← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 60

Sashe 39

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(78-79)* kusan securitys 8 ne suka shigo a bisa umarnin da mamy tayiwa qasim yakirasu,,
cikin kulawa ta dubesu kafin tace enason kutafi da khaleefa dik inda yakai 'yar mutane kudauko man eta kuje tare da shi yanzun nan kada kutsaya wasa ko a enane kai koba a garinnan bane yanzunnan nake so kukama hanya...
cikin girmamawa suke amsa mata kafin ta dube khaleefa cikin wani kallo da ni kaina nakasa fassara shi ko na menene?..
hanya suka bashi cikin rashin qwarin jiki yatashi a zuciyar shi kuwa cike take da haushin da takaici yanda asirin sa ya tohnu dab da lokacin da ya keson ya cika burinsa, bayansa sukabi har suka fita daga dakin,
mamy myda kallonta tayi ga emran kokadan ta lura hankalin sa kwata+2 tamkar ma baya jikin sa,,
kanta ta juya ta maida kallonta gurin qasim tace qasim abokin ka na buqatar futu kuje dashi ya watsa ruwa yasha magani tinda kaga ba sabawa yayi da wannan surutun da akayi ba anan gurin ba mamaki naga yanayin sa kamar ya canza ne...
tana gama fadar haka takoma maida hankalin ta gurin mutuminnan dake zaune atakure kallo daya zaka mishi kasan cewa ya matuqar yin nadama akan abunda ya aykata...
mamy tace kai kuma nadawo kanka kamar yanda nama alkawari zan sassauta maka akan hukuncin da za'ama
tohh ensha Allah zancika wannan alqawar, amma da sharadi kokusa koda wasa karnaji maganar nan awaje kamar yanda ka eya riqeta aranaka kaqi fada saida kasha wuya tohh haka nake son kaci gaba da adanata a zuciyar ka har abada,, hakan shi zaisa nayafe maka dikkan abunda natashi sawa amaka kana jina ko???
cikin rawar jiki yayi saurin cewa eh!ehh!!eh!!! ranki yadade wllh nayarda edan har maganar nan tafita aman dik hukuncin da akaga dama,,
wllh tamkar kin fadawa mamaci wannan maganar har abada bazata ta6a tashi ba, namiki alqawari...
tohhhh shikenan kai kuma ensha Allah yanxu zaka fita annan amma ka kiyaye ko bamu ba kaji tsoron Allah karka koma maimata koda kwatan kwacin haka,,
ensha Allah hajiya bazan qara ba, ayko yanzu ma wllh naga jarabawa,
qasim kiramin securities 2 sufitar dashi a gidan" haka qasim yaje yakirasu suka fita dashi daga daki sai xuba godiya yake tamkar zai are baki...
ni zanshiga ciki nashirya saboda zanfita munada taro na mussamman da zamuyi na bada taimako ga mata,,
tana gama fadar haka tayi hanyar fita Afra ma bayanta tabi suka fita a tare,,
kafarsa qasim yadafa kafin yace kadaure katashi mutafi kawatsa ruwa kamar yanda mamy tace...
saida ya6atawa qasim lokaci sosai yanafaman lallashin sa tamkar wani yaro akan yatashi subar nan yayi banza da shi ko motsi kafin yayi saida yadan dauke lokaci da qyar ya tashi sukabar gurin,,
~***************************~
shirye+2 bikin zainab da d'an abokin babanta ya kankama dan yau kusan saura sati daya a daura aure mama kam bayan da zatayi ta tarkata komy ta fawalawa Allah,,
baba kadai keta shirye-shirye biki sa,, sai kuwa gidan su ango,,
yaya mas'ud kam tamkar ya daura hannun sa aka yakeji,, tsabar baqin ciki,, khaleed kullum cikin zancin auntyn sa yake, wani lokacin edan yaje gidansu raliya ko teema haka zasu rungume shi suyita kuka shi yanajin kewarta sosai edan yagan su, suma haka sunajin kewarta edan suka gansa...
tamkar yanda kullum tasaba zama tin ranar da aka kawota wannan quntataccin gida cikin duhu toh ko yanzu hakan take,, wannan karon zaune take tare da kife kanta akan qafafuwata tanata tunanin 'yan uwan ta, dan eta tariga ta sadaqar da fita gurinnan
motsi taji alamar anshigo cikin dakin mamaki tayi dan mai kawo mata abinci bai dade da kawowa ba kuma edan ya aje by ta6a dawowa ba,
jitayi ana qarqarin bude qofa dakin da take fuskar ta, ta tadda ahankali tana jiran taga mai shigowa,,
haske tafara ganin ya gauraye cikin dakin dam zuciyar ta, taji ta buga da qarfi dan tasan tabbas wannan tsinanin ne, yadawo yau tashiga ukku shikenan ya kusan cika mumunan qudirin sa a kanta,
tinanin ta ya tsinke saka makon bude dakin da akayi da kuma wanda take tunanin shine,,
kafin taga wasu suma sun shigo, qara razana tayi amma batace komy ba dan tayi alqawarin bazata ta6a koma mishi magana ba koda kuwa yankanta taga zayayi,,
nunata yayi da dan yatsa kafin yace musu gatanan,,
daya ne daga cikin su yace mata, sannuki daman munxo ne abisa umarnin hajiya waton mamanshi, munzo mutafi dake ne gurin ta, kamar yanda tabamu umarni..
wani kukane ya su6uce mata na farin ciki babu wata+2 tatashi tashare hawayin ta tace mutafi dan Allah kuyi sauri kufitar dani daga gurin nan dan Allah dik ta wani rikice,, sosai suka tausaya mata saboda yanda sukaga tana kuka tana murmushi tabbas sunsan akwai wani 6oyayyin abu a nan...
basu wani tsaya bincike ba suka fita da eta daga gidan qwarai tayi mamaki da taga gidane qwalle daya cikin wani qasurgumin daji shi kadai ne agurin bazaka ta6a tunanin da akwai mutun a gidan ba,,,
tabbas taqara gasgata wannan mutumin baya tsoron Allah kokadan...
khaleefah ko haushin ta ne cunkushe a cikin ransa,, a zuciyar sa yake cewa wannnan yarinyar takuru Allah, dan wllh da na mugun banbance mata tsakanin aya, da tsakuwa,, yayi shigewar sa, a cikin mota daya suka kama hanya zuwa gida ashe cikin wani qauye ne dake cikin garin abuja ko qauyin ma, a cikin wani sunqaqqin daji,,,
zee sai zumude takeyi ta matsu su esa gida tawatsa wa jikin ta ruwa danji take tamkar anmata wanka da zuma tsabar dauri da take jin, jikin ta nayi,...
zaune suke su biyu a cikin parlour bayan da ya watsa ruwa amma yaqi shan magani, haka qasim yayi ta biyar sa yaqi ko kulashi, kwance yake kan doguwar kujera tare da, daura hannanu sa daya a kansa tamakar mai wani tunani tare da lumshe kyakyawan edanun sa,
yanaji wayoyin sa nata faman ringing amma ko juyowa baiyi ba, bare yakulasu qasim sai kallon ekon Allah yake baice mishi komy ba dan yasan ko yayi mishi magana ba kulashi zaiyi ba,,,
shi bama wannnan ne damuwar sa ba, lura da yayi da halin da yaga abokin sa, na cike ne, shi ne" ke matuqar damunsa kuma ba abun ya tambaye saba, wani qarin haushe mane dan yasan ba amsa zai samu daga gurin saba,,
daurewa qasim yayi ya taso daga gunda yake yazo har gurin sa, ya zauna dai+2 gunda fuskar sa ke kallo, kafin yace emran dan Allah inason na tambaye ka kuma ka taimaka dan allah, ka tankan koda sau daya ne, saboda wllh ena cikin damuwa matuqa da ganin ka hakan, dan tabbas abinda mamy ke hasashe a kan ka bashine ke damunka ba,,
enason kafa sani nine dai naka qasim da duk duniya bancin mahaifiyar ka, ba kada wanda zaka gayawa damuwar ka edan bani ba, kuma nine a duk fadin duniyar nan kaf bancin family ka, zanfi kowa shiga cikin damuwa edan har naganka acikin ta...
plss and plss ka taimaka kafada min tell me your problem??
shiru dakin yayi tamkar ba kowa a cikin sa, har na kusan tsawun 15 mint, qasim shima baice uffan ba kuma bai tashi daga enda yake ba,,
qafarsa yafara motsawa daga nan ya sauke hannun sa daya daura a kansa, kafin yabude edanuwan sa a hankali masu matuqar kyau da haske,, kallo daya yayiwa qasim ya dauke kansa,
cike da ezza ya fara motsa la6ansa cikin tsadadiyar muryar sa yafara magana..
ni kaina bansan abunda ke damuna ba, nasan dai ba haka nake ba, kuma nakasa tantance yanayi na da har ya sauya haka" enajin zuciya ta na yawan bugawa,, ena tsintar da tunanina a enda ni kaina bansan gunda ya dosa ba, ni kyana ina mamakin meke damuna ne wllh qasim edan nace maka ga abunda ke damuna nayi qarya...
nisawa qasim yayi kafin yace tabbbbdi, jam" babbar magana kenan, emran yanayin ka na kama da erin mutanin da suka fara tsintar kansu a tarkon soyayya basu sani ba,, amma fa bance kana daga cikin su ba, saboda sanin da nayi wa riqaqin ra'ayin ka, dan haka karkaji haushi n...
qarar bude qofa shine ya katsar da qasim daga maganar sa da yake, Afrace ta shigo da saurin ta hadeda sallama tana cewa yaya qasim mamy tace kuzo su khaleefa sun dawo tareda zainab tana fada tana juyawa da gudu ta fita...
a dai+2 lokacin da yaji afra ta shigo tare da cemusu su khaleefa sun dawo,, da qarfin Allah yatashi zaune daga kwancin da yake tare da dafe zuciyar sa, sakamakon qaruwar buguwar dayaji tayi,, kansa na kallon qasa...
saida qasim ya zabura danshi harya bashi tsoro ya dauka wani abune, tinawa yayi da abinda afra tashigo tafada musu...
nan fa qwaqwalwar sa ta shiga tinano mishi abubuwa da dama, tin daga kan lokacin da akace zee ta6ata emran ya kwanta ciyo zuwa lokacin da yayi waya da matarsa ya ambace cewa, za'awa zee aure yafasa masa wayar sa,, har ezuwa abinda yafaru yau da kuma yanzu...
Anyaaa hasashin shi ba gaskiya bane amma bari ya gwadashi yagani qasim ya fada a ransa...
dafa kafadar emran yayi a hankali cikin tattausar murya, yace mishi meke faruwa ne? ya daga fada mana su yarinyar nan sundawo taredasu khaleefa kayi wannan zaburar har da kuma dafe zuciya,,,naga yanayin ka ya matuqar canzawa?
kansa emran ya dago a hankali wata erin zabura qasim yayi, tare da miqewa a tsaye, saka makon ganin hawaye akan fuskar emaran dik da halin da yake ciki bai hanashi magana cikin qasaitar saba...
sannu a hankali yace qasim wllh zuciyata naman zafi qasim mutuwa zanyi ena matuqar jin haushi da takaice sakamakon abunda zuciyata ke qunshe da shi wanda nikaina bansa ko menene ba, qasim kasan yanda nakeji kuwa??,
a hankali qasim yace masa kayi haquri,, amma bari na tambaye ka kuma kafada man tsakani da Allah kada ka cutar da kanka, enason ensani _*KAR DAI....*_
[11:25AM, 1/26/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 39 · 0% Book details