← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 60

Sashe 21

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*_Haqiqa ba abuda zancewa Allah (s.w.a) sai godiya Allah nagode maka, tabbas masoya nada matuqar dadi arayuwa, Allah kabarmu da masoyan mu na kwarai, Allah ka nisantamu da maqiyan mu duniya da lahira, ina godiya agareku masoyana da masuyimin, fatan alkhairi arayuwata, damasu man addu'a, dika ina godiya, wa'anda bansamu duba texts dinsu bare namusu reply kumun agufuwa, saqonni sumin yawa, kuyi haquri edan nasamu sarari zanduba, Allah ya barmu a tare har mutuwa ameen,_*
*(46-47)*...wayar sa ce keta faman, ringing amma ko kadan bai kulata ba, danna laptop dinshi kawai yake, mai kiran kuma yaqi ya dai na kira, kirane bayan kira sai da yaga dama dan kansa, sanan ya dauke wayar tareda dan ya mutsa fuskar sa, saka makon ganin, mai kiran, sis sadiya yagani kan screen din wayar sa mamaki ne fall aranshi dan shi dai yasan babu number wata 'yar mace a cikin wayar sa, edan bata mamyn sa ba, shi ko number Afrah ma baya da eta,``` ( bai san wannan aykin Affan bane)```
kin dauka yayi qarshe ma yasa number a blacklist tare da goge number ga baki daya cikin wayar, tareda sakin wani siririn tsake..
tabbas yasan wannan aykin ba wanda zai yishi sai affan, dan yayi ta cusa mishi ra'ayi akan ya kula qanwar sa yaqi shine ya biyo ta wannan hanyar, shine dan wulaqanci har zai daukar wayar sa, ya mishi seve din nmbr wata can kucaka,
kashe wayoyin sa yayi gaba daya, dan baya son damuwa, yana son yayi sammako gobe edan Allah ya kai masa ransa dan suyi saurin tafiya zuwa, airport, zayje qasar Dubai, domin gudanar da wani dan kasuwanci da ya taso masa, amma bazai wuce 2days ba, zai dawo dan Abbanshi ya kusan dawowa,
siyayyace sukayo bata wasa ba, ba abunda Afra bata siyowa wa zee ba, bayan sunkai dinke ne, daga can suka wuce gurin saloon gurin gyaran jiki,
kanta aka fara gyarawa, zo kaga suman zee gashi ne, ke gareta bana wasa ba, sakin baki Afra tayi tana kallon ikon Allah,
dik wani gyara daya dace awa zee anmata, tin daga gyaran gashi, gyaran fuska, zuwan gyaran jiki, da wankin qafafu ammata, tubarkallah masha Allah
tabbas hausawa sunyi gskiya da sukace edan kanada kyau ma toh ka qara da wanka, ba qaramin kyau zee taqara ba,
wannan wllh zuwa kwana biyu, nasan dole afara mana go solo a bakin get Afra kefadar haka cikin zuciyar ta,
gaskiya zainab kinda kyau tinda nake arayuwa ta, yaya emran ne mutun na farko da nake ganin banta6a ganin mai kyau afili ba, kamar sa, toh wllh kece ta biyun sa,
murmushin da ke dauke a fuskar zee ne da take lokacin da Afra tafara magnar ta, ya dauke dif a fuskar ta, sakamakon maganar emran da tasako azanci ta, bama kamar enda tace wai etace ta biyun sa, ko kadan bataji dadi ba, data kwatanta ta, da shi,
lpy naji kinyi shiru sis?
maganr Afra ce tadawo da eta, daga tunani da take, tareda danyin murmushin da bai kai ciki ba, tace wllh ba komy, kawai ina tinanin mamy ne, erin wannan son da take man wannan erin hidima da gata haka?
hannayin ta, guda biyu Afra, tariqa, kafun tace, a gaskiya, ba abunda zancewa mamy tsakani na da eta sai dai, Addu'a Allah yasaka mata, da gidan Aljannah ma d'aukakiya, allah yasa tagama da duniya lafiya, kuma ena roqon dik ranar dana cuce mamy azamana da eta, Allah kamun hukunci dai2 da abunda nayi mata,
murmushi Afra tayi kafin tace dan Allah sis kidai na erin wannan maganr, ay ke bakimaye kama da masu cutar da mutane ba, kedai kawai Allah ya bamu haqurin zama da juna, sannan ina roqonki da abu daya dan Allah dik abunda ke damunki kada ki ta6a 6oye min kiyi gaggawar sanar dani, inason ki dauke ni tamkar ciki daya, muka fito ni da ke, ki dauke ni tamkar 'yar uwarki, kamar yanda na daukeke, muyi niya mutafi gida ko? kada mamy tajimu shiru,
zee rungume Afra tayi tana cewa sis nagode sosai kuma insha Allah namiki Alqawarin ba abunda zan 6oye miki, na ga medani, kema kinka dauke ni tamkar 'yar uwa balantana ma ni,
ay karkiji komy, kuma inason edan muka koma gida akwai maganr dana ke sonyi da mamy,
wace magan ce kenan?
tabb ay bazakiji ba, sai randa zan sanar da mamyna,
au abun haka mane?
tohm ay dai zanji edan har zaki sanar da mamynki ko?
dariya sukayi gaba daya tareda qara hugging din junan su, har suka esa gorin motar su arigangan shiga mota sukayi,
zee tariga shiga, tanawa Afra dariya, cikin wasa Afra tace ai zan rama, kafun driver ya jasu sutafi,
koda suka eso gida ma, arigangan fitowa sukayi cikin mota, suka nufe ciki gida, driver shima abunma dariya ya bashi, sosai suka burge shi, kafun ya fito ya rurufe morfin mota da suka bari abude,
Mamy na zaune cikin parlour tana kallon, sunnah tv, taji shigowar su aguje, kafun ta ankara suka fado mata ajiki, dan tsorata ta, sukayi, kafin tace lpy kuke kuwa?
cikin 'yar shisheka Afra tace Allah yanxu kam narigaki,
bawani ninarigaki tana Allah zee namata
sai yanzu mamy ta fahimce mafarin gudun nasu, har suka fado mata haka, daman dan wannan kuka tsoratani kamar wasu yara,
toh ay yarane mu agunki mamy, suka fada a tare,
murmushi tayi kafun tace toh naji ina siyayyar da kukay...
bata eda maganar ta ba, driver yashigo niqe2 da kaya sauran securitys ma, su 2 dauke suka da kayyayakin, suka aje a tsakiyar parlour tareda gaida mamy kafun su fita...
kallon su tayi kafun tace tuni kudagani kutashi ku shiga da kayan ciki, enjin ankai d'unkunan ko?
Ehhh mamy Afra tace, munkai yace nan da kwana 2 mu koma mu kar6o,
toh ba damuwa,
tohm ay saiki fadi maganr da kikace zakiwa mamy afra tafada tana kallon zee data lafe a kafadar mamy,
ywwa gara da kinka tina man my sisi, uhum-mamy?
na'am ya ankayi ne zainab...
daman wata Alfarma nake nema agunki dan allah..
tohm ina jinki fadaman,,
daman nace dan Allah inason masu miki girkinnan, ki dakatar da su, suringa yin nagida baki daya kawai, ni zanriga muku da keda daddy, da kuma gyaran dakinki dika ni zanyi, dan Allah mamy karkice a..a
kallon fuskarta mamy taqarayi sai yanzu taga erin gyaran da akawa zainab, sasai taga tadawo mata tamkar wata, kamr ba zainab din data saniba, kafin tace, toh babbar magana, zainab kenan dik wannan roqon haka,? toh" ay shikenan zan miki yanda kikeso, kuma daman wannan yana da kyau saboda gidan wani zakuje, karku tafi baku eya komy ba, yanada kyau kukuye ayki, musamman ma, wannan tana nuna Afra, danke nasan garake ma, maybe kinayi a gida,
hakane mamy nike abinci wataran,
ohk tohm shikenan kinga da ganan kidan ringa koyawa wannan sakakar,
kai mamy
agaban ta zakice man haka, salon kisa wannan ta rainani
baki mamy ta riqe, tace toh dadi uwar son girma, edan dai ke baki girmeta ba, toh ko eta ta girmeki..
mamy nama girmeta zee tafada cike da tsokana
gurin zee ta nufa zata kamota, zee naganin haka, tayi saurin tashi ta haye sama, etama ta bita, mamy na kiransu kai ko jinta basuyi ba, qarshin ta dai, masu aykinta takira tacesu shigar musu da kayan a can dakin su
qarfe 8:09 am, jirgin su emran ya daga zuwa qasar Dubai,
wai, mamy wllh naji sakat, da yaya emran yatafi, amma ace mutun ko dogon motsi bayayi, shi kunnawan sa bansan ko wadanne eri bane, daga yace ancika mishi kunne da surutu say yace ancika mashi kunne da hayaniya, ni narasa gane erin kalan yaya wallh, wai mamy baki matsa masa yayi aure ne, ni ya tafi na futa da wata takura,
toh" zan fada masa dik saqon da kika fada a yanzu nabasa, daga nan sai yabaki dika amsoshin maganganu n ki,
Chapter 21 · 0% Book details