← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 60

Sashe 49

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*NASADAUKAR DA WANNAN PIGE DIN SUKUTUM GAREKI*
(```MATAR YAYANA UMAMAT BABA BUHARI SIRIDDAWA```)
*_ALLAH YAQARA DANQON KAUNA DA SOYAYYA DAKE DA YAYANA, MUNEER ALKALI D/TSAFE ENA YINKI ERIN OVER
*(96-97)* bayan kwana biyu komy ya dai+2 ta game da magana 6acewar zainab duka zancin yacika gari cewa anganta,
haka kuma duk wata qafa tasadarwa taji labarin auren emran dan hakama ananan ana ta, sanarwa akan maganar auren EMRAN YOUSUF USMAN jama'a sai mamaki suke na auren sa, saboda ba wanda bai san tsarin sa, naqin aure ba, da kuma na rashin kula mace, dik wannan labarin daya gama karad'e qasa, ba wanda yake da masaniyar wacce tsaddadin mutun erin emran zai aura ba, kuma dik maccin da taji maganar auren sai taji enama etace, musamman wa'anda suka mutu akansa, sadiya haukane kawai ba tayi ba, da taji labarin auren sa, amma eta kanta ba tasan wacce emran zaya aura ba, masu karatu edan kukaji yanda ake zancin auren nan tako ena sai abin ya baku mamaki, gidan biki ne, gugun samari da magidan ta ne, majalisoshi tako ena tamkar ba wani labari sai na auren nan, kai abin ma ba'ako cewa komy,,
*(HHHHHHHHHH
wllh dole ne nayi dariya saboda fa)* wanda duk aka wannan domin sa yana a kwance saman gado yana tunanin ta yanda auren nan da a keson masa zai fasu zazza6ine keta neman rufeshi da gashi sai qasim aka bari sai kuma Afra da take gidan su zee, dansu mamy da daddy jiya sunka koma dan fara shirye+2 gagarumin biki erin wannan, lokacin da mamy takera aunty Hajara yayar emran dake London etada mijin ta, tasanar da eta maganar auren emran kokadan bata yarda ba, dik da ko tasan mamy bazata mata qarya ba, amma gsky abin da mamaki dan tana ko kwanto, sai da mamy ta rantse mata sanan taqar yarda tabbacin sunanan zuwa tabawa mamy dan dole ne tazo taga mai wannan sa'ar, har dai sukayi sallama aunty hajara na cike da mamakin wannan lamarin wai emran ne zaiyi aure babbar magana,
shirye+2 kayansu kawai suke saboda daddy yabada umarni sutashi, daga gidan dan akwai dai daga cikin gidajin emran dake nan cikin zariya da sukoma a ciki saboda za'a rushe gidansu zee gaba daya kuma har wani fili dake gefen gidan su angama ciniki ansiya za'a qara dashi duka domin amusu gini erin na zamani kafin matsowar lokacin auren akeson angama aikin sukuma ciki abinsu, dan koshi abinda yasa za'a gyaranshi saboda lokacin da daddy yace sutashi daga gidan sukoma cikin gidan da yabasu, alfarma baba yanema akan yafison gidansu na gado wanda suka gada shida qanwar sa akan yakoma wani gida, daddy bayja ba akan zancin, shiyasa yace toh sudan tashi zuwa kwana biyu domin a gyara gidan,
zee tasha kuka harta gode Allah kokadan batason wannan auren sam" kunyar mamy da daddy takeji tana matuqar jin nauyin su, shiyasa takasa musu,
su raliya kuwa qwarai sukajiwa 'yar uwar su, dadin wannan auren zata huta matuqa harda su ma dasuke atare da eta, uwa, uba samun handsome kamar emran ay wllh tacira tuta, ashe dik wannan rikicin nasu daqin junansu dasuke ashe Allah yaqaddara, mata da mijine ko ya za'ayi zaman wannan auren??
hafsat qinbiyar gwaggo tayi da zata tafi hakama sakenat su acewarsu suda komawa gida sai sunraka zee dakin ta, ko zasu koma, eyayinsu basuja ba, dan sunga yakamata subarsu sufara shirye+2 bikin tinda ba time ne a akwai sosai ba, suma dan kawai sutafi suyi sabon shirin bikin ne, yasa zasu koma,,
a Abuja kuwa duk wani shiri da ya kamata uwa tayi na bikin danta ko d'an-d'an gata mamy nanan na famanyi tare da 'yan uwnata da qawayen ta, matan many+2 mutane da matan sarakuna, suna taya mamy shirye+2 biki,
Yanzu antsaida magana zuwa nan da jibi za'a tura manya zuwa kai kuddin aure emran gidan su zee,,
Mamy samun tayi cikin amintattun qawayen ta, cikin wa'anda ba suda aure zawarawa kenan, kuma tsofaffin 'yan business wa'anda edanun su, suka bude sosai gurin yawon qasashin duniya, toh su mamay ta tura kusan qasa Hudu akan suje su hadu lefe da ba'a ta6a yinshi ba aduniya,
hatta Ankon da za'a fitar na biki mamy wata tasamu ta koma tura ta wata qasa domin ayomusu nasu na mussaman wanda sukadai ne zasuyi amfani dasu,
cikin wannan shirye+2 bikin ne mamy tasa aka fitoh da khaleefa daga gurin da yake tsare dik ya kwamtse yayi duhu yayi laushi gaba daya ya canza, kafin mamy tasa afara bashi kulawa ta musamman dan yadawo dai+2 kafin daddy ya Ankara,
Haka Kuma tabashi tabbacin cewa ba zasu ta6a shirya ba harsai yaneme afuwar zainab...
kwalliya ce suke ta faman tsantsara wa, ga dukkan alamu fita zasuyi wani guri dikan su sun shiry *(Afra, Raliya, teema, Hafsat, sakeenat,)* zee ce kadai suke jira data shiga gurin wanka tindazu, raliya ce tamara cewa nikuwa meye wannan amaryar take ne a toilet tun dazu sai kace mai janza fata, ay kamar jira Hafsat keye ta amshe zancin da cewa ke kuwa raliya banda abinki ay kinsan da zaran aka cemeki ankawo kuddin aure gidan su yarinya tohhh komy nata sai kiga ya canza,
enji ubanwa suka jiyo muryar zee dake fitowa daga cikin toilet kingaki Allah yarinyar nan kikiyaye ne, dukan su kwashewa sukayi da dariya kafin Afra tace gaskiya nidai kudai nawa aunty na, haka dan gsky yanzu kam bazan dauka b.... Hararar da zee ta watsowa Afrane ta tsayar da eta dag qarasawar zancin ta, gaba dayansu dariya suka koma kwashewa da eta banda zee da takejin sun matuqar bata haushi da wani zancin kiran ta amarya da sukayi,
sakeenat ce tace shin ni kuwa na tambaye ku jiyafa naji baqi sunzo gurin kawo kuddin aure shin ko kunjiyo mana tsegumin ko nawa ne aka kawo, cikin zaquwa Hafsat tace enban da abinki sakeenat wannan tana wuce tayi 2000 lolz.
turarin da zee ta dauko zata shafa ne, ta wurgowa Hafsat gocewa tayi kwalban bai sameta ba, sai dariya sukewa zee ganin da tayi zasu mai data wata eri ne, shiyasa tafita batunsu taci gaba da abinda take, esa tayi gurin closet dinsu na tufafe tare da ciro wata a tamfa mai kyau wacce ba tada color da yawa sosai, sai hijab dinta milk saboda a tamfar tama akwai milk, dikan su kallon mamaki suka bita dashi kafin teema tace zee meye haka, yazaki wani saka mana hijab dan wulaqanci muda zamu tafi supermarket bafa cemiki mukayi gurin walima zamu tafiba ko kuma gurin Harda, zaki wani dauko hijab kisaka mana sai kace wata kakar mu, sai da tabari dik suka gama yima tsiyar su dariya, sanan tace tohh bari kuji dashi naga damar tafiya kuma wlllh bazansa gyale ba, tinda naga abin eskanci ne, daman fa ba asun raina zan tafi ba, Allah edan kuka matsaman zanyi zamana naqi tafiya nagani edan da akwai mai sani dole,
Allah yabaki haquri sukace atare, haka dole sunaji suna gani suka qyaleta tasa hijab din ta, a tare suka fito sunata cece kuce, dakin mama suka shiga suka mata sallama akan zasu tafi tohh daman mama tasan da maganar zuwa supermarket din, shiyasa addu'ar dawowa lafiya kawai tamusu suka amsa da ameeen suka fito, da motar sakeena ce da tazo da eta zasu tafi dan momy lokacin da zata koma ta jirge tatafi
wai niko na tambaye ku wani supermarket ne zamu tafi wanda ya mugun haduwa raliya ce ta riqe baki tare da cewa tabbbb akwai wani supermarket ne da zamu tafi baya ga,
*E. Y. U MALL*
ay enajin ba gurin da ya kaishi duk afadin garinnan haduwa da kaya masu kyau dik wasu masuji da kansu anan suke siyayya, ay atare sukace muje gurin saboda Afra ce dik qarfin tafiya dikan su tace kowa yaza6e abinda yakeso komy kyansa komy tsadar sa zata biya saboda tanason suyi fitowa ta musamman amatsayin su na qawayin amarya, ay dikan su ba qaramin dadi sukaji ba, kuma gaba dayan su ba wanda yasan MALL din na emran ne, saboda sunan da ba'a fidda ba yanda za'a gane, har kuwa Afra dan kokadan eta ba tada labari ko masaniya akan erin kadarorin emran,
Chapter 49 · 0% Book details