← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 60

Sashe 41

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(72-73)*... kallon sa mamy tayi kafin tace toh menene?
bazaka sanar dani ba harsai kasanya ni natashi?
a hankali yace a mamy kiyi haquri, ki daure muje kigani plss, yafada cikin sanyin muryar sa,,,
toh naji tashi mutafi tinda kamatsa...
Afra tayi saurin cewa nima mamy zantafi....
kallon daya watsa matane ya katsar da eta da abinda tatashi fadi,, mamy ce tace kema zaki tafiko uwar gulma ko kinji anfadi sunananki,,,
Yi haquri mamy da wasa nake,,, kyaji da shi kai kuma mutafi" atare suka fita shida mamy cikin takonsa na esa,
Afra kuwa kasa hanquri tayi tatashi cikin sanda tamkar wata munafuka tana tafiya a hankali aranta tana maganar zuci,, haka kawai shi wannan yazo ya takura ka ya hanaka saqat toh nima sai nagani naga menene ne, a ba'ason mugani,,, sai kamar tayi nisa dataji mutse tayi sauri ta dawo ta zauna...
ciki da mamaki mamy ke kallon securities da suka kewaye wani mutun sun kakkafeshi da
Kuma da alama yasha duka,
mamy tayi saurin cewa meye haka meya muku dazaku mishi haka?
kallo daya emran yawa amintaccin security dinsa yafara gyaran murya dan shi baya magana agaban securities dinsa...
security yafara wa mamy magana cikin girmamawa, yace ranki yadade wannan da kike gani yanada sa hannu gurin 6acewar yarinyar nan munsameshi dumu2 amma bari kiji ta bakinsa...
cikin rawar jiki mutumin yafara cewa hajiya kiwa girman Allah ki tausaya man wllh Allah banda masaniya gurinda akakai yarinyar nan nidai nasan an cilasta ne dole akan nagwade gidan su, kuma nayi musu hakan badan naso ba,, amma wllh hajiya bansan enda take ba,,,
cikin tsananin tashin hankali mamy ta dubeshi cikin takaici dajin haushin sa, tace yanzu dakai za'a hada baki acuce 'yar mutane, anya kana tsoron Allah kuwa??
ni yanzu abinda nake so nasani, kafada man wanene yasanya ka kayi wannan ayki,?
shuru yayi baice komy ba sayda securitys suka qara tusa masa bakin
a wuya sannan yafara magana dik wandon dake sanye da shi ya fitsareshi tsabar tashin hakalin da yake ciki,,
roqon mamy yaci gaba dayi akan tamishi rai ta taimakeshi, shi a gaskiya bazai eya fadar wanda yasashi ba,,
tohh shikenan tinda bazaka fada ba, kushiga da shi ciki kumishi dik abinda kukaga damar yimasa harsai yafadi wanda yasashi wannan mummunan ayki...
tana gama fadar haka ta juyawarta, ta koma ciki tanaji yanata faman roqonta tayi banza dashi,,
emran da tun dazu yake faman dannan waya ganin mamy tatafi shima ya juyawar shi yatafi securitys na dafa mishi abaya,,
shi kuma mutumin suka nufe wani 6angare da shi yanata faman ehu yana roqonsu amma tamkar zugasu yake...
haba mama tayama za'ayi a bari wannan abun yafaru,, ace wai wacce batanan etce za'a daura mata sure,,, yarinya nacan cikin quci, yanzu koda ace Allah yayi dawowar ta,,
maimakon tasamu farin ciki edan tadawo saboda tafito a cikin qunci, sai kuma ace ankoma" asanyata a cikin wanni quci wannan ma quncinma, nahar abada wanda baya gushewa, allah,,,bai san mutumin nan ba mugun dan son mata bane,, sannan taya wanda ke bada katin shiga asibiti ace salary dinsa ya kai da har zai kulamana da eta, yabata farin ciki,,
wllh nasan halin zainab matuqa, da wuya wannan abun edan akayishi tazo ta riskeshi nida ke ne zatafi jin haushi akan baba,,,
dan Allah mama kitausaya wa, 'yar qanwata kimishi magana abar wannan maganar...
numfasawa mama tayi kafin tace kayi haquri masu'd wllh ba yanda banyi da mahaifinku ba,,, akan kada ayi abunnan da kukana da hawaye na,,, amma karkaso kaga erin cin mutunci da toxarcin da yaman ya kuma riga ya rantse da Allah, akan edan har naga ba'ayi wannan auren ba, tohh sai dai edan baya numfashi a doron qasa,
yakake son nayi da baqin cikin rashin zainab akusa dani koda baqin cikin mahaifinku,, salon kasa naje naqara janyowa kaina wani 6acin rai,, kai ma kuma kokusa wllh banma ezini kamishi maganar nan ba,,, dan kasan halinsa sarai, abinda kawai zamuyi shine muci gaba da addu'a, Dan Allah kadai ne, zai eya yayimana magananin matsalar mu...
kaje kadauko khaleed daga makaranta naga kamar lokacin tashin su harya dan wuce...
cikin mutuwar jiki ya miqe jinshi yake wani eri, ko jiya saida zuciyar shi, tayi ta mishi zafi cikin dare, yanama gudun kada ciyonsa yatashi...
tashi yayi yafita zuwa gurin dauko khaleed daga scol..
su zainab kam har ansaba da rayuwa cikin duhu, ni kaina yanzu edan naga zainab bazan eya gane ta ba, ban hana ko eyayin ta ba,,
muryata bata ma fita saboda tsabar kukan da take kullum, ga mura tamata yawa ciyonta yayita tashi ji take tamkar ba tada wani gata a duniya, rayuwa takoma mata wani eri...
ta tsane mutumin da yamata wannan abun ya sakata a cikin wannan mugun hali, ya rabata da eyayinta da kowa nata,, wllh daga shi har dan uwansa ji take ko mutuwar ta tafiso akansu bata qaunar su kokadan...
******************
Abokina naga sai wani jin dadi kake fa yau saboda kawai xaka tafi gida,,
murmushi khaleefa yayi kafin yace masa'aff kenan ay yau jina nake tamkar yauce ranar sallah kagafa nadade banje gida ba,,, dik da qwarai nake son natafi lokacin da ena najeriya tohh kuma ena tsoron abba, shi yasa ban tafi ba, amma kaga yanzu tinda Allah yasa munyi futu kuma kaga futun nada dan yawa, zanje na zauna cikin family na naji dumin jikinsu suma haka, daga nan zan tafi gurin waccan tsinanniyar yarinyar dan naqara tabbatar mata da qodirina kuma acikin wannan tafiya tawa nake son a daura mana aure da eta...
abokina kenan kai dai wllh bazaka canza ba,, tohhh Allah ya taimaka ya qara rufa asiri, bari ni nafita naqara yowar 'yar tsarabar da zanje da eta gida...
~:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::~
Afra ce na hango tanata faman safa da marwa tsakanin kiching da parlour sai faman jera abinci ake akan dining area, daka dube fuskarta zakasan yau acikin farin ciki take, mamy ce take saukowa qasa a hankali har zuwa cikin parlour qamshin girki dika ya cika cikin parlour kafin tace tabb lallai afra wannan girki haka gaskiya Zainab ta kyauta data koya miki girki,,
dik da koni ban kula da shi acikin parlour a zaune ba,, amma tarin da naji nashi ne yanayi lokacin da y qware sakamakon juice din da yakesha,, gefen shi mamy ta kalla kafin tace a..a yaushe kuma kashigo..?? shiru yayi baice mata komy ba,
kakosan yau khaleefa zai dawo,,
a hankali ya dago kansa ya dube mamy kafin yace Allah yadawo dashi lpy ya maida kanshi ga kallon laptop din dake gabansa yana ayki,,
*( 2 hours later)*
khaleefa na cikayo kan dining anata kwasar garar da Afra tayi masa dik da ko akwai daruruwan masu ayki haka ta dakatar dasu dan kawai yau tanason ta burge brother dinta, ta nuna masafa yanzu ta eya girki tafuta da tsokanar sa,,
emran kawai yaketa aykinsa ko gefen bai kalla ba, saboda shi acewar shi bayacin jagwalgwalon da Afra tayi, mamy taci magana harta gaji haquri kawai yabata,,
jin sukayi an bude qofar parlour security yadan shigo da sauri tare da cema emran sorry sir, nashigo batare da ezini ba, wanda yakewa magana ma yi yayi kamar ba dashi yake ba,
kamar daga sama yaji security nan yace sir, mutumin nan fa yace zai fadi wanda yasashi su dauke yarinyar nan yana buqatar ganin ku,,
wata dagowa yayi kafin yatashi, su mamy ma, atare suka miqe tsaye ba kamar khaleefa da bai gama fahimtar enda zancin ya dosa ba, amma kasancewar yaji kamar anyi maganr yarinya yasashi fargaba,
dukan su bayan security sukabi har zuwa dakin da mutumin nan yake,, edo hudu sukayi da khaleefa da mutumin nan atake wani erin tashi hankali ya ziyarce khaleefa da tinda yake duniya bai ta6a kasancewa aciki ba.....
[11:25AM, 1/26/2018] Official sa'adat Alkali:

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*DEDICATED 2 ...* ~<><><><><><<><~
*_BATUL ADAM JATTKO_*
*(marubuciyar Damata)*
*Ana tare*
*MY DAUGHTER*
Chapter 41 · 0% Book details