← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 60

Sashe 55

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(106-107)* gaba daya gurin dinner nan ya wani hargitse sakamakom leqin da a keyiwa Ango da Amarya, danni abun ma har tsoro yaso yafara bani erin yanda naga ake watse da naira abin ma ba'a cewa komy" dan qasim da sauran fans. na emran dollars ne na hango a Hannusu na America suke ta faman watse dasu sam ko ajikin su.
mamy kuwa na 1000k, kawai take ta yarfarwa, haka qawayin ta daga na 500, sai na 1000,) mawaqa kuwa gaba daya hankalin su yagama tashi saboda sunga naira nata faman zuba babu sauqi kokadan, haka 'yan matan da sukazo gurin domin kawai emran suma sunnuna tasu bajintar sosai, suma kansu su raliya ba'a barsu a baya ba" dan liqin 'yan 200, sukayi wa'anda koshi Afra ce ta rarraba musu eta kuma Afra ta dinga na (1000,&500) kai gaskiya kam 'yan zuba naira dan tayi kuka kam, su wa'anda akewa liqin ma sai faman hararar juna su, suke k'asa+2 guri kam yayi kyau ba qarya haka mutanin dake gurin suma sun qara haska gurin, sai faman kwasar shoky ake
da daukar selfie,
babu zato ko tsammani su Emran sukaji ana musu ruwan kuddi, dago kansu sukayi dukansu khaleefa edonsu yayi tozali dasu yana musu liqi yana murmushi, cikin sanyin murya yacewa Emran, *Happy Marriage Life* *_my sweet brother_*
ciki+2 Emran yace *tnx* tare da dauke kansa, Khaleefah na gama musu lik'i yafita daga gurin ko gefen da zee take bai dubaba" Emran kamar jira yake shima yafita daga gurin yakoma gurin da aka tanadar musu na musamman ya zauna, dan daman mamy ce ta takurashi akan saiya fito.
Ay kamar jira ake ya zauna aka dinga daukarshi pics" wasu ma da sace suke komawa bayanasa adauke su photo batare da yasaniba, saboda kowa ya gansa ba Alamar wasa ko fara'a, babu atattare da fuskarsa.
shagale kam anshashi ranar bana wasa ba, ba yanda ba'ayi Emran yataso a yanka cake
ba" Amma yaqi lallashin duniyar nan mamy tamasa tare da qasim akan yazo a yanka cake dinnan amma yakafe yace sai dai mamy tayi hanquri wllh shi a gaskiya bazai eya ba, haka badan sunji dadi ba musamman mamy suka qyalesa, zee kuwa tana daga gefinsu tanaji duk yanda sukayi da shi Amma bata nuna tama jisuba, kallon daya wannan Emran baiwa Zainab shi ba, dan da dukkan Alama miskilancin nasa a yau qarshe yake,
*11:12pm,*
su mamy ne dasu gwago ne nagansu a harabar Hall din gurin, sunraka Amarya da Ango gurin motarsu dan tafiya gida, ko bayan da suka shiga cikin mota nasiha ce naga mamy taci gaba da musu erin mai ratsa zuciyar nan.
koda wasa su teema basuyi gigin maganar raka Amaryar su gidan taba, bare ma suyi maganar sayin baki" dan basuko ga alamun dama a fusakar angon su ba, dan eta Afra ma" cewa tayi ko zasu tafi eta gaskiya bazata jeba, dan tana matuqar son lafiyar ta.
Haka sunaji suna gani sukawa zee sallama akan zasuzo mata sallama da zaran zasu tafi, ko kulasu batayi ba" dan sun matuqar bata haushi na rashin rakiyar ta da basuyi ba, sai da sukaga tashin su sannan kowa yafara haramar zuwa gida, qasim ne kawai sai sadik sukaje raka Amaraya da Ango gidansu.
***********
Wani Erin tamfatsatsin Gida ne naga su qasim sunyi parking, kafin naga an bude wani tangamemen get, tabbb wannan karon kam ya canza SALO dan Soldiers ne ke gadin gidan sa, gaba daya lissafi na yagama daukewa sakamakon tohzali danayi da wannan gida nagani na fada,
_*Na Multi- billionaire,Emran Yusuf Usman,*_ a gaskiya fans bazam iya tsayawa na 6ata muku lokaci na 6atawa kainaba gurin fadamuku erin tsaruwan gidan nan ba, sai dai wannan karon bari na daukar muku picture nashi" na wajen gida kugani
wannan shine, kudai kubiyoni kawai mu antaya cikin gidan gadan-gadan dan muga wainar da ake toyawa.
Gaba daya su qasim basu tsaya erin wasar nan ta Abokanan Ango da ake ba, saboda gudun kada suyi wata magana su 6allo da ruwa shi yasa kayan da sukayo siyayya kawai suka aje suka musu sallama da fatar zaman lafiya mai dorewa suka fece.
shiru dakin yayi bakajin qarar komy saina Ac sai kuma na tsuntsayin dake cikin garden, sun shafe kusan 15 mint cikin parlour ba wanda yayi wani qwaqwaran motsi, sai da yagama duk abinda yake da wayoyin sa sannan ya miqe a hankali ba tare da yakula da gefin da take ba ya haye sama ga dukkan Alama nanne dakin sa jin alamar tafiya yasa zee sauke mayafin dake kanta tare da etama miqewa tsaye ta nufe wani daki dake nan gefen parlour, dik da bakowa aciki bai hanata addu'a da sallama kafin tashiga ba, batasan lokacin da bakinta ya furta woww.... ba, haqiqa tsaruwar dakin ya matuqar birgeta ga wani sanyi da taji yana ratsata ga qamshi na fita tako ena, closet din dake cikin dakin ta bude a hankali kayanta ne taga aciki ashirye kowani an ajiyeshi a muhallin daya dace gaskiya abun ya burgeta matuqa, kayan dake jikinta masu nauyi tashiga cirewa tare da daukar wani madaidaicin towel ta daura tanufe cikin toilet, ruwa ta sakarwa kanta tare da darzar fuskarta da akyita dada6a mata abu, fes" tayi wankanta tafito tare da shafa mai da turare, ta ninke kayan data cere tasasu agefe ta dauko wata sleeping dress gown mai matuq
r kyau da tsada,
ta sanya sanna ta dauko wani hijab fari ta sanya tafito parlour dan yunwa take matuqar ji dubi+2 tashigayi cikin parlour ko zataga enda qofar kichin take, can ta hangota a tsakiya bata jira komy ba tasakai ciki, nan ma saida ta 6ata lokacin ta tana kallon komy yanda aka tsarashi kamar a films na turawa komy tsaren gidan nan eta haka take ganin sa, _niko nace dole kam kigansa haka tunda daman susuaka yi gidan baki daya dole tsarin gidan yazamo erin tsarin gudajin su,_
plate
ta dauko sai pork, tafito" fitowar ta tayi dai+2 da saukowar sa, shima ya canza kaya wannan karon jallabiya ce ruwan toka mai walqiya ce yake sanye da eta, tako yake a hankali lokacin da yake saukowa qasa kamar wanda bayason tafiya, wannan edo hudu sukayi da juna dan qofar kicin na kallon step din da zaka hau ya kaika dakinsa, kafin zee tafara dauke edonta daga garesa tanufe gurin da taga su qasim sun ajiye lidojin da suka shigo dasu, wayam tagani ba komy" ashe tana shegewa cikin daki shi kuma daman bai tafi ba sai yakoma saukowa ya dauke kayan yanufe dakin sa dasu, dan yasan dole tafito neman abinda zataci, shi yasa yafito domin yaga yazatayi.
sarai tasan shi yadauke ledojin nan kuma dukda taji kunyar abinda da yamata amma ta daure, hmmm lallai eta kuma yau sai tagani,
sosai yaji dadin hakan da yamata dan yasan taji kunya amma sam sai yaqi nunawa, ganin yayi tana nufu enda yake batare da tace mishi komy ba ta ratsa ta gefen sa, tare da hawa step tanufe dakinsa,
tsantsar mamaki ya hanashi magana bin bayanta yayi shima dan yaga yarinyar nan da gaske take eyakarsa zata nun masa, kuma bazai ta6a yuwa ba..
kafin ya esa harta shige cikin dakin ta maida qofa tasa key, murdawa yayi yajita gam wani haushine yazo masa arai dan wllh yamatuqar jin ciyon hakan data masa. dole badon yaso ba dan bazai eya cigaba da tsayuwa abakin qofa ba, dole yakoma parlour ya neme guri ya zauna.
zee kam cikinta tacika taci tasha sai da ta qoshi, har sai da taji kazar ta esheta, sannan tasha lemo sosai tabar ragowa sauranan gurinda ta gansa, tare da bud'e daki tafitowar ta, etama kamarshi a hankali ta ta ringa saukowa, tana lura dashe a hakimce kan kujera banza tayi dashi" tare da wuce sa tanufe d'akin ta domin ta huta,
ta murda qofa kenan zata shigewar ta cikin daki taji yace cikin wata 6oyayyar muryar sa, dan shi kansa baiso ya mata magana ba amma yaga alamar kan yarinyar nan edan bai tasar mata a tsaye ba" bazai daina rawar da yake ba, dan haka shirunsa zai matuqar cutar dashi gurin koya mata hankali.
Ke" yakira ta dashi cak" taja ta tsaya kafin ta juyo funsakarta tafara waige+2 a cikin parlour, can dai tata6i bakin ta kafin tace cikin wata murya tafara maganar erinta rainin hankalin nan tace, Ke" kuma? tafada sannu a hankali na erin kamar tana mamaki
kafin taci gaba da cewa, tohhh?- tabbbdi, tohh nidai a eya tunanina da kuma sanina wannan gidan ba school ba ne, sannan kuma banga yaran da yakamata wa'anda ake koyar dasu *A.B.C.D.* ba, kuma ni a eyanan kadai nasan da akwai wata abu *K,* aciki...
Oh" na manta, natina da tv a kunne yake " mai yuwa anan ne naji ankira Kalmar *K*" daga haka, bata tsaya jin komy ba, tai shigewar ta daki, tabarshi nan a zaune mamakin duniya yataru yamasa yawa, yauce rana ta farko da yad'a qare mata kallo, bama kamar abinda yafi dauke masa hank
li erin d'an mitsitsin " bakin ta shi yafi tafiya da tunaninshi baki daya,
edanun ta kuwa tubar kallah sai wani juyasu take tamakar zasu fado, kai
wannan yarinyar zata kashe ni da yawa fa, yace a ransa kafin shima ya miqe a tsaye kasancewar shi ba ma'abocin kallo bane yasa sam bai eya kashe tv ba shi yasa ya barshe a kunne nai ya haye sama dan shi kadai yasan yanda yakeji.
da kamar 5 mint da haye warsa zee ta leqo kanta a hankali cikin parlour ganin da tayi ne yatashi shiyasa tafito gaba daya, dai-dai tsakiyar parlour ta tsaya tare da yin wani murmushi da yamatuqar qara qawata fuskar ta, A hankali tace wllh guy dani kake zance, takashe komy tare dayin shrgewar ta daki tayi Addu'a ta kwanta,
Haka Emran da Zee suka raya wannan dari nasu day
kasance na FARKO, wanda kamata yayi, dasu rayashi da soyaya dan samun d'imbin ladar dake tattare dashi.
*ASUBA TAGARI*
*_ZEE & EMRAN_*
[7:22PM, 2/22/2018] Official sa'adat Alkali:
Chapter 55 · 0% Book details