← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(62-63)*... Atsaytsaye suke bakin Emergency room dik hankalin su a tashe, mamy, Afrah sai kuma daddy da qasim da aka kira a kasanar dashi halin da, ake ciki..
doctor ne yafito daga cikin dakin, cikin hanzari su daddy suka tareshi suna tambayar sa halin da emran yake ciki, ajiyr zuciya ya sauke kafin yace daddy da qasim susameshi a office,..
a gaskiya ranka yadade emran nacikn mawuyacin hali dan har yanzu munkasa samo kansa,
*Ennalillahi wa,enna elaihir raji,un*
tohh yanzu doctor bakusan a bunda ke damunsa bane?
gaskiya ranka yadade, abu daya ne muka gano shi shine, zuciyar shi nada matuqar rauni, abu kadan za'a mata, yanayin bugawar ta zai canza, kamar na 6acin rai haka, kokoma wani abu marar dadi,
tohh yanzu doctor ba dai wani matsalane zuciyar shi takamu da eta ba ko..?
Ehhh... tohhh hashashe na, shine a gaskiya koda yanzu ba tada wata matsala matuqar zataci gaba da fuskanta abunda zai canza yanayin buguwar ta a kai2 lallai ba abunda zai hanata kamuwa da mummuna wani abu,,,
kansa daddy ya dafe
cikin jimamin wannan lamari, azuciyar shi yake tinanin tohme ke damun emran haka, da har yasa kansa cikin wannan hali, kar dai akan zancin auren daya mishine ya sanya abun azuciyar sa, yana tsaka da wannan tunanin wata nose tashigo cikin office da sauri tana cewa doctor kazo da sauri mun samo kansa,,,
haba... ay dikan su da sauri suka fece daga cikin office,
mama dan Allah kiyi hanquri ki dai na kukan nan, wllh wannan kukan da kike baya da wani magani, bashi zaysa zainab tadawo cikin gidan nan ba, dan Allah ki dayna kada ayi biyu babu, gashi kina fama da ciyon hawan jini, kada yazo ya tashi dan Allah mama kiyi haquri mucigaba da addu'a ensha Allah zainab zata bayyana a ganta, matuqar addu'a natasiri a doron qasa, ba zamu fasa yinta ba, kuma da ekon rabbu zainab zata dawo garemu...
hakane mas'ud mama tafada tana share hawaye ta, da mayafin ta" tabbas nasan kuka ba zai dawo mana da zainab ba, amma abun da ciyo ne, kuma da daga hankali yake, wllh dik edan natuna yanxu zainab bansan awani hali take ba, kuma a ena take dika bamu saniba sai naji hankali na yaqara matuqar tashi, taya hankali na zai kwanta har nasamu sukuni zainaba bata akusa dani, wllh dik wanda yamana haka Allah ya sakama na tsakanin mu dashi, kuma ena roqon Allah ka bayyana mana zainab cikin gaggawa, kada kabawa wa'anda suka dauke ta damar cutar da eta, dan nabiyull rahamati, taqare maganar ta, tare da sakin wani erin kuka mai matuqar ciyo...
ameen! ameen!! mama ki dayna kuka Allah zayshige mana a gaba, shima yana matsar kwalla qarfin hali kawai ne yake, bari naje masallaci, dan naji anata kiran sallah la'asar muyita miqawa Allah kukan mu...
kafin kace haaa" asibitin da aka kwantar da emran tacika maqil da manya2 mutane dan taya dan takarar shugaban qasarsu, kuma adili garesu jimamin rashin lafiyar dansa da yake mutuwar so,,
zo kaga 'yammata masuji da kansu diyan qosashin governorty masuji da qasaita da mulki, yanda suke kuka da hawayin su, saboda rashin sanin wani hali emran yake ciki, abin soyowa azuciyar su...
dik wanda ke cikin asibityn nan yasan da rashin lafiyar emran...
ana cikin haka doctor yafito yana share zufan dake a fuskar sa, zo kaga yanda aka kewayesa, kafin likitan yasamu damar cewa, *Alhamdulillahi Allah*} sai muqara gode masa dan munyi nasara yalla6ai ya dawo cikin hayyacin sa, yanzu haka mun fita dashi ezuwa qofar baya, dan kayshi daki hutu na musamman dake cikin wannan Hospital,
dan haka enaso kowa ya kwantar da hankalin sa, ensha Allah da zarar ya farfado zamu muku ezini da kugansa,
wayyo dadi asibiti tacika da murna da farin ciki, kyaututtuka kam doctor yashasu da sauran wa'anda suka taimaka masa a kasamu nasarar ceto, rayuwar emran,
anan take daddy yayiwa qasim umarni aje afitar da kaya a rarrabwa mabuqata sadaka, saboda nuna godiya ga Allah madaukakin sarki daya amshi addu'ar su, sauran ma abokanan daddy kudi suka bada masu yawa sosai, da aje ararrabawa mutane sadaka Allah yaqara bawa emran lafiya,
*lallai emran dan gata ne gaba da baya, na shaida hakan*
cikin wani daki take mai matuqar duhu da tun sanda tafarka ta ganta acikin sa, bata ta6a ganin wani haske cikin dakin da take ba, sai dai endan aka turo mata abinci da ruwansha take ganin alamar dan haski ya ratso daki,
kuma dik yadda tayima mai kawo mata abinci magana bayace mata uffan'" barema har taga fuskar sa, ruwan da ake kawo mata ne na sha, dasune ne take samu tayi alwala tayi sallah,
cikin wani erin mawucin hali take, tana rayuwa ne, tamkar a cikin kabari, taci kukan ta harta gode allah
kullum addu'a take Allah kafitar da eta cikin wannan qangi da take ciki, tasan yanzu duk enda hankalin family ta yake, a tashe yake, ga yayan ta, dake da ciyon xuciya ga kuma mamarta na fama da hawan jini, tsoronta garwani abu ya same su, tinawa tayi da khaleed, taqara fashewa da kuka,
tinanin take wani marar emani ne, yamata haka me tamasa, tunanin ta yafi tsayawa da mutunmin da take jin tsanarsa na ratsata a zuciyar ta, tabbas tasan shika dai ne" zai mata erin wannan abun, jintayi ta dada tsanarta a kansa feye da tunani,
ranka yadade yalla6ai ya farfado fa, ay dika jama'ar dake gurin sukayi saurin miqewa a tsaye,
doctor yayi saurin cewa, am ranka yadade kana eya shiga kayda mahaifiyar sa, ka dai saboda, gaskiya ba zaiyu a shiga da yawa ba, sai dai duk mai buqatar ya gansa suyi haquri har zuwa anjima ko gobe da safee, zamu eya bada damar ganinsa amma yanzu yanayin nan, da yake ciki gaskiya baya son yawan surutu, *_{{ toh daman ya lafiyar kura bare tayi hauka_*}}
ba dan sun so hakan ba, dole suka haqura mutanin dake gurin, daddy ka dai da mamy doctor yawa jagora ezuwa dakin da yake, ko Afra da taso matuqa tagansa, qin yarda doctor yayi,
kwance suka taddashi harya fada, yaqara wani erin haski edonsa kadai ne ke motse ya kafesu dasu tamkar yau ya saba ganin su,
ruwan hawaye kawai kebin fuskar mamy kafin tace emran cikin wata erin murya wacce ta dishi saboda tsabar kuka da tasha,,
emran dan darajar Allah kafada mana abunda ke da munka, da har yayi sanadiyar janyo maka wannan mummuna abu,
meka nema karasa, me kake so, a fadin duniyar nan, da ba zamu eyayimaka shi ba, kafada mana abunda kaki so, ko yake da munka ko dan kawai namaka zancin aure ne?
toh edan har hakane, na dayna zanbaka lokaci har sanda katashi dan kanka, kuma zanci gaba da maka addu'a Allah ya baka macci tagari,
shiru yayi bayce komai ba, bayan edonsa da ya lumshe tamkar mai bacci,
mamy ce tace daddyn ameer muqaleshi yaqara samun futu ko zuwa anjima ne, mai wuya bai gama samun dai-dai tuwa ba, edan yaso zuwa gobe sai mu tambaye shi, muji matsalar sa,
haka dai suka gama zantikan su, harsuka fita bai ce musu uffan ba,
ga magana yana son yi, amma tsabar miskilanci yasa baya eyayi,
[10:40AM, 1/13/2018] A:

(WANI SALO)
~-------------------------------------~
*Written-by
*Sa'adat alkali D/tsafe*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*(64-65)*...mama! mama!! na'am khaleed, mama wai yaushi ne aunty zata dawo ne, ko dai tatafi enda taje ne ranar, ya fada yana mai shaga6e fuska tamkar zaiyi kuka,?
wani murmushi mama tayi erin mai ciyon nan, kafun tace kayi hanquri khaleed ensha Allah auntyn ka zata dawo nan bada jimawa ba kaji,
tohhh- ayni mama kullum haka kike tacewa kumani har yanzu bangan ta ba bata dawo ba,
zaka ganta khaleed kaji,kaci gaba da addu'a, Allah zai dawo mana da auntyn ka,
yanzu katashi kaje na aykeka gurin musa mai kayan miya, kayo mana cefani mu aza ko wani abune muci kafin baban ku, ya dawo da yayan ku ko?
cikin rashin qwarin jiki ya tashi, tare da cewa yanzu mama da aunty nanan da tare zamu tafi gurin cefanin nan, dan Allah aunty kidawo garemu, wllh ina kewarki, mama ma haka, nason ganinki, haka khaleed yaci gaba da surutun shi gwanin tausayi,,
yauma kamar kullum bude daki akayi mai kawo mata abinci ne, haka wanda ya kawo mata abincin ya fita ba tare da yace mata komy ba,
etama yau qin mishi magana tayi tinda ko tamishi, ba amsa mata zaiyi ba,
da kamar mint 27 da fitarsa aka koma bude dakin aka shigo tada kanta tayi tana kallon mai shigowa, har cikin dakin ya shigo ya tsya dai2 gurin da ya tsinkaye ta azaune lokacin da zai shigo, amma eta kokadan bata ganin wanda ke tsaye a gabanta, saboda tsabar duhu dake cikin dakin,
ya dade a tsaye agurin kafun yatafa hannuwan sa, har kusan sau biyu,
nan da nan haske ya gaurayi cikin daki, saurin rufe edanun ta zainab tayi, saboda yanda haskin taji yamata wani eri a cikin edanu, sakamakon kwana da kwanakki da tayi, a cikin daki mai matuqar duhu,, edonta sun dade arufe, kafun wanda ya shigo ya mata magana" kamar daga sama taji ance, bazaki bude edonki kiganni ba,
sannu a hankali kuwa tafara bude edanunta tin daga kan qasan qafafuwan wanda yake a tsaye, tafa bi da kallo har ezuwa kan fuskarsa data dire edanuwan ta a kanta..
wata erin zabura ne tayi, tare da miqewa a tsaye hannuta nata rawa bakinta ma na karkarwa saboda tsabar kaduwa tare da nunashi da dan yatsan ta, cikin wani erin tashin hankali da tsananin mamaki take son cewa....
yau wallahi sai a slow banajin jikina dai-dai, sai zuwa anjima nagani ko zan eya muku wani typing, dan Allah kiyi haquri...
[10:40AM, 1/13/2018] A:
Chapter 30 · 0% Book details