← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 60

Sashe 18

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[10:38AM, 1/13/2018] A:

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
_*SAUDATU CE... burin zuciya tashiga 6argo, har jijiya alkawari dama nariqa mai sona bazan barta ba,*_
_*so ya sarqemin zuciya yabu jinina ya kewaya saudat ce inban ganta b zan cigiya ko in tambaya, tinda na dauko alqawari ko nai nisa zan waiwaya, SAUDATU kin zan raba gardama wacce ta kaike bangan ta ba, nayi aminci na gasgata so komy na iya, haddasa banda kamarki nan duniya indai har babu, UWA UBA...*_
_I'am really luv u so much SAUDAT
my lovely sis
wannan page din na sadaukar dashi akan sis SAUDAT, ana tare erin kyakyawan tare dinnan
~<<<<<<<<<<<<>>>>>>>>>>>>><<<<<<<<<<~
*(39-40)*... turus sukayi dukan su ganin da sunkayi daga emran har affan azaune zamansu ko wannesu na danna wayawar sa ba abunda ya da mesu ga zee kwance aqasa shame2 ba numfashi dikan su sukayo kanta sai a lokacin mamy ta dago kanta tana cewa waiko kunada hankali kuwa ubame kukeyi a zaune bazaku tashi mutafi ku dauketa mutai asibiti ba dan wulaqanci qiri2 kuna ganin yarinyar mutane a kwance dan rashin emani kuke a zaune kuna danna waya ba abunda ya dameku kuma wllh sai kun fadaman abunda kukai mat....
bata eda maganar taba emran yadafe zuciyar sa yana wani erin numfashi sama2 kamar wanda za'a dauke ransa ay nan danan aka koma rikecewa musamman mamy daba tata6a ganin emran hakan ba nan kuma aka koma rikicewa kafin mamy tace da yusra d momy sukama zee sukaita cikin mota tace ma affan ka kama emran muje asibiti cikin tashin hankali take magana...
a..a mamy yanxun nan bari nakira wani family doctor dinmu y dubashi ay yata6a yin hakan ay a lokacin muna Cairo basai munje asibiti ba kawai kuje kukai waccan yarinyar ni zankula da shi...
mamy badan taso ba tabar emran tatifi alhalin taga erin halin da yake ciki dan kar aga tacika sonkai ne Allah da bazata eya tafiya ta barsa ba.. khaleed kawai akabari gida har baba da yayi niyar tsayawa affan yace gara yatafi tinda doctor nanan zuwa..
meye sunanka? Affan ya tambaye sa, khaleed yace sunana Abdullah amma khaleed ake kirana, ywwa khaleed kunada ruwan zafi kuwa aba wannan marar lpy?
a.. a bari dai na dora, a..a ka eya ne, ehhh, ywwa toh maza kakawo man kaji, khaleed yace toh tareda fita daga cikin daki da sauri yanufe kiching..
ahankali yabude edonsa lokacin dayaji khaleed ya futa kafin affan yasheqe da dariya, ahankali amma fa ka eya acting wllh...
a toh d fa banyi hakan ba, wllh mamy samu daukar qazamiyar yarinyar nan zatayi, Allah ko enajin dana amaye dika hanjin cikina, ya za'ayi ma, nata6a mace haba wllh bazai yuba..
affan yace gaskiya ba kada dama aini tin lokacin dana ga kana ya tsinar fuska lokacin da mamy ke maganar mudauke ta, aje hospital da eta nasan cewa akwai qura toh tinda kafara wannan abun n harbo jirginka shi yasa nima, nabaka taimako na cikin gaggawa...
kuma wllh abunda kawa 'yar eskirin, yarinyar nan kaman dai2 yanxu kawai" katashi mutafi gida kafin su mamy su dawo ka chanja kayan nan...
hakan kuwa akayi suka fita atare motar da suka shigo eta suka shiga driver yajasu suka tafi
da qyar likitoci suka samu nasarar dawowar numfashin ta, kafin akaita dakin hutu,
sai a lokacin hankalin kowa ya kwanta, sannan baba ya dubi mamy, yace hajiya fa yaka mata kikira kiji jikin yaron nan, batai musu ba kuwa, takira wayar affan lokacin emran na gurin wanka sunan mamyn emran yagani kan screen din wayarsa saurin dauka yayi, ya gaidata kafin ta tambaye shi y jikin emran din ?
mamy d sauqi yanxu ma muka dawo gurin doctor gamashi nazo dashi gida ya dan watsa ruwa, idan kika gansa tamkar ma wani abu bai sameshi ba, yasha.magani ma gashi can a gurin wanka, daya gama ya shirya gamunan dawowa gidan,
hamdalah.. mamy tayi kafin tace masha Allah affan agaishe ka fa da qoqari, Allah dai yamaka albarka, sai kunzo
ameen mamy kafin su yanke waya..
sannu ko zainab a hankali take daga kanta inane ke miki ciyo yanzu ? tace bako ina toh yayi kyau, mamy taqara tacewa sannu kinji, tace yawwa..
toh ay yanzu Alhamdulillah zamu eya tafiya gida ko? bari naje likitan ya bamu sallama daman yace yaga jikin ta, da sauqi sosai.. gara mutafi kar abar yaran can gida su kadai..
bayan sun eso gida ne, zee na tashiga gurin wanka dai2 lokacin dasu kuma su, emran suka eso gidan sunfi 15 mnt da esowa qofar gidan, kafin affan yasamu nasarar fitowar emran a cikin mota da qyar,
khaleed suka hadu dashi zai fito cikin gidan cikin mamaki yake kallon su kafin yace, a..a su yaya ( da yake tinda bai san sunayin su ba yake cewa hakan.)
binsu yayi har cikin parlour bayan sun zauna ne, yace
ina kukaje ne, nadafo ruwan zafin da kace naje n dora na kawo parlour na tadda ba kowa...
kanshi emran ya dan shafa kafun ya mai da hankalin sa kan wayar sa, khaleed ya dago yana kallon shi, yace yaya handsome kana da kyau sosai, amma kuma meyasa baka magana kokai kurma ne?
affan yace wannan sunan kuma yasamu khaleed? yace yaya handsome yana magana baya dai yi ne sosai,
toh meyasa?
ba komy haka shi yake,
etama aunty zee haka take wllh sai wataran kawai take magana,,
affan ne ya sharar da xancin khaleefa da cewa ba aykinka akayi ba?
ehhh daman baba ne yace wai yaji tsayuwar mota naje na duba ko kune, yace nace muku ku wuce cikin gida
toh shine kuma katsaya kana janmu d surutu ko? bayan kuma aikoka akayi
toh ay namanta ne
tohm ay sai katashi mutafi kamana eso ko?
yakoyi saurin miqewa a tsaye mutafi yace
toh sarkin bincikar waya ay saika tashi mutafe kafun mamy t kira..
tamkar wanda kejin kasala y tadda kansa ahankali kafun ya kalle affan, ni Allah abun nan y eshe ni yawon nan bana sonsa kokadan yafara esa ta...
toh haka zaka daure mutafi, kamaci arziki Allah da har yanxu mutanin garin nan basu san kana gari ba, da lokacin ne zakaji jiki, amma shiga kawai cikin gida shine wani yawo, tinda kai kariga kasaba da qunshewa tamkar mace..
ya zamuyi haka zakayi hanquri tinda mamy ce, yanda tace haka zamuyi koda kuwa ba masu dan haka kadaure mutafi kawai, yaron nan na a waje yana jiran mu...
tu kubude mana taro da addu'a mamy ta dube su,, affan ne yabude taro da addu'a zee na can lungu dan eta mugun ta kaicin emran take ji, bata buqatar ganin sa kokadan...
bayan anshafa addu'a kowa ya natsu yana saurari,,
mamy ce tafarawa eyayin zee bayanin dik yanda zee tafada mata, da kuma eta kanta abinda taxo dashi akan tanason ayi maganin matsalolinnan dake faruwa atsakanin su.. kai affan mamy t dube affan dake zaune kusada emran kafada man tsakanin ka da Allah meya faru dazu har ciyon da keda zainab yatashi na sanyi,
tirya2 yafada mata dik abunda yafaru da abunda zee tayi hatta da yajin da tasanya acikin zo6on, yace danna sha naji lokacin datayi ehun tana cewa edon ta nikuma na dauka nasha kadan
taslima ko wannisu yayi kafin baba yace.
ayni yaro kaman dai2 wllh ba enda naga laifinka kokadan Allah yadad'a baka eko kayi mata abunda yafu haka..
daman nafadawa uwarki wllh dik randa kinka dawo saina sa6a miki mutuniyar banza mutuniyar wofi naso matuqa yayanki, na gari yaji erin abunda kikayi shida ke daure miki gindi, toh bari kiji
wllh! wllh!! wllh!!! kinji ratsuwar cikakkin musulmi ko? wllh ko kifitar da miji kwanan nan, ko kuma kibar gidannan, dan nagaji da eskancin da kike shukawa, dan haka wllh kwanannan ki fidda miji kona 6a6allaki anan gidan..
haba! Haba!! baban zainab wannan fa ba girmanka ba ne, yakake magana erin hakane? dan Allah kasanya wa zuciyar ka salama..
bari kawai Hajiya zulay ni kawai nasan yanda nakeji" tinda kinkaji narantse toh fa wallh ba fashi matsawar tana gidannan wllh kwana biyar kawai nabata edan ko bata kawo shi ba, toh zan bata dik wanda naga dama,
gyaran murya mamy tayi, kafin tace banqatse hanzarin ka ba malam, ina roqonka da abu daya.. dan Allah ena neman Alfarma......
*ALAHAMDULILLAH..*
_*A gaskiya ina matuqar godiya agareku masoya na da kuka kasance masu yimini addu'a samun lafiya gashi yanzu qafa alhamdulillah naji sauqi kamar ba'ayi ba da masu kirana da masu man magana ta PC dika ina godiya lallai qaunarku gareni ajini take nagode! nagode!! nagode!!! tabbas nasan lallai ananan tare
[10:38AM, 1/13/2018] A:
Chapter 18 · 0% Book details