanin zanyi Aure ba anan kusa" haka kuma banta6a tunanin zan eya bude bakina nawa wata macce magana ba mussaman ma qaramar yarinya erinki sai gashi naga hakan yafaru, banyi tsammanin koda zan kasance da wata mace ba arayuwata na nayi tunanin kasancewa da keba, saboda ko acikin lissafi matan da zan aura banyi tunanin zaki kasance cikin dai daga cikin su ba,
sai dai kash" gashi Allah yariga yatsara komy yanda banta6a tunanin hakan zai kasance ba,, haqiqa dik yanda kaso katsarawa kanka rayuwa matuqar ba haka Allah yatsara maka eta ba tohh tsarinka na banzane, Hmmmmmmm sai kuma yatsaya yaja numfashi kafin yaci gaba da cewa, tohhh yanzu dai gashi.
Narantse a kanki nafara yiwa wata diya mace magana arayuwata, a kanki kuma nafara baccin da haushin mutun araina, haka a kanki nafara daukar fansa edan akaman Abu, kuma a kan kine nafara kwanciya a asibity a tun lokacin da nasan kaina, kece kika canja man duk wani tsari na rayuwata ciki kuwa harda kasancewar zamana miji agareki wanda sam" banshirya son hakan ya kasance ba,
*MEYASA KIKA SHIGO RAYUWA TANE KIKAMAN SHISHIGI?*
Yafada tare da tsare zee da edo duk yanayinsa ya matuqar canzawa.
qwarai maganganun sa kemata yawo aka, amma wannan tambayar etace tafi komy tsaya mata arai, kauda zancin zuci da take tayi da cewa, bangane meyasa nashigo rayuwar ka nama shishigi ba? Ko kuma dai nace kai meyasa kashigo rayuwata kaman shishigi? Matuqar eadan amsar da zakabani tazamanto ne da a..a baka da amsar, tohhh nima hakan yake agurina, Allah ne ya hadamu dan haka banida amsar tambayar ka, wannan amsa Allah kadai ne yabarwa kansa sani " kaddara tariga fata, enada labarin kai kowanene kayi matuqar sona a duniya wanda kai kanka nasan bazaka eya qirga adadin eya miliyoyin qasahin da sunan ka yake acan ba, dikda lokacin da aka kawoni gidannan baqaramin girgiza nayi da yanda naga gidan nan ba saboda ko villah bata kaishi tsaruwa ba, amma kokadan wllh banyi farin cikin kasancewa acikin saba, haka kuma banyi farin ciki da kasancewar ka miji agarini ba, Inason kasan wani abu daya wllh na aure kane kawai abisa kaddara da Allah ya aykoman da kuma a bisa umaranin mahaifana da naka, dan kasan kasani wai badan wani abu naka ba, WLLH BANTABA SONKA BA KODA NA DAI-DAI DANA RANA DAYA NE, dan haka karma karkayi tunanin na aure kane saboda so ko kuma kuddin ka ko kuma wani abu dai naka tohhh narantse bako daya, dan haka kama daina tambayana meyasa nashigo rayuwar ka dan karkayi tsammani kwadayi ne yasa na aure ka...
da qarfe ya runtse edosa sakamakon yanda yaji kalaman zee na qarshe yanda suka doke kunnansa da zuciyar sa jiyayi tamkar zuciyarsa zata fito........
shiru dakin yayi ba abinda kakaji sau qarar Ac da yake a kunne, shikuma kansa na qasa kamar mai wani tunani, sunfi kusan 20 mint ahakan batare da yin koda wani qwaqwarar motsi ba.
a hankali yamiqe tsaye batare da ya kalle ta ba, yanufe qofar fita yana maida numfashin sa da yakejin tamkar ya dauke daman haka Kalmar nan take da zafi kodai dan yakasan ce etane ta fada shiyasa yaji ciyon haka matuqa, ada yafi qaunar yaji wannan kalmar so dubu da afadamishi kalmar so, saboda kalmarso ciyonta yakeji edan yajita abakin wa'anda ke furta wannan kalmar agarisa feye da yanda yakeji ayanzu, amma tohh yanzu meyasa yakasa jure jin wannan kalmar?
kasancewar baida Amsar wannan kalmar yasa yayi hanzarin fita daga cikin daki kafin ya koma jin wacce tafi wannan zafi da quna...
~****----****~
Ko ajikin zee bataji badadi da hakan da tafada ba asalima haushin sa da takeji, ace mutun mugun girman kai kamar kafiran farko, dan rainin hankali ni yakewa wannan tambayar wai meyasa nashigo rayuwar sa, tohhh anshigo din kayi abunda zakayi mtsss" taja wani siririn tsaki afili taketa wannan surutun eta kadaya kafin ta tashi tanufe toilet dan sakarwa kanta ruwa,
~_____=====_____~
Cikin wani tamfatstsin parlour ne na kusan shida acikin gidan su emran suke a zaune shida qasim saka makon kiran da yamasa na gaggawa dikda yanzu lokacin yadan ja, dare yafara dan yanzu kusan qarfe 9:36pm, amma haka ya daure yafito saboda yanda yaji muryar emran wani eri,
Haqiqa duk wanda yakasance cikin wannan parlour sai yaji tamkar angafarta masa dukkan zunubansa saboda tsatsan ni'emar dake ciki gaba daya gless ne a kewaye da dakin Ac akallah kusan 6 ke ciki, bama kamar rantsatsun kujerun dake ciki na miliyoyin kuddi wa'anda suka amsa sunan su, kusan ma shine parlour da kowane parlour yafishi haduwa, dan shine ma qarami.
qasim zaune yake a gefin emran yana bashi baki kasancewar sashi gaba da emran yayi sai faman ciccika yake alaman yasa kuka yagaji, cikin raunaniyar murya yadago kansa yadubi qasim" dikda qasim yatsorata da ganin yanayinsa amma bai nunaba ellah ma cigaba yayi da tambayarsa abinda ke faruwa,
cikin qarfin hali emran ya kwashe duk abinda yafaru tsakaninsa da zee a yau da erin maganganun da tafada mishi amma shi ya 6oye nasa daya fada mata, yaci gaba da cewa, wllh qasim tun lokacin da nabar dakin ta da qyar da taimakon Allah na esa nawa dakin tunda na shiga narufe zuciyata takeman zafi tamkar zata fasa qirjina tafito, wallahi qasim yarinyar nan zata kasheni da sauran kwanana, da addu'a da komy nasamu zuciyata ta karaya kuka yazo man wanda banta6a tsamanin zuwansa ba.
Qasim ensonta tamkar nayi hauka, qasim ya zanyi da rayuwa ta, qasim kataimake ni please kada kurasani, dan narantse enajin matuqar edan bata soni ba zan eya mutuwa, kafadamin yanda zannuna mata yanda nake sonta dan Allah qasim....... yafada da qarfi yayinda kuka yakoma kwance masa.
sai da qasim yabari yayi kukansa sosai ya gaji kafin yacigaba da lallashin sa ciki da tausayawa dan koshi harda 'yar qwallasa saboda sosai ya tausayawa Abokinsa, sunan emran qasim yakira cikin wata murya kafin yacigaba da cewa, Haqiqa so ba qarya bane kuma ba wasa bane, emran ka tafka kuskuri babba arayuwar ka, ka dauke ji da kai da qasita da kuma ezza da esa, kadaurawa kanka wanda kuma hakan ba dai-dai
bane" ansha lurassa dakai tun kafin ka mallaki hankalin kanka amma ko kallo mutun bai eshika ba balle ma harka saurareshi, kamata da duniya akwai jarabawa, mai kyau da marar kyau, kasanyawa kanka ta kunkumi narashin shiga al'umma bare harkayi fira dasu, daga mamy sai daddy sai kuma ni kaina kadai muke samun albarka bude bakinka kamana magana koshi da qyar" amma bancin mu ba wani wanda yake cewa yata6a jin muryarka na waje dai,
tabbas emran kayi mulki kakumayi qasita wanda ko sarki bazai nuna maka wannan ba, Allah yabaka kuddi yabaka nasaba mai kyau hadi da kyakyawan halaye da dabi'u uwa uba kyau da Allah yama, duniya ba abunda Allah yarageka dashi amma kai duk wannan ni'imar da Allah yama saida kaqara da abinda Allah bayason duk wanda keda wannan mumunar d'abi'a ta girman kai, dole ne nafada maka gaskiya duk da canma baya akullum ciki fada maka eta nake amma ga lokacin eskar naqi nakadaka ko saurarena bakayi ba, amma yanzu naga alamun kamar kadawo hanya dan haka zanbaka shawara matuqar kanason kaga dai-dai arayuwar ka tohhh duk wani abu da kakeji dashi ka sauke shi, koda Allah zai dubeka yakarkato ma da hankalin yarinyar nan shine kadai mafita a gareka, matuqar edan kadauka....
shiru yayi yana saurarin duk bayanin da qasim ke masa, tabbas yasan abunda qasim yafada gaskiya ne, tohhh ammafa koshi ba laifinsa bane haka yanayinsa yake meyasa mutane kemasa kallon mai girman kai bayan shi kokadan bahaka bane, amma matuqar hakan zaisa yasame so daga gurin ta, tohhh tambasa yayi niya dan Allah yakuma daure aniyar ajiye duk wani abu da ake cewa yanada.
tabbacin zaiyi duk abinda qasim yace yayi yabawa qasim tare da d'orawa da cewa kuma ensha Allah wannan tafiyar da zamuyi jibi tare zamu tafi da eta, ada kam na musa maka hakan da kace" amma yanzu hakan yazamemini dole kodan samuwar kwanciyar hankalina....
Fadar erin farin cikin da qasim yake ciki abune mai wuyar faduwa, Hamdala yayi ga Allah da yanuna masu wannan rana hakika shi yasan auren Zainab rahamani ga emran da kuma su baki daya,
cikin jin dadi ya rungumi abokin sa shima emran hakan yayiwa qasim cikin farin ciki qasim yayi zaune yafara shiryawa emran abubuwan da yakamata yayi da mutane da kuma eta kanta Zainab din......
*_Anyyyyya kuwa wannan tuban na emran na gaske ne zai eya abunda yafada Kuwa????_*
``` kudai Kuci gaba da kasancewa da 'yar gidan Alkali don jin yanda zata kasance...```
[5:24PM, 2/24/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 57 · 0% Book details