← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 60

Sashe 20

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(43-45)*... Yusra wai wannan kwalliyar duk ta mecece kike ga driver can tin dazu yazo yana jiran mu awaje, momy ay nagama ganinan, ena zee din take be?, tana gurin baba, toh kifito mata da kayanta muyi fitar gaba daya...
ohk momy, haka yusra tagama feshe2 turarin ta tana ta juye2 a gaban madubi addau'a take a zuciyar ta, Allah yasa yau tarkonta yakama kurciya, dan eta tinda Allah yasa, tayi edo biyu da affan taji zuciyar ta, ta mutu akansa, taga alamar koshi kamar yana da danjin kannan, amma dai yafi shahararrin can cewa da emran, haka dai tayi ta, zancin zucin ta, tareda daukar jakar kayan su tayi waje,
toh shi kenan Allah ya kiyaye zainab dan Allah ki kula banda tsira kidinga kuma haquri da mutane banason anyi ance Allah ya kiyaye,
ameen mama nagode sosai, khaleed ya wuce scol bari muyi sallama, shi dai yaya munyi waya dashi shima yace zai kawomin ziyara har can,
toh Allah ya qaddara kiyi niya kutafi Allah ya kiyaye, ameen mama zanyi matuqar kewarki,
naji ni dai jeki Allah ya tsare ya sauke ku lpy,
Hajiya Ameena wai keko wani erin zuciya ne kike dashi,? ke ko erin kishin danki d'innan ba kyayi, akan a bunda yarinyar nan tamasa, amma harda tafiya ki wani daukota, har ta zauna dake, ni gsky kwata2 wannan tsarin naki bai min ba,
toh kiyi hanquri fulani hauwa, kinsan kowa da erin, tsarin rayuwar sa, kuma daman Allah ya qaddaro da hakan, ko tafiyar da zanyi da eta haka Allah yariga ya qaddara, ba yanda zamuyi, dan Allah kicire, abun nan aranki, kuma naji dadi matuqa dakika nuna da muwarki sosai akan lamarin emran, shi yasa naso matuqa emran ya amince, ya aure sadiya, saboda erin qaunar da kike masa, da kuma xumuncin mu yaqara qarfafa, amma yaron nan yaqi, nayi2 dashi, amma, abun yace tira, dan Allah edan su sadiya sukayi futu tadawo gida, kiturata man eta, ko Allah zai sa su dai2 ta,
wani murmushi gimbiya hauwa, tayi erin na masuji da mulkin nan, saboda dadin maganar da hajiya ameena tayi,
ay wannan hajiya basai kin roqa ba zata zo, koba komy ta gaydaki, kuma maganar son da nakewa emran ay wannan tin asali yake, wllh tamkar affan nake jinsa a rai na, Allah dai yaqara mana danqon zumuci ,
ameen2 fulani, wannan maganar gaskiya ne, bari nayi saurin shiri, mutafi kinji jakadiya tace su zainab sun zo tin daxu, kada na barsu sunata zaman jirana, bari nakira wancan kurman dan naki,
sannu hajiya ywwa2 kuyi hanquri fa, natsaya shirya wane wallhy, ay ba komy hajiya, momy tafada, toh shi kenan nagode, Fulani hauwa ce, tafitoh cikin shiga ta alfarma, suka gaidata dikan su, ba yabo ba fallasa ta kar6a musu, a tare suka fito..
Mamy ce tace, wai ena emran dinne basu fito bane? hajiya ay yalla6ai yafito tin dazu yana cikin mota yana jiranki..
ohk hakan yayi kyau hakan" da bai sanyamu tsayawa zaman jiransa ba, fad'awa su momy tayi su shiga cikin motoci, su tafi kar jirgin su ya tashi,
da misalin qarfe 3:38 pm jirginsu mamy ya sauka a airport din dake garin abuja, motoci ne birjik sukazo taryar su, securitys ne, ta ha gunsu da daman su, har gurin motocin sa,
gaba daya emran bay san da zee ma, aka zoba wata haddadiyar motace aka bude masa ya shiga, su mamy ma haka, dik wanda yaga wucewar motocin yasan emran ne, aciki saboda number motar dake dauke da sunansa, kwance yake cikin mota ana tafiya dashi ahankali saboda bayason ayi gudu da mota, Ac ne keta fesowa tako ena fuskar nan tasa taqara wani erin haske da kyau, emran kyakkyawa ne na qarshe, lumshi yake da edonsa har suka esa gida bai sani ba nufashin sa kawai ke fita a hankali alamar bacci ya sace shi,
har su mamy suka fitoh ba taga alamar fitowar emran ba, securitys ga sunan a tsatsaye suna jiran fitowar sa, lokacin da mamy ta esa gurin mota, a dai2 lokacin da driver yafito daga cikin mota, ya ankayi ne jamilu? meye emran yake jira acikin motar ne da bai fito ba,? dan rusunawa jamilu driver yayi, yace hajiya yalla6ai fa bacci yake,
murmushi tayi erin na manya, tace emran kenan, emran rigima, yanxu har yayi bacci, kafin tace lallai zaman jiran tashin sa daga bacci ya sameku,
susa kansa jamilu driver yayi cikin girmamawa yace hajiya ay ba komy yalla6ai ne fa,
girgiza kanta kawai tayi kawai, kafun tawuce ta qarasa gurin su zee, eso tamusu har cikin gida,
sai da su momy sukayi sallah sukaci abinci sannan sukayi shirin tafiya gida etada yusra, haushi ne, tabb a zuciyar yusra da taga affan ko kallon ta bai yiba, zuciyar ta ce takejin namata wani erin zafi, haka sukayi sallama da zee kafun driver da mamy tasa ya kaisu gida ya daukesu suka tafi,
sai gab da magarin emran ya farka daga bacci firgigit yayi, saka makon farkowar da yayi yaga lokacin sallah la'asar har" ta wuce ana baton magarib
tsuwar mota sukaji alamar ogan zai fito, da hanzari sukayi saurin bude masa qofa, cikin qasaita ya nufe part dinsa tareda securitys guda 2 abayan sa..
Afrah! Afrah!! kena enane,? yes mamy ganinan zuwa,
wash" ance enakaji kira samune mamy Allah yasa dai tsaraba ce, kikamun ta musamman tafada tana shigewa a cinkin jikin mamy
kene dan Allah da gani komy ban siyo miki ba, kai mamy dik zaman kadai cinnan dana sha,
tohm ay maganin zaman kadai cin ne, naje samomi ki, inayake mamy?
gashi tana nuna zee dake a raku6e a gefin qafafun ta, kanta a qasa,
ko kadan afrah bata lura da mutun agurin ba, a lokacin da etama zee ta dago kanta a hankali,
What...? Mamy me zan gani wannan ba etace ta kifama yaya emran cake a fuska ba arananr birthday dinsa ba?
e tace mamy tafada a taqaice, ki zauna ya ban eda magana ba, zaki wani miqemin a tsaye,
jiki amace afra ta koma ta zauna cikin mamakin wannan lamari,
nasan zakiyi mamaki sosai akan koma ganin zainab da kinkayi anan gidan, nan dai mamy ta kwashe labarin komy tin daga kan abunda emran yawa xee, da kuma abunda yafaru a zariya da kuma yanda taroqi eyayin zainab a kan tanason su taimake ta, su dan bata eta ta zauna, na dan wani lokaci a dalilin ki kad'ai Afra, dan haka ena roqonki karki dubi abunda yafaru tsakanin su, abar maganar ta wuce, ina son ki dauketa, tamkar 'yar uwarki kuma qawarki, har zuwa lokacin da zata koma gidan su, dan Allah afra bana son anyi ance, daman ke nasanki ba gwanar zafi bace ke, gobe inason ki dauke zainab kutafi, kiciro kudi, kutafi, supermarket gurin sayyaya, dik abinda yadace ina son kuje a siyu mata komy da komy, daga kan sutura, har zuwan kayan shafa da turaruka, kayan makeup, dika komy kusiyo da ganan, kuwuce gurin kai dinki,
toh mamy ensha Allah komy yawuce, kuma ensha Allah zanyi yanda kikace,
ywwa Afra Allah yayamiki Albarka kinji da man nasan bazan samu matsala gurin shawo kanki ba,
ameen mamy, tashi tayi taje gurin zainab tareda riqo hannuta, cikin murmushi tace taso mushiga ciki ko,
mekewa zee tayi suka jera, a tare afra nariqi da hannuta suna tafiya tana tambayar ta sunan ta, suna haurawa, a sama,
murmushi mamy tayi cike da jin dadi, yanda taga afrah ta kar6e zee, cikin sauqi,
[10:39AM, 1/13/2018] A:
Chapter 20 · 0% Book details