← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 60

Sashe 47

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
, * **I
, * * *
*(92-93)* salatin da mutanin gurin keta rafkawa shi yafito dasu raliya daga cikin dakin dasuke a zaune suna jimami, wakuwa zasu gani zee ce atsaye ta canja tayi matuqar kyau ta qara haske amma haryanzu edan ka kalleta zakaga rama atattare da eta,
Ya mas'ud ne yayi qarfin halin kiran sunan ta cike da mamakin sa daya kasa 6oyuwa zee najin yayanta yakira sunan ta cikin kuka tafa cikin jikinsa tare da sakin wani erin kuka mai matuqar ciyo,
shima rungumeta yayi yana dan bubugar bayanta alamar rarrashi, suna hakan kuwa sai ga mamy da Afra sunshigo nan mamaki yaqara kamasu mama mekuma ya hada zee dasu hajiya dan da alama atare sukazo,,
baba kuwa kallo yabar kansa shima abun rudar sa yayi kwatsam yau ga zainab tadawo gaban su addu'ar su ta kar6u
nan fa akashiga gaggaisawa tare da suwa mamy sannu da zuwa kafin amusu jagora har cikin daki dumin su huta sannan ashiga tattaunawa
Zee kam anga su raliya ga kuma hafsat taubashiyar ta dasuka dadi basu haduba jinta takiyi yau cikin farin cikin dabata ta6a tsintar kanta acikin ba, gaba daya ta manata dawani kuncin data shiga abaya,
etama Afra ganin sisi ta nacikin farin ciki haka yasa dik taneme ciyonta tarasa nan danan wata shaquwa taqara shiga atsakanin su edan kagansu yanda suka hadu suna shewa da dariya kamar basu bane adazu suke zaune jugum+2 Allah kenan ba yanda bayayi gashi yanzu duk wani qunci dake cikin xuciyar su yawanke tas" kamar ba'ayi ba,
nan fa hafsat tashiga zolayar zee wai ta dauka tini anyake mata kai shiyasa ma tazo cin zazzafa ayfa nan maida martani yatashi
zee ce tace wai ena khaleed ne?
teema ce tace yana sukul yanzunan zaki eya ganin sa
gaskiya kam enason nagansa nema kodan naga wannan khaleed din da sisi keta faman bani labarin sa, Afra tafada tana kallon zee tare da murmushi dauke a fuskar ta,
suna hakan sai ga yaya mas'ud yadawo daga dauko khaleed daga scol har cikin dakin yashigo dashi amma baifada mishi zee tadawo ba dan yasan kakka6i erinna khaleed
ay khaleed naganin zee yafada kanta harda dan kukansa gwanin tausayi aunty kawai yake kira kamar wanda ake koyawa fadar sunan, etama rungumeshi tayi tana cewa khaleed tashi kaga aunty Afra danake baka labarin wacce nacema tabada chocolate ranan danayi tafiya tace akawoma...
Ay da saure yatashi yana cewa aunty na ena take zee nune tamasa da Afra dake agefen sakeena sai murmushi take masa tashi yayi yaje har gurinat cikin jikinta yashige tamkar yasanta dukansu dariya sukayi har yaya masu'd dake atsaye saida yadan murmusa kafin yasakai yafita,
Gefen su emran kuwa wani Hotel dinsa nakansa dake garin zariya suka sauka banda daddy da yasauka gidan sarkin zariya,
dan suna sauke su mamy suka wuce kafin sufuta suzo ayi magana,,
wani haddadin daki ne suke ciki tamkar ba aqsar ba tsabar tsaruwar dayayi kwance yake kan dogowar kujera da tayi kyau harta gaji ya daura hannusa a bayan qeyar kansa edonsa alumshe qasim kuwa yashiga gurin wanka Allah kadai yasan tunanin da yake,
har qasim yafito yashirya edonsa alumshi kuma duk abinda qasim keye yana jinsa zuciyar sa kadai yake saurare,
tsaf" qasim yakare masa kallo tare da ta6e bakin shi kafin yace guy wannan fa tunane+2 da kake bazai fishsheka ba kawai ka dainashi kada kawa kanka illah,
tinda abinda kecin ranka shine mukazo domin muyi qoqarin samarmaka dashi,,
qin kulashi yayi da dukkan alama miskilancin yau yafi na kullum,
haka da qasim yaganine yasa ya qyleshi bai koma cewa komy ba ellah cemishi da yayi zai dan fita yadawo amma ya daure yaci abinci daga haka yasakai yafiatawar shi,
Afra kadaice a tsakar gida tana alwala su zee dikansu suna daki sun tada sallah harsu mamy dukansu masallaci suke biya Afr kadaice tamakara sakamakon bacci datayi saida suka tadata,
mas'ud ne yayi sallama yashigo dauke da daduma alamar daga masallaci yadawo, amsa masa sallama afra tayi tare da mishi sannu da zuwa,
har cikin kansa yaji saukar muryar ta, tashigeshi ywwwa yace atakaice yawuce dakinsa bin bayanshi tayi da kallo aranta tace kai wannan shima erin yaya emran ne baya kula mutun ammafa gara kowa da yaya emran tafada afili a hankali tinawa tayi da dukan daya mata edonta tayi saurin rinteswa aranta tace gaskiya yaya emran mugune na gaske tabb wllh ranar nadaku, muryar sa data tsinkayo ne yakatsar mata da tunain da take, cemata yayi ke bazakije kiyi sallah bane sai lokaci ya wuce kuma daga haka yasakai yafita warshi
ekon Allah Afra takoma cewa lallai wannan shima baida sauqi ammafa gaskiya yamugun haduwa duk da shan murr" dinsa bai 6oye kyansa ba tafada tana nufar qofar dakin su,
A hankali na leqa kaina cikin parlour gidan su zee ganin takalme birjik a qofar dakin bakamar wasu dana tsinkayo ko ba'a fada ba sunji kuddi daga gani,
kai tsaye nima nashiga dannagane shin suwane aciki kuma me ake tattaunawa, tozali nayi, da dake zaune kan kujira sai baban zee, *Mamy*, *ZEE EMRAN* *QASIM* *AFRA MAMA*
duk wani bayanin 6acewr zee kamar yanda mamy tafadawa daddy anfada musu eta kanta zee tamusu bayanin tin daga lokacin da'a dauke ta har ezuwa kan wuyar da tasha amma bata nuna dan mamy bane,
Ana cikin haka wayar emran ta fara ringing kallon sa daddy yayi tare da cemishi yakashe wayarshi dan magana zasuyi mai muhummanci,,
gyaran murya daddy yayi tare da cewa baban su zee naji labarin zainab gobe zaka daura mata aure ko?
tadda kanta tayi da qarfi babu enda edonta ya sauka sai akan emran arnata tace aure kuma? wazai aurene? dawanene baban ta zai daura mata aure tabbas kasheta akesonyi bayan ga wanda takeson cika burinta akansa, a kullum addu'ar ta daya ce akansa....
[8:04PM, 2/7/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 47 · 0% Book details