← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 60

Sashe 45

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(88-89)* arazane emran yadago fuskar sa edo biyu sukayi da daddy,, kallo daya daddy yamasa duk ganin yayi emran ya rame sosai dik yayi wani eri,
yanzu emran da hankalin ka kake neman ellata rayuwar ka a banza, mufa eyayinka ne wllh baka da kamarmu a duk fadin duniyar nan, me yasa kai kacika zurfin ciki ne, kasani wannan abun da kasawa rayuwar ka baida wata amfani kwata+2
Kallonsa daddy ya maida gurin qasim yace haba qasim yanzu ace kasan abunda ke damun dan uwanka shine kuma kayi shiru da bakin ka bakayi gaggawar sanar da muba?
kanshi qasim yadan sosa kafin yace wllh ba haka bane ba daddy, nima kwananan nasani kuma koshi wllh bashi yasanar dani ba, da kaina nafahimce haka, kuma yaune nake da niyar ensanar da mamy halin da ake ciki sai kuma nazo natadda su suntafi asivity,,
gyaran murya dady yayi kafin yace tohh yanzu enason ensan yarinyar nan wacece eta, kuma a enane gidan su yake, dan naji kace ana gab da daurawa yarinyar aure...
Haka emran ya dingawa qasim
wai dan kada yafada fita batunsa qasim yayi yace gaba da cewa ,
Hakane daddy tabbas ana kusa da d'aura mata aure, sanan kuma bakowa bace yarinyar, ellah yarinyar da mamy ta ta6a daukowa tin kuna wancan gida, wacce take tare da afra kuma yanzu haka tanama gidan enamajin da eta ne aka tafi asibity,
cikin rashin fahimta dady _yace wacece haka? (kasancewar daddy baya gari aka kawo zainab dan haka bai gane wacce qasim ke nufin ba)_
daddy yarinyar da tayi zamanan kwana baya wacce ake cewa zainab, da qarfi emran ya lumshe edonsa saboda yanda qasim ya kira sunan ta,,
ohh" natuna ta daman tana gidan nan ne, daddy ya tambaya,
ehhh tananan bata jima da zuwa ba, kuma yanzu daddy wai kaji baxai aure ta ba, saboda ba class dinsa bace,
kai dan Allah fita batunsa bai san ciyon kansa ba ne, narasa abunda ke damun rayuwar emran wllh, ko ranar nakira manager office dinsa naji ko yana fita gurin ayki ceman yayi yanzu ya kwana biyu bai fita ba, tohh wannan wace erin rayuwa ce,
[ _ba abunda ke damunsa tsabar esace kawai da jinkai_ ] qasim yafada a cikin zuciyar shi, kafin ya tsinkaye muryar daddy yana cewa yanzu mutafi can asibitin tukunna edan muka dawo zuwa anjima zamu tsaida magana gobe ensha Allah zamu tura gurin neman auren ta,
Edo emran yaturo cikin rawar murya yake cewa daddy pls kada kuman haka dan Allah, nifa ba sonta fa nake ba, kuma yanzu abba arasa yarinya da za'a aura man sai waccan, baqauyiya ce fa kuma qazamiya daddy kwata+2 fa ba class dina bac....
daddy yayi saurin qatseshi tare da cewa,, yaci gidan su class din ba class ba *jami'a* emran wllh Allah ka kiyaye ni, kana nufin haka zamu zuba maka edo gutai+2 dakai kaci gaba da zamarmuna acikin gida arasa ma dani da kai wanene mai gidan tohhh wannan karon Kayi kadan naga alama sai munsame matsala dakai fa sosai zakayi hankali wllh tohh kamaida hankalin ka kana jina ko,,
Kansa ya duqar tare da cewa a hankali kayi haquri daddy ensha Allah hakan bazata qara faruwa ba, Allah ya huci zuciyar ka,
daddy bai caya saurarin sa ba, yacewa qasim sutafi asibity dan kadama ya6ata musu lokaci, satar kallon emran qasim yayi, shima akayi sa'a edon emran na kansa,, kallon qasim yayi tare da mishi wani kallo erin na zakasani
Murmushi qasim yayi
_a zuciyar shi yana cewa guy kakusan shigowa hannu bakasan mata bane shiyasa duk kake wannan abubuwan_
bayan daddy yabi suka barshi nan a zaune cike da takaicin abunda ya kasance a yanzu tayama zai zauna da wannan yarinyar gaskiya shi za'a cutar dashi da yawa,, duk shi kadai keta zancinsa a zuciyar sa,
*A Hospital kuwa*
duk wani abu daya dace awa afra anmata hatta da gashin jiki duka anmata tare da shafa mata magungunna masu rage radadin ciyon kuma anmata allura gashi harta samu bacci,
mamy ce da zainab zugum+2 sukadai a cikin dakin sai securities din dake waje a tsaitsaye duk wanda yawuce gurin dakin nan yagansu a tsaye yasan ba qananin mutane bane aciki,,
Mamy dubanta takai zuwa ga zee yanda duk taga tawani birkice tamafita shiga cikin damuwa, ahankali takira sunan ta, dago kanta tayi tare da amsawa tana kallon mamy,,
zainab ki kwantar da hankalin ki kinji mamy tace mata, sannan kuma kada kidamu ensha Allah data farko yanzu zamuga sauqi,,
amma na tambayeki wai ko afra tafada miki abunda tawa emran haka na rashin kyautawa ko kikaga tamasa dan gaskiya wannan dukan daya mata ba abanza yayishi ba, saboda nasan halin emran yanada kauda kai akan abu, lallai baqaramin tunzurashi tayi ba da har yakai da ta6a lafiyar ta,
Uhumm kawai zainab tace, can kuma qasan zuciyar ta cewa take ba abunda tamasa tsabar mugunta ce, kawai, amma afili cewa tayi ni ganin nake mamy kamar dai da'akwai wani abu amma edan ma da akwai wllh tohh ni bansani ba, kuma banga alamar tamasa komy ba, dan kullum atare muku tohh edan harko tamasa wani abu tohh tabbas zansani amma yanxu dai bansan meya hadasu ba gaskiya,
sosai mamy ta gamsu da bayanin zee kafin tace tohhh yanzu enason kije driver ya maidaki gida ki dauko muna duk wani abun da zamu buqata edan kuma masu aiki sungama abinci kizo dashi, dan enajin da wuya yau edan zasu sallame mu maybe sai gobe,
cikin girmamawa zainab ta amsa tareda miqewa tayiwa mamy sallama tafita,
fitarta da kamar 20 mint su daddy suka qaraso aynan danan asibity taka came da zuwan mai girma shuguban qasa, Doctors kam sai kawao gaisuwa suke har cikin dakin da Afra take akamai eso,
~
Esar zee gidan keda wuya bata zarce ako ena ba sai part din emran security dake gurin bai hanata shigaba kasan cewar ganinta da yake a gidan kuma tare da Afra,
ahankali ta bude qofa tashi qafarsa tasa daya kafin tasaka ta biyu wani qamshine da sanyi Ac mai ratsa jiki taji yatarbe ta, ganin tayi wannan parlour yamafi na wancan na gidansu tsaruwa da komy saida taqare wa dakin kallo kafin tanufe qofar bedroom dinsa ta aza hannuta kenan da niyar bude qofar sai ta tuni da maganar sa daya ta6a mata a wancan gidan nasu, _na cewa ba'ayi maccin da zata shigarmishi bedroom dinsa,_ shiru tayi nadan wani lokaci tana shawar shiga tasan halinsa dan taga alama mutunci ba gama esarsa yayi ba, zai eyayimata wulaqanci naqin qarewa tinda eta takawo kanta,
sai kuma wata zuciyar tace mata toh ay ba neman wani abu yakawoki gurinsa ba qarshima ba mutunci yakawoki ba dan haka kishiga edan yayimiki kimasa qarshin ta dai ya dokeni kamar yanda yawa 'yar uwar sa, d'ayar zuciyar taji tace wllh ko dayaga hauka,,
babuwata+2 takutsa kata cikin dakin kamar yanda yasaba zaune yake kan fadeden gadonsa bayan yasa tufafin sa, laptop ce a gabansa sai wayoyinsa dake gefe yamaida hankalin sa sosai kan laptop dinsa sai faman bincikarta yake,,
jiyaye an bude dakin sa anshigo amma bai dago ba saboda yasan ko wanene baya wuce qasim
sundauke tsawun dan lokaci eta batayi maganaba kuma bata zaunaba shima bai tadda kansa ba da abunda yake,, yasan qasim yanzu da wani sabon eskanci yazo dashi kuma shi yamayi mamaki da yaga yadawo yanzu dan basu dade da fita ba kodai ganin yayi gara yazo ya cigaba da cimin rai shi yasa yaqi tafiya duk azuciyar shi yake duk wannan maganar,
jiyaye anmugun jan wani erin tsaki baisan sanda yadago kansa ba, babu zato ko tsammani yaga wacce bai ta6a tunanin ganiba
wani lalataccin kallo take binshi dashi,, sai faman yawo take acikin dakin, kafin tace *_babu maccin data esa tashigomin har cikin bedroom dina_* sai kuma gashi nashigo duk abunda mutun ya esa yayi yadade bayyiba dai+2 nake da duk wani mutumin da baisan darajar mutunba bare d'an uwa, nunashi tayi da yatsa edo cikin edo tace kana kuskure sosai arayuwar ka amma saboda hayaqin dake fita na kanka na shirme yahanaka ka fuskance haka, wllh da enada ekon daukar mataki akan abunda kawa Afra dasai namaka abunda sai kayita danasani arayuwar ka,
duk wani lokaci na mutane yana tafiya atsare amma kai kwata+2 bakada tsare balle har dubanka yakai ga alqibla dazata nuna maka dai+2 da rashin sa, yakamata katsayar da kanka abisa tubalin da zaka eya hango yanda rayuwar kowa ke tafiya ba erin takaba,
wannan shawara ce ganin damanka ne kabi haka kuma ganin daman ka ne kaqi bi, amma kasani lokaci qalilan ne ke gareka, so kana eya tafiyar dashi a hankali dan eta rayuwa batada tabbas,
sannan wannan duka dai kawa afra haqiqa kacan cance hukunci, wllh kakuru niba kowa bace, sannan kuma kafini kusance da eta dana sauke maka duk wani abu da kakeji acikin kanka, daga haka takoma jan wani tsakin dayafi wancan nafarko, kafin tafita cikin dakin, taje xuwa daukan abunda tazo dauka tafita,
[6:04PM, 2/4/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 45 · 0% Book details