← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 60

Sashe 28

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kafin driver yaja zainab su tafi da kashedin mamy tace kada ya kuskura yayi gudu sosai.. zaune yake a kan kujerar office dinsa, sai faman danna laptop dinsa yake sallama a kayi aka shigo.. wani mutunni mai d'an shekaru ya shigo tare da neman ezinin zama, batare ya dago a kan abinda yake ba, ya mishi alama da guri y zauna... saida yagama abinda yake kafin ya dago kansa edanunsa na 6oye cikin wani hadaddin farin glass wanda ya matuqar yimasa kyau.. mutumin yayi gyran murya kafin yace ranka yadade angama musu komy munce sudawo zuwa next week dan fara aiki, saboda tafiyar dakace zakayi, hannu ya dagawa manager sa, cikin taushin murya yace meyasa zaka yake hukunci batare daka kira kasanar dani ba, meye alaqar tafiya ta, da farawar su aiki maza tin kafin sutafi kasa a kirasu dasu dawo kafada musu gobe su fito gurin aiki, tareda tsagawa kowannen su albashin sa, dai2 gwargwado, karka koma man haka, sorry sir ayi haquri hakan bazai koma faruwa ba ensha Allah.. qofa yanuna masa alamar yafita.. cikin girmamawa ya amsa tareda miqewa yana qara neman afuwa sannan yafita.. raliya ce, tafara hangowa lokacin da suka shigo cikin unguwar su tana tsaye da etada wani saurayi suna zance a dai2 enda yayi parking din motarsa.. murmushi zee tayi tace a hankali oh salisu na raliya.. dai2 qofar gidansu raliya kuma dai2 qofar gidan su, zee tacewa driver yayi parking a gurin, mamaki zee tayi da taga har tafito daga cikin mota har kuma suka hada edo biyu da raliya bata ko nuna ta santa ba, har gurinsu zee ta matso tareda cewa raliya bako magana? ay wata erin ehu raliya tayi dan eta wllh kwata2 bata gane zee ba, ta canza mata gaba daya, ruqunqumeta raliya tayi sai da zee taga alamar zata kadasu qasa ne, ta tureta daga jikin ta, tare da cewa. Kedai bazaki canza ba wllh, ni dai kinga tafiya ta sai kin shigo, batako tsaya sun gaisa da salisu ba tayi gaba, gida tashiga khaleed tamkar ya dagata sama yakeji tin lokacin da mamarsu ta fada mishi auntyn sa nanan zuwa yakasa zama yakasa tsaye.. dan lokacin da tatafi, daya dawo gida a kafada mishi auntyn sa tayi tafiya kuma zata dade bata dawo ba, kuka ya dingayi har mama tagaji da lallashin sa tafita eskar sa, sai da yagaji dan kansa ya dai na.. bayan tayi wanka ne taci abince take tambayar jikin baban ta, mamarta tace yaji sauqi dan harma yafita kasuwa, yayanki kuma na gurin aiki yanzunnan zakigan sa yadawo.. Kai gaskiya mama naji dadi sosai da baba yaji sauqi harya fita.. kaya tashiga janyowa da tazo dasu wa'anda driver yasa yara su shigo dasu dan yaga alamar harta manta kayanta a mota saboda zumudi.. shikam ana sauke komy yaqara gaba, tinda lokacin da suka eso gurin shagonan yalla6ai daya fada mata cewa tayi sutafiyar su, tareda roqonsa dan Allah kada yasanarwa mamy, kota tambaye shi yace sun kar6o, shidai ya amsa mata kawai ne da toh... Raliya ce tashigo gidan tare da teema da raliya takira tasanar da eta zuwan zee a gari, nan fa sukayi ta zuzuta erin kyau da taqara da kuma canzawar da tayi, yayan ta ma yadawo nan ma, akaci gaba da fira tare da basu labarin Abuja, da kuma gidansu mamy erin kirkin da suke mata da yanda suka riqeta, da kuma labarin Afra yanda suka zauna tamkar 'yan uwa batare data nuna mata komy ba, har labarin zuwan da zatayi, ta fadamusu, amma sai dai labarin fadansu da emran ne kawai ne, ta 6oye bata fada ba, nan dai rarrabawa kowa tsarabar sa, cikin jin dadi suka kar6a tare da mata godiya, bama kamar khaleed da aka cikashi da kayan chocolate murna kawai yake... _*BAYAN WATA DAYA..*_ [10:40AM, 1/13/2018] A:
Chapter 28 · 0% Book details