← Book details Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 60

Sashe 27

Wani Salo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(WANI SALO) ~-------------------------------------~ *Written-by *Sa'adat alkali D/tsafe* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION *(58-59)*... shiru kakeji a cikin daki, ba kajin komy sai kukan Ac, tamkar ba mutane a cikin dakin, Afra ce kadai tatashi tashiga toilet dan dauro alwala sallar magarib, zee kuma magani ta dauko tasha bayan tasha ne,.. tadauko jakarta tana parking din kayan ta a ciki jaka, qwallah duk ta taro a edon ta, abu biyu ne kecin zuciyar ta, na farko rashin lapiyar baban ta, na biyu kuma haka kawai takejin batajin dadin tafiyar kwata2 dik da son datake taga yayan ta, amma bata farin ciki da tafiyar batasan meyasa ba, sadiya kuwa riqi take da waya tana ta, charting amma rabin hankalin ta na gurin zee da taga tana shirya kayan ta a cikin jaka, aranta take cewa Allah yasa tsinanna yarinyar nan tafiya zatayi.. Afra ce, tafito daga toilet taga zee nashare qwallah tana shirya kayan ta, edo tazaro tamkar taga wani abun tsoro, tace ya kuma haka sisi ina zaki tafi naga kina shirya kayanki haka a cikin jaka? hawayin dake zubomata ne tashare kafin tace, babana ne, baya da lpy gobe zantafi gida, wata nannauyar ajiyar zuciya sadiya tayi da taji zee zata tafi gida har cikin ranta taji dadin haka, Afra matsowa tayi a hankali gurinta tare da dafa kafadun ta, cikin muryar lallashi take mata magana, eyya sisi kiyi hanquri kinji addu'a zaki mishi ensha Allah zai samu lafiya, ki dai na kuka banaso, wllh kina tadamin hankali ganin hawayin ki, pls kidai na, edan ma ban da sis sadiya na gidan nan wllh da tare zamu tafi.. amma ensha Allah dik randa zata tafi, tare zamu tafi, na sauka a gidan ku, kibani Address din gidan ku kafin kitafi, hawayen ta, ta share tareda daga kanta takalle afra dake tsaye tace nagode sosai sis da kulawar ki gareni, haqiqa dake da mamy Allah kadai zai saka muku da erin yanda kuke kula dani, da kuma dawainiya dani nagode sosai, kuma naji dadi matuqa da zaki zo gidan mu, kuma zan baki Address din gidanmu yanda bazai miki wuyar ganewa ba, Ywwa sisi nima naji dadi but.. dai ba tafiyar kenan ba, zaki dawo Abuja ko? wllh sis bansani ba, amma ensha Allah zandawo kodan ke, rugumi junan su sukayi, tareda jin kewar junan su, naratsa su, ta6e vaki sadiya tayi kafin ta tashi tafita cikin dakin.. bari nayi sallah naji antada sallah garake kinada uzuri.. murmushi suka sakarwa juna kafin Afra tasa hijab dinta, ta tadda sallah... kwance yake a cikin bedroom dinsa, saman tsadaddin gadon sa tamkar wanda a kayi da ruwan zinare saboda tsabar haskin da gadon kiyi, tashi yayi tareda jawo laptop dinsa, aransa yake cewa yafadace gobe Monday nafita office, saboda 2 days bai shiga ba, saqon zuwanshi gobe ya turawa manager da kuma buqatar ayi sanarwa gobe dik wa'anda ke zuwa neman aiki ana sallamar su, akan bayanan sai yadawo, toh yanaso afada musu suzo dun a musu interview, bayan ya tura ne yaci gaba da aika saqonnen sa, asauran kamfanonin sa, dake qasashin waje.. dan kawai yamanta da, damuwar da kecin ransa, dan yayi Alkawarin babu abinda zai koma hadashi da yarinyar nan, beye mata da yaye ne yasa har ta rainashi har wai zata dubi shi tace bai san darajar mutane ba, yana kuma wai neman qetare eyakokin Allah, gashi daman kuma hakan yayi gudu, amma bai tsira ba, dafe kansa yayi dan siririn tsaki yaja, qasim ne, yafado mishi arai danshi a ganin sa dik shine yaja masa haka, tinda dalilin bukin sa ne, dik hakan tafaru, wayarsa ce tafara ringing dubawa yayi yaga Daddyn sa ne, ke kira saurin dauka yayi yareda sadda kansa qasa.. cikin sanyin murya ya gaida daddyn sa, a can daya 6angarin daddy yace ya akayi gashi har anfara kira sallah nazo masallaci ban ganka ba, bayan kuma dik edan nazo masallaci anan nake taddaka.. cikin girmamawa yace wllh daddy ban san tym yayi bane, amma ganinan yanxu dana dauro alwala zan fito kafin a tada sallah... yakama kahanzar ta, kuma idan muka gama sallah daman akwai maganar danake son muyi da kai... gabansa ne yaji yafadi kardai daddy zancin aure ne zai masa, jin yayi jikinsa yayi wani eri, yanaji kayi shiru kafayi sauri dan kasan ba tsayawa jiranka zamuyi sai kazo za'a tadda sallah ba,, am! am daddy ensha Allah zanma fito yanzu.. tohh yayi daddy yace tareda fara katse wayar sa, cikin mutuwar jiki emran ya shiga toilet tareda dauro alwala yafita daga part dinsa, zuwa masallaci... bayan sun edar da sallah ne sunyi addu'o'en da suke suka fito atare, wani part naga sun shiga da ban ta6a tunanin a kawaishi a gidan ba, securitys kusan 6 ne ke a gurin da hanzari aka bude musu qofa suka shiga... masu karatu bazance komy ba, kada kucemin nacika zuzuta abu, bayan kuma ba haka bane abinda edona ya ganimin ne, tsarowar parlour kam bazance komy ba, amma kunsan ay dik parlour da ake sauke baqi edan akayi aqasar waje kunsan ba qaramin tsaruwane da kyau yakeda shi ba, amma nabar muku ku qiyasta da kanku kugani.. guri suka samu suka zauna har emaran zai zauna qasa daddy yace a..a yazauna kusa dashi dan zasuyi muhummiyar maganane.. emran daddy ya kallah kafin yakira sunan sa, sai da gabanshi yaji ya koma faduwa, jin muryar daddy ba alamar wasa, kafin ya amsa yace na'am daddy.. ba komy yasa kaji nace enason magana da kai ba, ellar inason enfada ma jama'ar qasar nan sun nace akan lallai sunason na tsaya takarar shugaban qasa, aza6en nan da za'ayi, bama kamar.. *His Excellency* Ayuba A tukur.. yanunamin qwarai ya keson edan ya sauqa yanason na hau kan kujerar saboda yanda jama'a keson natsaya awannan sugabanci.. banqi ba, amma wllh ena tsoron shugabanci arayuwa ta, ko yau meeting din da kaji nace zanje, maganar dai ce aketa man tareda roqona alfarma, toh shine nace musu su bani kwana biyu zanyi shawara, shine nace toh bari nafara tuntu6arka kafin nafadawa mahaifiyar ka, Kai meka gani mezaka ce? Ajiyar zuciya ya sauke da yaji ba zancin da yake tsoro bane.. kafin yace.. haqiqa daddy maganar ka ce, shugabanci nada matuqar wuya, toh amma edan har ka tsare adalci da gaskiya, dik da Allah kadai ne, ya keda eyawa amma edan ka kwatan ta hakan, komy zai zo maka da sauqi, ni dai aganina da kuma shawara ta, kadaure ka amshe buqatar bayin Allah nan, tabbas da basu yaba da kai ba, da basu nace akan sunason kazama shugaban su ba, sunga ka cananta ne, shiyasa sukeson kamaye kujerar mai girma Ayuba A tukur, kaga edan baka kar6e buqatar su ba, bazasuji dadi ba, kuma kabada qafane ga Azzalumai da suke qoqarin ganin al-ummar qasar nan, cikin wahala da uquba... fatana ka amshe kukasu kayarje musu mukuma zamuci gaba da maka addu'a Allah ya tayaka riqo yabaka ekonyin adalci,, yakuma tsare gabanka da bayanka daga Sharrin masu sharri... daddy ameen2 yake ta amsawa tareda kuma jinjinawa emran da qoqarin da yayi, na lurasar dashi da yayi kuma yayarda da bayanin sa, 100% haqiqa yana godewa Allah daya azurtashi da 'ya'ya nagari fatamshi Allah ya qara shirya su, da suda na jama'ar musulmi baki daya... emran naji dadin bayanin ninka kuma nagamsu zan sanar da mamyn ka yanzu dana shiga kuma ensha Allah na Amince da buqatar su, Allah kashige mana gaba, Ameen daddy nima naji dadi sosai daka fahimce ni Allah yayi maka jagora, ameen my son.. Har yanzu dai kaqi wa kanka fada ko? kafitar da mata kayi aure kaqi, Naseera 'yar His Excellency tayi biyarka harta gaji kaqi kulata, da duka sauran 'ya'yan abokanayna ba wacce bata nuna tana sonka ba, amma emran kabani kunya kaqi ko kallonsu, enya rayuwa natafiya haka kuwa emran? enfa mune yau ba famu bane ba, gobe, yakamata kawa kanka fada, enajiye maka tsoron kar mutuwa ta riskeka hakan da kake,, da lafiyarka da komy naka gwargwado Allah yabaka amma ace kaqi kayi aure, wace amsa zaka bawa ubangijin ka lokacin da riskeshi, emran ena dada jan kunnen ka kamay da hankalin ka, zuciyar shi ne yaji ta karye maganganun daddyn sa, keta mishi yawo a qwaqwalwa, haqiqa maganar daddy gaskiya ne toh ammashi gaskiya.. kayi tunani ni zanshiga daga ciki Allah yasa mudace... maganr daddyn shi takatse mishi tinanin da yake.. Kafin ya amsa da ensha Allah daddy zan duba.. toh Allah yasa yakuma bada sa'a yaza6a maka macce ta kwarai mai kirki da hankali.. canciki yace ameen... tare suka fita daga cikin parlour zuwa part din mamy dan yin dinner,,, Afra ce na hango dauke da jaka,, zainab na saqale da mamy tanata zuba mata godiya saboda Alkhairin da suka mata, ko daddy kuddi ne yabata bana wasa ba.. bare mamy data hada mata komy.. koma tace edan suka esa zariya akwai shagononin emran dake garin, na abinci da sauran abubuwa, driver da zai kaita subiya tadauke dik abunda take so, amma a ranta tace bazata ta6a tafiya shagonan sa ba, toh me zatayi da kayansa dama na mamy ne, *(niko nace dik dai)* sai yanzu kuka yazowa, Afra da taga zee da gaske tafiya zatayi, amma data tuna tabata Address din gidan su yanzu kafi su fito, sai taji dan sanyi a ranta, driver mamy ta kalla kafin tace sulaiman ena jamilu ne,? naganka bayan shi nace yazo ya kai ta.. am Hajiya sun fita da yalla6ai ne office shi yasa yace nabaki haquri nazo na kai ta... murmushi mamy tayi kafin tace Oh emran manya waton yau anga damar fita office kenan ciyon kan har ya sauka.. toh shikenan zainab shiga kutafi Allah ya kiyaye hanya muna gaida gida ki gaida abbanki da jiki kinji.. tohm mamy ensha Allah zan fada musu, ena kuma dada godiya Allah yasaka da Alkhairi.. ameen zainab Kazal" Afra tayi tace sisi sai nazo.. murmushi zainab tayi tace ena dibinki edan kuma baki zoba toh Allah niko bazan koma dawowa ba. a...a zamma zo ko mamy? a.... baruwana wannan zancin kune, amma karki damu zainab, zata zo kodan ta duba abbanki, nima dan daddyn su na gareni yasa bazan samu damar zuwa ba, Ba komy mamy ko afra ma taje dik daya ne, haka dai suka gama sallamar su,
Chapter 27 · 0% Book details