← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 60

Sashe 15

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(33-34)*..likitoci ne dafifi akansa bayan sunyi nasarar shafe dik wani cake din da yashiga cikin idonsa suka mishi allurai tareda bashi magungunna.
tabbas baza a qyale wannan yarinyar ba wai yama akayi tazo nan gsky fa ena ganin dik yanda akayi turota akayi..
amma haka kawai ta neme nakasa mutun, kuma ko mutun ace erin emran, kuma ga dukkan alama eta ba mahaukaciya bace da hankalin ta sadiq ne keta wanan maganr,, cikin ta kai ce da abinda akawa emran
qasim shima sai yanzu yayi magana yace wllh nima yarinyar nan gaba daya tafara bani haushi ace shi mutun baya ta6a yafiya a rayuwar sa?
wllh sai kunga lokacin danake tausar yarinyar nan ina bata haquri akan abinda akamata nunamin tayi wllh komy ya wuce ashe qarya take,, daman aysha tafada man tace da wuya edan ta haqura! dan eta haka take wai dik aka mata abu syta ram......
toh ko ay yanzu zata koci, uban ta, dan wallh sai ta gane kurinta, wani ke mata abu tarama, wani ko wllh tayi kadan qaryar ta tasha qarya, bari ace tawa kamar mutun erin, emran" affan ne ke magana dan sarkin zariya, ( _nayi kuri da page dina lokacin da danace affan dan governor zariya ne sarki zariya nake son nace.._)
wllh zatasan ta debo da zafi affan ya kai qarshin maganar sa shima yana huci...
shima salman cewa yayi, ni bama dik wanan ba 'yan jaridar dake gurin suna daukar rahoto ana yadawa akowani tashar tv ta qasa dan nunawa duniya erin shagalin da ake,, toh yanzu nasan wllh ba enda wannan tozarcin da wannan yarinyar tayi bai kai ba, gaskiya! gaskiya!! Allah yarinyar nan bata kyauta ba.sannan tayi jarumta matuqa juriya, fada da wanda yafi qarfin mahaifinta ma bare eta..
dikansu shiru sukayi ko wanninsu zuciyar sa cike ta ke da takaici,, musamman idan suka kalle gefin da emran yake a kwance edonshi a lumshe tamkar mai bacci amma azahiri dik abinda suke fada yana jinsu,
sallama khaleefa yayi yashigo dauke da basket din abinci ya ajeshi a gefe gado kafin ya gaida su qasim dake gurin, bayan sun amsa mishi suka koma yin shiru, kafin khaleefa yace gaskiya yaya qasim dan Allah yarinyar nan kada abarta batare da an hukunta taba, kwatan kwacin abunda tayi...
karka damu khaleefa insha allah zata fuskanci hukunci, dik hukuncin da mamy tayanke da shi kanshi emran din,, shine hukuncin da yafi dacewa da eta...
ance dady baya gari ko?
ehhh yaje maleshiya tin wancan satin
yayi kyau gara ay da bayanan abun yafaru...
Tabbbbdi jam-babu enda abunnan da yafaru bai zagaya ba a duniyar nan,
gidansu zee ma labari yaje musu lokacin da su raliya suka ga abunda yafaru ba shiri sukaje suka sanar da mamar ta,, ba qaramin tashi hankalin suka shiga ba dajin abinda zee tayi, musamman baban ta da yayan ta..
cikin wani hadaddin parlour na hango mamy hakimce fuskarta ba yabo ba fallasa qarema zee kallo take tanata saqe2 aranta kafin tace...
menene sunan ki?
sunana zainab ta fada kanta na qasa,,
awani gari kike?
a zariya nake...
cikin wace unguwa?
unguwar ganye...
meya kawoki garin abuja?
nazone gurin kawo wata qawata amarya ce...
wace unguwa aka kawo qawar take?
a maitama
Unguwar nan kenan wane gidan?
zee tayi shiru..
meya hadaki da dana emran har kika za6e kimishi wannan ayka2 agaban jama'a?
sai lokacin ta dago kanta suka hada ido da mamy takoma mayar da kanta tayi shiru
dakefa nake inada abinyi
am!!! daman lokacin da yaje garin mune a zariya......
tin farkon haduwarta da emran da abinda yamata etama da abinda ta mishi har zuwa abinda yasa aka mata lokacin da akazo dinner da zaman ta gidan qanwar maman ta dika tasanar da mamy taqare da share 'yar qwallah datataru a qasan edonta tace dan Allah hajiya kiyi haquri, nasan bai dace nayi hakan a gabanki ba amatsayiki na mahaifiyar sa, wllh banyi hakan dan naci miki fuska ba, amma wllh akan dai abinda nawa emran kokadan banyi danasanin akan abunda namasa ba kokadan, dan ya wulaqantani wulaqancin da ba'a ta6a manshi ba arayuwata ba, na yarda aman duk hukuncin da za'aman man, ina maraba dashi ashirye nake na dauke ko wanni erine
d'an numfasawa mamy tayi kafin tace yanzu yaushe zaki koma?
gobe insha allah tabata amsa..
kikira qanwar maman naki kifada mata sunan mai gidannan kice mata gidan ALHAJI YOUSUF USMAN endai a garinnan take ba wanda bai san gidannan ba.,
da ganan takira masu mata aiki tace Ku kaita daki ku gwada mata toilet tayi wanka tayi sallah ku bata abinci taci.. daga haka ta miqe ta nufe d kinta
mai aykin dayar mai suna zubaida taci mata mutafi ko jikinta ba qwari ta tashi tabi bayansu..
yauko munshiga ukku da wannan jarabawar data samemu
toh yanzu a can kuka barota?
momy tafiya fa matar tace ayi da eta ya zamuyi
momy wllh zee batajin magana kokadan
wai shin meyasa tama mishi hakane? sakinat ta tambaye yusra
abinda zee tafada mata duka tafada musu..
taslima.. momy tayi kafin tace zainab tajanyo mana jan gwan gwama
zaune yake kan dadduma bayan ya gama sallah magarib yana sanyi da wata jallabiya color milk yana jan tasbi...
yayi zurfi cikin tunani sosai akan abunda yafaro dashi jiya
tambayoyi ne fall aranshi akan yarinyar nan tinanin yake erin kalan wuqancin da zai shirya mata yake amma kafin nan zai kira mamyn sa yanzu yanason yiwa yarinyar nan wasu 'yan tambayoyi dan shi dai yasan baya shiga harkar kowa toh meyasa eta dole takeson shiga harkar sa ne har take son tozartashi a edon duniya?
wayarsa y dauka yakira mamyn sa
etace tafara sallama kafin shima y amsa sallamar ta
bayan sun sun gaisa yane
mamy alfarma nakeson keman dan Allah
haba emran wace alfarma ce wannan zaka nema aguna da bazan eyayi maka etaba matuqar inada ekonyi mamy zandawo gida yanzu pls edanuna banajin komy a cikin su bazan eya koma kwana anan ba.
she kawai ne kake nema?
a...a mamy d akwai
toh menene, ne emran?
enason ganin yarinyar da taman wanan abun yanzun nan dana dawo gida naji khaleefa yace tana gidan
hmmm emran kenan kai da baka eya magan sosai taya za'ayi kayi mgn da eta harka mata wadansu tambayoyi nafasan halinka?
mamy nasan yanda zanyi nidai wannan alfarma kawai nake nema...
OK" karka damu nima edan kaji sauqi enada fada dakai sosai..
fada kuma mamy? haba mamy na kada kice hakan mana kokadan banason jin wanan kalmar daga bakinki
toh naji saika qaraso gidan
ywwa mamy na i love u so much
luv u 2 my son
kafin ya katse kiran yakira babban security sa yana ganin kiran ogansa bai dauka ba dan yasan ko ya dauka ba magana zai masa ba sai yiyi saurin budi dakin d aka kwantar da emran koda y shiga yana zaune a bakin gado..
da sallama ya shigo yace ranka ya dade ya jikin bai ce mishi qalaba, ya nuna masa alqu'ani dake kan dadduma sa,,, alama kenan yadauko masa, sanan yatsahi yafita yana tafiyar nan tasa hankali..
saura naganin fitowar sa sukayi saurin esowa suka mara masa baya har gurin motocin su,, saurin bude masa mota sukayi yashiga tamkar bayaso, ya zauna sannan suma, saura suka shiga mota sukaja suka tafi sai gida...
kiran zee ne yashigo wayar momy sai yanzu tasamu natsuwar kunna wayarta tun jiya da abunnan yafaru tasan maman ta tayita kiranta basu sameta ba
saurin dauka momy tayi tace zainab? na'am momy yanzu zainab abinda kinkayi kin kyauta kenan kafin momy ta rufeta da fada akan abinda tayi bai da ce ba, ai wannan rashin hankali ne, yazaki biye ma mutun erin wannan? to yanzu gashi kinsamu a matsala ba muko san inda kike ba, mahaifanki sai nemanki suke awaya wayrki a kashin nan nima haka nayita kiranki bansamu ba, hankali duk ya tashi haba zainab da eliminki da wayonki kina matsayin 'ya mace ace kina erin wanan abun bai dace ba sam....
momy kiyi haquri amma nika dai nasan yanda nakeji akan abunda mutumin nan yaman momy wulaqanci fa ba dadi...
toh naji wulaqanci ba dadi basai ki qyaleshi ba komy yayi miki tinda kowa da erin rayuwar sa, kekuma gashi bakida haquri gaskiya abinda kikayi baki kyauta ba ni abbanki ma nakeji miki, kinfi kowa sanin halinsa.. yanzu sai yaushe zamu ganki kenan?
Hajiyar tace min wai kizo nan gidan tana nemank....
tana me?.......
nashiga ukku ni zulaiha yau ina zansa kaina wllh zainab dai kingama jamana
tafada tana share qwalla yanzu edan naje kinsan abunda za a mana dani har ke?
momy ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru
matar gaskiya naga kamar tanada sauqin hali sosai bakiga yanda take man ba...
wani erin ba abunda zai faru kitozara ta mata yaro kice ba abunda yafaru zan dai zan dai yi shahada, nazo dan ba yanda zanyi enkashe mu ma za'ayi yazanyi tinda kin riga kinja mana...
momy ki dai na fadar wannan maganar dan Allah.. gama hajiyar nan ta aiko kirana..
toh Allah dai ya sauwaqa..
ameen momy suka tsinki wayar atare
keje dakin can ina zuwa! dakin da zubaida ta nuna mata ne ta bude tashiga,
wani haddadin parlour ne da yafe wancan parlour haduwa da girma da komy ma, tabb wanan gida kam baqaramin haduwa yayi ba Allah,, tamkar baza'a mutuba yanda aka tsarashi tamkar gidan turawa datake gani a tv,, ~niko nace su zee karfa afadi gurin kallo~ gaskiya masu kudi najin dadin su, ta furta ahankali kafin tasamu guri, dai daga cikin lumtsatsun kujeron dake cikin parlour ta zauna shiru2 har takusan 30 mnt bataga kowa ba, can taji alamar motsin tafiya kafin amurda qofa ashigo, wanine taga yabude dakin kafin wani daddadan qamshi ya ziyarce hancin ta
emran ne y shigo ahankali cikin takon wani tako na esa, shigar da yayi kam tamasa kayu sosai, kamar a kullum qar masa kyau ake, yasamu guri can nesa da eta ya zauna ko kusa bai ko kalle gurin da take ba
security daya bude masa qofane ya shigo da wasu memos
guda biyu,, da pain
guda biyu ya ajewa emran memo daya da pain daya, a gefe,, etama zee yaje gurinta ya aje akusa da ita tareda cewa, wanan shine zaki rubutawa wa, yalla6ai amsa idan nakawo miki, saqonsa.. ya juya ya koma gurinsa yayi tsayuwar sa tamkar wada baya motsi.....
daukar pain emran yayi yafara rubuta tambayar sa kamar haka............
--------------------------------------
[10:38AM, 1/13/2018] A:
Chapter 15 · 0% Book details