← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 60

Sashe 56

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(108-109)* cikin kwanciyar hankali taketa baccin ta gaba daya ta sha'afa batayi sallah ba sam bataji ba, dikda ko akwai masallacin Emran dake qofar gidan kuma ga agogo acikin dakin amma saboda gajiyar da tayi da kuma tsawun lokacin da tadauka kafin tasamu natsuwar bacci erin haka harta manta shi yasa ma yau ta makara batasamu sallah Assuba ba.
Addu'a tafarayi ta tashi daga bacci cikin yanayi na erin baccin bai saketaba edonta yakai kan agogon dakin" qarfe 8:06am, tagani wata eriyar zaburace tayi cikin sallalami ta sauko daga kan gadon tanufe cikin toilet da saurin ta, ruwa ta sakarwa kanta kafin ta dauro Alwala tafito, dadduma ta shimfida tare da tadda eqama tafara sallah.
zaune yake cikin parlour bayan mamy ta ayko driver da brkfast dinsu masu gadin gidan ne suka kawo a 6angarin masu Aykin gidan sukuma suka hada tareda da wanda suka girka suka jera akan dinning, lokacin da yasauko yaci uban wata shadda tamasa kyau harta gaji, saida yajima a zaune cikin parlour yana danna laptop dinsa sannan ya esa gurin dining area, sam kasa yanda za'ayi ya zubama kansa abinci yayi, ana haka yaji budewar qofa tare dajin wani daddadan qamshi ya ziyarce sa amma bai juyoba ellah ci gaba da dannan wayarsa da yake.
zee da tafito taci kwalliya cikin wata atanfa mai ruwan zaiba ta mata kyau sosai tayi daurin dan kwalin nan erin mai step dinnan yayinda taidda gashinta ya zuba a gadon bayanta, dukda ba wani make up bane ke a fuskara ta, amma shigar tamata kyau mussaman da dinkin ya dan kamata, sosai take karantar yanayinsa, eta abinma mamaki yake bata na ace shi mutun duniya komy bai eya ba, tana matuqar tausayawa erin rayuwar da yaza6awa kansa amma shi taga kokadan ko ajikinsa, esowa tayi a hankali gurinsa tare dasa hannuta ta kar6e wayar dake hannusa tare da cewa gsky yakamata na dauke selfie
naga ko nayi kyau, gaba daya numfashinsa daukewa yayi lokacin da tadan raqufu ta kar6e waya erin yanda yaji dimin jikinta ba qaramin wani hali ta sanyashi ba, kansa yadago cikin tanki fuska da muryar nan tasa mai sanyi yace Meye haka,? Kina haukane zaki kar6an man waya?
zee da tafara daukar selfie tana wani juye-juye agaban sa cikin gayya daman tamasa haka, ta tsikayo muryar sa yana mata magana, juyowa tayi tare da daga d'ayar girar ta sama " tace wayar ka kuma? Ay wannan wayar daga lokacin da nakar6eta tazama tawa kamata wayana na hannuka ne, so karma ka qara maganar wannan wayar dan zan eya koma kar6e wannan dayar, sosai ya tsare ta da edo kafin yace banason yawan surutu kibani wayana zanbaki naki yace cikin wata murya ta Alamar yaqosa da zancin,
wani qayattacin murmushi ne zee tayi kafin tace kaga nayi kalan kar6an abunda ya dade a hannuka ne, ko wannan ba'a hannuna zan ajiye ba canjin ta za'aman dan bazan eya riqe abunda ya dade a hannuka ba dan gudun shafuwar erin halayin ka, Allah natuba namata fa yanzu wai kai mijinane. Hmmmmm tayi wani murmushi kafin tace Allah da badan haka ba ko.. sai kuma tayi shiru kafin tace bari dai nazuba ma abinci koshi abisa umarnin Allah da manzonsa.
tuni ya daina mamakinta saboda gaba daya shi yanzu Al'ajabin zee yafara bashi tsoro, daman shine yayiwa gudu yarinya qarama kuma marar class a sanya kawai tarainasa a gaskiya shi ancuce sa.
harta gama zuba masa abinci tayi shigewar ta sam bai kulaba saboda ya fada kogin tunani Allah ya esa kawai yakewa zuciyar sa dan etace ta kaishi da haka, dan da bancin son dayake mata wllh da yadade da daukar mumunan mataki a kanta,
yau gaba daya agajiye take saboda baqin da suka tazuwa mata sallama cikin baqin kuwa hardasu raliya saboda gobe jirgin safe zasu bi sutafi, nasiha su momy da gwago suka qara mata harda kukanta yanzu yanda zatayi rayuwar kadaici, mussaman Afra ko biyo su raliya tayi tazo taqi saboda Emran ya riga yaqara sanyawa Afra tsoron sa, tarasa yanda zatayi mussaman yanxu data rakasu tadawo cikin parlour sai tajita tsint gashi batasan part din da masu Ayki suke ba bare taje su debe mata kewa, haka ta zauna har bayan esha" dan Emran tundazu suka fita shida qasim saboda sallama da abokansa da sukazo daurin Aure, shiru shiru har 9 tayi bataji motsin komy ba sai na tsintsaye har tsoro taji yafara kamata sai taji Alamar bude qofe sau daya ta waiga taga dayan security dinsane yabude masa qofa yashigo waya na a kunnesa da alamu wayace yake mai muhimmanci, ciki-ciki yayi sallma etama zee dake zaune kan daya kujerar tana dan karanata wani qaramin liitafi na Addu'a tarage volume din tv tana karantawa, a gajiye ya zauna yana cigaba da wayarsa ganin haka da zee tayi ne taje ta dauko drink da cup ta ajiye gabansa tare da tsiyaya masa cikin ladabi ta duqa tare da miqa masa, da kamar bazai kar6a ba, sai kuma ya kar6a tare da cewa yanzu dole sai nazo za'ayi komy? can kuma a hankali yace toh ensha Allah nan da 2 weeks zanzo san yakashe wayarsa a hankali yake kur6a lemun har cikin ransa yaji dadin haka saboda yana matuqar jin qishirwa sosai yaji dadin abinda tamasa.
ji tayi yakira wayar qasim tare da roqon qasim dan Allah ya gayawa mamy tafiya takamashi zuwa England tohh yasan edan yasanarwa mamy zata eya cewa wani abu, tohh bataji dai abinda qasim yace ba sai taji Emran yace dawa? Allah kiyaye yayi tsaki yakashe waya.
dik da bataji abunda qasim yace ba tasan maganarta akayi dan haka batace komy ba taci gaba da karatun ta, kamar daga sama taji Emran yace ki bani sim card nawa dake cikin waya enada buqatar su
fita eskarsa tayi dukda taji abinda yace amma bata kulashi ba tsareta yayi da edo yana saqa wani abu a ransa can yaji tace batare da ta kalle ko gefinsa ba tace, kana eya jiran nagama abinda nake saboda wannan abinda nake yafi wanda mutun yake son sakani.....
Ay babu zato ko tsammani taji...........
bata ankara ba taji ya dalla mata baki saurin dago fuskanta tayi sukayi edo hudu dashi kafin yace mata cikin sanyin muryar sa, kokusa karkiso kirainane Allah dan ranki zai matuqar 6aci.
bakinta zee tariqe yayinda takejin matuqar zafi agurin a ranta take cewa lallai da gaskiyar Afra wannan mugune na gaske" amma afili ko kusa bata nuna shakku akansa ba ellah tsareshi da tayi da edo cike da tsiwa ta tashi tsaye ta nufe dakin ta da gudu kafin ta rufe qofa ta daga muryar ta yanda zai jita tace Allah edan ka koma man haka bazan qyaleka ba sai narama taja qofa tarufe tana maida numfashi.
shima murmushi yayi mai qayatarwa kafin ya kwashe kayansa ya nufe sama.
juye yake tayi akan tsaddadin gadon sa yarasa abunda ke masa dadi ba abinda edonsa ke nuna masa erin lokacin da ta tsareshi da edo laptop dinsa ya janyo a hankali tare da bude ta pictures dinsune na dinner wanda akayi ta daukar su lokacin da a keta musu liqi, edanunsa ya kafe akan fuskarta bai san lokacin da ya dinga shafar lallausan sajinsa ba yana murmushi a hankali a fili yace anya bazan qware kaina ba kuwa saboda wllh enajin son yarinyar nan tamkar namutu. Wata zuciyar tace mishi gaskiya da girman ka yayi matuqar faduwa, wata zuciyar kuma ce mishi tayi kai ko zaka dawwama cikin qinci da Azabtar da zuciyar ka.
Emran yagama yanke shawar daga gobe zai fara nunawa zee erin tsananin son da yake mata koda kuwa bazata kareshi ba...
[4:40PM, 2/23/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 56 · 0% Book details