← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 60

Sashe 50

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

<><><><><><><><><><><><><><
tohh amma dai kasan tare zamu tafi ko saboda ma'aikatan supermarket din zasufiyi mana bayani yanda ya kamata edan kana kusa, bayani na akan game da kayan da yanzu ake buqata a qaro, ko afitar da kuma maganar qarin salary dinsu kaga zuwa da kai yafi zuwa da saqo kaga nan take ayi maganar komy agaban ka ko kuwa?, qasim ya qare zancin sa yana kallon emran dake amfani da laptop dinsa dake kan qafafuwan sa yana shan juice tamkar baya so,
shiru dakin yayi da kamar bazai amsa ba, sai can ya dago kansa tare da cewa ok' daga haka yaci gaba da abida yake sai da yaqarasa sannan yamiqe dan shiryawa, qasim dai na zaune yana kallon sa bai ce masa komy ba,
kayane naji da fadi suke kwasa kamar hauka dik wani abu na buqata sun gama dauka nan Afra taciro *A T M*
dinta tabawa wanda ake biyan kuddi domin yacire dik kudin dayayi list na kayan dasuka dauka, su raliya kuwa kwashe komy duk sukayi suka kai mota zee kawai suke jira etada Afra dake ciki sufito sutafi domin mareci nayi, suna zaune cikin mota suna jiran fitowar su kawai sai ganin sukayi,
wata erin dalleleyar mota ce baqa wulik sai sheqe take tamkar lokacin aka fitar da eta acikin kwalin ta etace naga ta danno gurin, gaba daya ko glass din motar baqine wulikk, ko kad'an ba kama ganin wanda ke cikin motar, tafiya motar keyi a hankali har zuwa dai+2 gurin da qofar da ake shiga cikin MALL din motar tayi parking, gaba daya hankalin mutane ya koma gurin, ciki kuwa hardasu sakeenat dake zaune cikin mota suna jiran su zee, mamaki ne yakama mutane yanda su kaga wannan motar tashigo hardai+2 gurin da baiko dace ace anyi parking din mota gurin ba, kuma securities din dake gurin suna kallo basu tsayar da eta ba, ellah ma ganin da sukayi sunzo gurin motar da saurin su, tsayawa sukayi dumin suga wannan wane erin esashin ne haka, sundan jima kafin abude qofa qasim ne yafara fitowa qofar bayan motar kafin driver yafito da hanzarin sa, yabude dayar qofar ganin nayi qasim yadan leqa kansa a hankali cikin motar kafin ya fidda kansa kallon securities din gurin kawai yayi da hanzari suka matso kusa gaba daya kafin kace me duk ma'aikatan dake gurin na waje dana ciki sun hallara ay nan mamakin mutane yadada qaruwa wai wannan wanene?
jin sukayi qasim yace kufitar da duk wani wanda ke ciki, har zuwa lokacin damai gidan ku yagama abunda ya kawo shi, ay qasim baiko qarasa zancin sa ba, wa sunsu sukayi ciki da saurin su,
Afra dake bakin qofar hagu, atsaye tana faman jiran zee tafito sutafi edonta tazaro da qarfi dan hango qasim da tayi ta jikin glass din qofar ba shiri asace tabar gurin dan tasan tabbas tare da yaya emran yake daman tasan basu koma ba suna cikin garinnan,
dik wanda ke cikin gurin ba wanda bai fitova gaba dayan su, dayan security ne qasim yaga yazo da hanzarin sa, yana ce masa sir gawata yarinya can wllh taqi fituwa wai saboda bata gama abinda tazoyi ba, ba yanda bamuyi da eta ba, ko kallon mu taqi tayi, alama qasim ya masa da yashiga gaba sutafi
Afra ce tayi saurin esuwa kusa da enda sukayi parking din motar su tana cewa wai kunsan yaya emran ne yazo gurin nan, ay gaba dayan su edo suka zaro kafin raliya tace haba wllh ninasan wannan tsarin sai shi dan shi kadai ke yinshi teema ce tace tohhh ena zee din take tana ciki Afra tabata amsa, raliya ce takoma cewa kece kenan ango ne da amaryar sa agurin, kinada hankali kuwa Afra tafada cikin wata murya kin kuwa san ko waye yaya emran wllh toh en gayamiki shi ba ruwan sa da wata amarya kamar dai ba kusan yanda abunnan yake ba, gaba dayansu sai kuma sukaji jikin su yayi sanyi, tinanin suke yau kuma yazata qare,,
edonsa ne ya sauka akan zee dake tsaye kamar tana duba abubuwan datake buqata nan ko tagama daukar komy tsabar eskanci ne kawai na sai takai qarshi dik wani dan esakan da keji da kansa na wai dole sai kowa yafito zai shiga hankalin ta kwance take komy nata kokadan babu tsoro atattare da eta
aran qasim kuwa ganin da yayi bata kula dashi ba ne, hankalin ta na kan kayan gurin yasa ya koma tare da fita gurin azuciyar sa, yana cewa nasan arina wannan yarinyar qarshe ce, shi yasa take matuqar burgeshi, esa yayi gurin motar tare da cewa emran sai kafito tinda kasa kowa yafita, sai da yagama qasaitar sa sannan yafito a hankali nan take aka kara mishi lema
saboda akwai dan kingin zafin rana dik da marece ne amma da kingin rana,
koda yafito babu wanda bai nasa aransa ba, yace no wonder wllh shiyasa biri yayi kama da mutun saboda sunsan duk wannan abun sai shi kadai keyin shi, emran yusuf usman kenan yaro matashi maiji da kuddi da kyau ga ezza uwa uba kuma mulki,
tako yake tamkar ba yason taka qasa yayi kyau sosai harya gaji cikin wata erin gizzna mai matuqar tsada sai sheqe take tana qarawa dinkinsa ya dinku ba qarya, gless dinnan nasa kuwa na ga edon sa, amma kala-kala ne, kuma dukan su farare ne,
```shin niko kodai emran yasan glass dinnan na qaramasa kyau ne, shiyasa yake sashi
?```
[6:43PM, 2/14/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 50 · 0% Book details