← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 60

Sashe 43

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(84-85)* dik enda hankalin mamy yake edan yayi dubu tohh yatashi, randa take bata ta6a ganin emran erin haka ba, kuma hardai yanda taji muryar sa nafita tamkar ba tasa ba,
uwa, uba kalaman da taji emran na furtawa, enya kuwa yana cikin hankalin kansa lallai babu lafiya, cikin qarfin hali bayan da tagama zancin zucin ta, tamatso kusa dashi kafin ta da fashi haka ta janyoshi a hankali tare da bubuga masa kafada alamr lallashi har takawoshi kan gado ta zaunar dashi...
shiko gogan jinsa yake tamkar ba'a duniyar nan tamu yake ba, jinshi yake ana lulawa dashi gurare da dama zuciyar sa, wani erin zafi take mishi tare da bugawa da qarfi,
kansa qasa gefin sa mamy ta zauna tare da kafeshi da edanu kamar zata gano wani abu 6uyayye a tattare da shi,,
sun kwashe kusan 10 mint a zaune shi bai d'ago kansaba kuma bai koma cewa komy ba, ellah saurarin zuciyar shi kawai yake, etama mamy hankalinta na kanshi tanason ya daidaitu ne kafin tace mishi wani abu,
suna haka sukaji an bude qofa Afra ce da zainab bayanta, sunzo sukawo qarar sa, sai kuma suka taddashi a zaune cikin dakin,,
wani kad'awa ne cikin Afra yayi ba shiri takoma tafita da sauri etama zainab bayan ta tabi zata fita, sai mamy ta tsayar da eta tare da tambayar lafiya shunshigo kuma sunka koma,,
ena baqin harsun tafi? Mamy ta tambaya...
babu shakka kokadan azuciyar ta, zee kai tsaye tace wa mamy ehhh sun tafi amma mamy korarsu akayi gaisawa kawai mukayi...
shine ma mukazo mufada miki,
mamy tace bangane korarsu akayi ba, akan me, waya koresu din,
shiru tayi batace ko qalaba danko kallo bai esheta ba, ganin da mamy tayi zee tayi shiru ne yasa ta tabbatar lallai wannan aykin emran ne, dik abunda akeyi kanshi qasa yana jinsu cikin tsanaki yatashi yafita batare da yace ko qalaba,
da fitar sa bai darje ako ena ba, sai part din Afra yaci sa'a kuwa qofa abude take turawa yayi yashiga tare dasa key a qofa kasan cewar ahankali yashigo bataji lokacin da aka bude qofava saboda taba qofar baya tanacan tana cirar sarqarta data sanya...
dube+2 ya shigayi a dakin ko zaiga wani abu wayar chaza yagani a qasa da hanzari yaje ya dauke ta, yayi gurin ta, kamar daga sama taji saukar duka babu shiri ta juyu wazata gani dodon ta,
ayfa nan bashiri yashiga lafta mata wayar chaza kafin yace a hankali, yana dukan ta,, ke harkin esa kiyi jagora har kujee kukai qarata gurin mamy, dan kawai nakore wasu 'yan eska mutane marar mutunci, sai yanzu nayi nadamar korarsu danasa ankayi dan wllh naso rufesu nasa akayi, badai kece jagaba ba, tohh kuwa lallai yau sai kinci ubanki, qaramar marar kunya kawai, babuji ba gani, sharara mata bulule kawai yake kururuwa take tana neman agaji, kasan cewar akwai 'yar tazara tsakanin part din mamy dana afra yasa ba tasamu agajin gaggawa ba,
mamy ce ketawa zee tambayoyi akan tanason taji yanda akayi aka kore baqin da sukazo can zee ta zabura daga zaune da take, tace mamy wllh kamar fa, naji qara Afra, kafin ta koma magana suka komajin ehunta da qarfi, ay da gudu suka fita, har mamy sukayi enada sukejin qarar kefituwa,,
part dinta suka nufa ayko nan ne take, kuma qofa arufe take, shiga bugun qofa mamy tayi tana fadib Afra! Afrai! da qarfi" tanajin maganar mamy ta qara sakin wata erin qara wayyo mamy yaya emran zai kashe ni, kutaimaka man dan Allah,,
baqaramin tashi hankalin mamy yayi ba, shiga kiran sunan sa mamy tayi, amma enah... kokadan baya jinta, sai da ya lallasa Afra sosai da sosai, sannan ya yarda wayar chaza dake hannun sa, edonsa yakai kan wayoyin su guda ukku dake kan madubi, ta Afra biyu ta zee daya, ya kwashesu duka, kafin yace enga dan eskan dazaku koma kira ko yakira ku, kuma wllh bari kiji, kika kuskura nakoma ganin ki da waya saina kusan rabaki da numfashi, daga haka yayi hanyar fita,
saura kadan ya bangaje ta sai da taja baya da sauri, etakam mamy tsoro ne, matuqa yakamata, lallai babu tantama aljannu sun shiga emran, kafin suyi cikin daki,da Hanzari, koda suka shiga Afra na kwance, ko dan yatsanta bata eya dagawa tsabar azaba,,
da gudu zee tafita takirawo driver akai Afra hospital takusan fita part dinsu kenan taji an janyo hannuta da qarfi tafad'a kan....
[6:24PM, 1/27/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 43 · 0% Book details