← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 60

Sashe 52

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(100-101)* zaune yake akan kujera kusada mamy yana cin abinci dik da yanajin yunwa kuma yanason abincin hakan baihanashi yin cinsa yanda yaga dama ba,
tsaf mamy ke kallon sa tana qara jinjinawa lamarin emran mutunne mai wuyar sha'ani komy nasa tamkar d'an jinin sarauta yake yinsa yoko affan bai wannan qasaitar tunanin take yanda emran zai tafiyar da gidan sa bayan sanin halinsa da tayi emran komy nasa da ban yake dana kowa mamy ta zufafa cikin karatu wasiqar jaki sam bataji abinda emran yakecewa ba, sai da tasake cewa me kace?
tamkar bayaso haka yakoma bud'e bakinsa yace mamy cewa nayi amma eta wacce za'a kawo anan zata zauna tare da ke ko,?
sakake mamy ke kallon sa kafin tace wai kuwa anya emran kanka d'aya kuwa ena kata6a ganin anyi haka tazauna nan taman me kone ke auren ta, kaga wllh kamaida hankalin ka banason shashanci yakake magana tamkar wani qaramin yaro ko ena wasa da kaine Allah emran edan baka kiyayeni ba zan mugun sa6a maka sosai mamy tarufe edo ta dinga yiwa emran fad'a babu k'ak'autawa.
sam bai aza maganr da yayi abin zai zama haka ba, ashe ruwane ya jawa kansa da qyar yasamu tayi shiru yanata bata hanquri shi bai aza zataji zafin maganr sa haka ba
saida yaga tafuce sosai kafin yayi shirin miqewa ganin haka da tayi yasa tace ya koma ya zauna ba musu kuwa yakoma ya zauna yana addu'ar Allah kuma kasa ba wani abu bane katse mishi tunani mamy tayi da cewa yakamata emran yadace ace ka saukar da komy da kakeji kakar6i auren nan kodan farin ciki na kaifa ba yaro bane ba, baka ganin sa'annin ka dikansu da auren su wasu ma harda 'ya'ya toh muddin kanason mushirya ka janye komy ka shiga ayi komy dakai matuqar nice mahaifiyar ka ena baka umarnin yin hakan kuma a gidan ka dakake gini zaku zauna naji ma qasim yace an kammala komy na gidan toh Dan haka banason jin komy tashi ka esko qasim edan yadawo daga kai matar sa dan yau nan tawunan min yace da ya kaita zaidawo.
dole badan yaso ba a baiqara cewa komy ba jiki dik a sanyaye yatashi yanufe part d'insa shi a gaskiya duk antakura sa haka ya esa 'ban garinsa sai faman cika yake tamkar zaya fashi ```{ dole dai ko bakaso sai anyi mai kai kamar na
lolz..
}```
abubuwa sun kankama gaba d'aya damuwa nason rufe zee ganin da tayi lallai dai kuwa auren nan za'ayi babu fashi wllh gaba d'aya jitake tamkar afasa auren nan eta batasan amfanin wannan naci na auren nan ba, wllh da tanada eko wannan abun sam baza'ayishi ba, amma ba yanda zatayi
masu gyara jiki musamman mamy ta turo 'yan qasarsu edan baku manta ba mamy shuwa ce shiyasa ta daukosu dan ayiwa 'yarta gyara na musamman sosai su mama sukaji dad'in wannan karamci na mamy sai fatan alkhari suke mata shiyasa su anasu 6angarin kokad'an basuga matsala na wannan auren ba dan sunsan kan zee zatasamu kulawa tamkar a gidansu tunda ba yau bane tafara zama tare dasu ba gwargwado sun d'an san halin juna su.
gobe ta kamane za'a sanya zainab a lalle gaba d'aya abubuwa suntaru sunwa su raliya yawa sai faman kai da kawowa suke basu nan basu can, motar sakeenat kuwa taji jiki sosai, saboda yawan zirga-zirga da suke ta siyayya da kuma aykinsu dasu mama suketa famanyi.
'Yan Abuja sun qarso sakeenat ce da teema sai hafsat sukaje dauko su, Afra da aysaha daga airport saboda sunqi yarda su zauna acan sunfison suzo nan komy ayi dasu enda zasu dinga shewa da halaqo" da esarsu gida kuwa sai kunga yanda zee takejin dad'i saboda yanda dik tabi ta rungume su Afrah da aysha tamkar zata mai dasu cikin cikin ta" tsabar dad'in da duk taji yagama cikata har yazan taji 'yar damuwar ta dake damun ta tad'an ragu sosai ba erin yanda takeji ba
yauce ranar da aka sanya Amarya Zainab a lalle dik da ba yau bane za'a kaita tayi kuka sosai saboda yanda wannan ranar tazo mata kwatsam batare da son ranta ba sosai tayi kuka tana ganin yau kwanaki kad'an suka rage tarabuda mamanta da yayanta da d'an k'anin ta khaleed da duk wannan shirye+2 da ake yana fama da d'an zazza'bi amma haka ya daure yake d'an shiga mutane
shiri na musamman k'asim keye tamkar shine angon su Affan kuwa dasu sadik da salman duka antare part d'in emran sai buga lissafin su suke sukad'ai shi kurman Ango yana gefe tamkar ma baya cikin d'akin shi duk abin duniya ya damesa bama kamar yanda yaji ance yanzu da yayi aure bai k'ara kwana gidannan hakan na nufin ana neman rabashi da mamyn sa kenan?
kafad'arsa da Affan ya dafa shi ya dawo dashi daga tunanin da yake yace haba maza ya kayi zaune haka ka zurfafa acikin tunani duk ga damuwa nan 'baro+2 a fuskar ka tamkar mace yauko amaryar ka bana jin tana cikin damuwa erin haka mata mako da kowa yafi sani da raki edan ana batun auren su dan Allah ka waske ka dawo normal mana plss
fad'a masa dai guy ninarasa wannan hali na Handsome d'innan shiyasa ma ninayi shiru koda naga yanayin sa saboda magana ma zaka masa yafita eskar ka tamkar kanayi da dutse abun haushi shiyasa na futar da yawuna nasa mishi wannan.
jin da yaye suna neman fasar mishi da kai da yakejin yana mugun masa ciyo yasa batare da yakulasu ba yayi cikin bedroom d'insa dan yasamu sa'eda
wata dariyar haushe ce qasim yayi kafin yacewa Affan wacan dakeke ganin sa yawuce dik yanda kake tunani wllh gara kufitar eskarsa muci gaba da abinda ke gabanmu kaga daddy mamy dani kaina ba erin ban baki had'i da lallashi da bamuwa bawun Allah nan ba but da yake baud'ad'in mutun ne shi duk bai d'auka ba addu'a ce kawai zata taimaka gurin daidaituwar wannan guy d'in dukansu sun gamsu da maganar qasim dan ba wanda baisan halin sa ba.
zancin emran suka aje gefe sukaci gaba da shirye+2 abinda ke gabansu mussaman dinner dasuke son ta tsaru sosai dansu enda ma daddy nabari dik wani abunda zasuyi awaje zasu yishi saboda kasancewar su manyan yara.
******************
Yau ne akayi walima yayinda aka tara manyan malamai suka suburbud'a wa Amarya nasiha da jan kunne tare da nuna mata muhimmancin sunnar ma'aiki (s.a.w) tare da hak'k'ok'in aure da sharud'an sa, had'i da dad'in sa da kuma akasin haka Haquri shine maganin duk wani abu na rayuwa nussaman Aure zo mu zauna zo musa6a duk wanda yazo wannan walima ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba da erin nasihohin malaman nan Zainab tasha kuka harta gode Allah ganin take tamkar farin cikin tane yazo qarshe _(Niko nace kokad'an ba haka bane Zainab ay aure yafi gaban nan)_ haka akatashi walima tare da yiwa kowa sha tara ta arziki gwargwado wasu da sunkayi sa'a cikin jakarsu sun same turmin atamfa wacce za'asa ran kamu gobe wasu kuma ta wunin biki suka samu taro walima dai ya watse lafiya yayinda Kowa ya kama gabansa,
~^^^^^^^________^^^^^^~
Ko ran kamu ma hidimar da akayi ba 'yar kad'an bace Amarya tayi kyau matuqa hartaso tafara sa mutane ko kwanto suna tantama wai ko anya etace?
Masu kid'ane aka dauko qwararre suka baje kolinsu ansa rawa su sakeenat gaba d'ayansu qawayin Amarya hardasu mommy sun taka lokacin da sukazo yiwa Amarya liqi amma banda mama dan eta bata zo ba.
Afra kuwa sai da aka fiddata daga fagin rawa haka ma ran kamu komy anyi lafiya aka koma gida sai ciyon jiki yawa su raliya sallama bama kamar Afra saida aka mata gashi tsabar yanda takejin jiki zee kuwa sai faman dariya take musu har saida taji cikinta yafara ciyo, yau dai haka kowa yayi bacci cikin ciyon jiki daga masu aykin abinci zuwa wa'anda sukayi rawa *[ bama kamarsu besty na hannu tamkar zaya cire sabida tsabar d'ibar shoky
*_Ranar muke jira yau gashi tazo_*
*_Nima sa'adat tambura
dole na d'auko na bugawa ango shida Amarya
, * **, *
*sannan kuma I
u masoyana
, * * *
_*YAUFA
*RANA BATA K'ARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA...
~_______=======_______~
Da milasalin qarfe 8:am zaune yake a bakin gadon sa kansa na kallon k'asa ya wad'e kai da hannuwan sa nanata wannan kalma kadai yake a zuciyar sa, ni imran yau nene za'a d'aurawa Aure" gaba d'aya yau jinsa yake tamkar a mafarki yake jin yayi an bud'e qofa anshigo tare da yin sallama mamy ce tare da qasim yaje kai qarar emran gurin mamy saboda yayi-yayi ya tashi yasa kayansa dan jirginsu 9:am zai tashi kuma 3:00pm akasa 'Daurin auren amma yayi banza dashi ga tym na tafiya shi yasa ya yanke shawarar zuwa dan ya gayawa mamy.
a hankali ta dafa kafad'arshi tare da kiran sunan sa, kansa yad'ago duk edanun sa sunyi wani eri ga dukkan Alama bacci ne taff a edonsa yasawa ransa abin shiyasa ko bacce baya samu sosai gaba'daya mamy har fad'awa taga emran yayi ga wani haske daya qara tamkar wanda bayada jini saboda rashin cin abinci.
dik da mamy etama tana cikin wani yanayi dan matuqa yabata tausayi sannan kuma ko etama ga kewarsa da zatayi ba yanda zatayi haka ta lalla6ashi da itada qasim yasa tufafin sa.
Wani rantsatsen yadi ne wanda kyansa da kud'insa ba'a magana satin nan qasim yayo order kayan da zasuyi amfani dasu a qasar *Dubai* daga kan Hula zuwa
had'e da Turarin da zasuyi Amfani dashi dika acan aka siyo.
dikansu sunyi kam tubarkallah masha Allah mamy sai tasbihi take kafin tace 'yar uwarku takirani cewa da Hajara taso matuqa tazo bikin nan Amma wane abu ya gifta sai dai After Aure wani d'an sirirn tsakene yafitowa emran wanda baisan fitowar sa ba murmushi mamy tayi kafin tace nasan Arina dan tace tayita kiranka kaqi d'auka shi kuma qasim tace duk takira busy takeji tohh nace mata shidai qasim ta masa uzuri amma kai nasan bakada wani uzuri ganin da qasim yayi 9 saura 20 yacewa mamy zasu tafi addu'ar dawowa lafya tamusu tare da tambayar su Anan Abuja za'a dinner kenan?
qasim kad'ai yabata Amsa da ehhh shi gogan bakinsa ma yakasa motsawa.
Unguwar su zee ta cika manqil da Al'umma kai kace ranar Idi ne ba masks tsinke makad'a da mawaqa duk sun hallara zuwa *Daurin Auren Zainab da Imran*
[2:03PM, 2/17/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 52 · 0% Book details