← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 81

Sashe 78

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Barrister sannu da zuwa”.
Cikin jin daɗi ganin yadda Jannart ta dan sake a cikinsu yace.
“Barka dai Hajia ya bakuwarku?".
Murmushi Mamy ta ɗanyi tare da cewa.
“A'a ai mu bamu da bakuwa, mu duk nan yan gidane”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu.
Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart daketa murmushi tace.
“Jannart kawo masa ruwa ko.”

Mik’ewa Jannart din tayi, Tana murmushi, taje ta kawo masa ruwa da kuma ragowan drinks din da ta had’a, harma da sandwich din.

“Abbana sannu da zuwa.”
Ta fad’a cikin tsananin farin cikin da ta samu kanta aciki, tare kuma da ajiye masa dan tray din da ta Hado ruwan agabansa.

“Yauwa Jannart sannu.”
Barrister Kabir din ya amsa yana murmushi, tare da juyawa suka gaisa da Mamy.

Ramadan da Riyyam ne kuma suka gaidashi, fuska asake ya amsa musu.

Jannart kuwa sabida tsananin jin dadin ganinsa, dan matsowa kusa dashi tayi, tare da manna kanta jinin hannun kujerar da yake zaune a kai, cikin yanayin rauni tace.

“Abba Ina kwana.”

Murmushi Barrister Kabir din, yayi cikin jin dadin yanda ya ganta yace.

“Lafiya k’alau Jannatuwa, ya kwanan bak’unta.”

Kanta tad’an sunkuyar kasa, fuskarta dauke da dan murmushi tace.

“Alhamdulillah Abba, yasu Aunty Dijat Hafeez,da Hafeeza”.

“Alhamdulillah suna lfy”.
Ya bata amsa yana kallonta.
Cikin nitsuwa tace.
“Ayya Abba da kazo min da Hafeeza.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da dubanta yace.

“Uhummm Jannart kenan, waya gaya miki yanzu, bayanni akwai wanda zai na kawo miki ziyara.”

Fuskarta ta dan shagwabe, cikin sanyi tace.

“Ayya Abba yanzu har Aunty Dijat dasu Hafeez babu mai zuwa, ba wanda zaizo wajena kenan.”
Kai Abbansu Rayyern ya jinjina tare da cewa.
“Shima ai zamu hanashi zuwa sai naga kin saki jikinki kin dena zama kina tagumi da zubda hawaye”.
Da sauri tace.
“Abba na dena”.
Yar dariya sukayi kana
Barrister Kabir yace.
“Ato kin dai ji kam ko”.
Turo dan karamin bakinta gaba tayi, wanda hakan yasa Mamy, Ramadan da kuma Riyyam duk sukayi murmushi.

Adai-dai lokacin kuwa Rayyern wanda fitowarsa daga part d’insa kenan, ya soma saukowa daga kan steps din, cikin shigar wani lallausan yadi mai kalan mobile blue mai masifar taushi da sheki wanda akayi masa dinkin half jamfa da kuma, wando pencil, sosai kayan sukayi masa masifar kyau yanayin kalarsu ya kara hasko farar fatarshi ta fito ras,
Hular damanga farace a amsa mai ratsin Nobel blue ɗin.
Yayinda kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa ke zuba sheki har wani dauke ido yakeyi.
Sai takalmin toms Noble blue dake kamarsa.
Kamshi kawai yake zubawa, yanayin yanda yake takun nasa kuwa cikin dan sassarfa alamun sauri yakeyi.

Yayi kyau matuk’a, Daddaɗan kamshi da kuma jin sautin takusa ne kuma yasa, duk suka kalli steps din.

Dai-dai lokacin kuwa ya gama sauk’owa.
Ganin Barriter Kabir da yayi ne kuma, yasa shi ɗan yamutsa muskarshi.
“Kai wannan menne irin mutum ne mai masifar nacin tsiya mutun kamar maye!.
Wannan jaraba har ina, toh yanzu kuma Meya kawoshi da sanyin safiyar nan, kamar mai binmu bashi.”
Yayi mgnar zuci tare da kwaɓe fuska yana mai k’arasowa cikin falon.

D’an rusunar da kanshi yayi, cikin naɗe murya can ƙasa yace.

“Barka da zuwa Barrister.”

“Yauwa Barka Dr. Rayyern.”
Barrister Kabir din ya amsa masa, cikin sakin fuska.

Rayyern din kuwa dan matsawa gefe yayi, tare da zama akan kujera dake gefen Ramadan.

Ganin hakanne kuma yasa Abba kallonsa, cikin kulawa yace.

“Rayyern fita zakayi ne.”

“Eh Abba”.
Ya bashi amsa a takaici.
Cikin tsaresa da ido Abba yace.
“Ina zakaje”.
Ya ƙare tambayar da alamun son cikekken bayani ina zaije me kuma zaiyi.

Hannunshi ya ɗan d’ago.
Tare da saidashi kan wuyanshi.
Ya ɗan shafa wuyanshi har zuwa kan ƙeyarsa kana a hankali yace.
“Inason zanje company ne, saboda P.A yamin waya, wai akwai wani inji da ba’a gane kansa ba, like dai baya aikin daya dace kana Engineer bello yana can yana jirana shima.”

Kai Abban ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.

“To Allah Ya bada sa’a.”

Da “Ameen.” Ya Amsa.

Barrister Kabir kuwa, ledan dake hannunsa ya mik’awa Jannart dake zaune akasa, cikin kulawa yace.

“Jannart ga waya nan na sayo miki, akwai new sim acikinsa, bayan number na kuma bansa miki numbern kowa ba, sannan kada ki fara amfani da laptop dinki yanzu, kina dai charging nasa amma kada ki yi using dashi,domin hakan zai taimaka wajen gujewa duk wani shaida.”

Karb’an ledan da yake mik’o mata din tayi, cikin jin dadi tace.

“Nagode sosai Abba Kabir Allah ya kara budi.
Amma fa jiya Abba ma ya sayamin sabuwar waya.”

Ta kare maganan tana meyi masa nuni, da Wayar dake hannunta.

Barrister Kabir din kuwa murmushi, yayi cikin jin dadi yace.

“Masha Allah waya tayi kyau sosai, Allah yasanya al'khairi ya kuma saka da alkhairin.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa, saidai banda Rayyern wanda ya kawar da kansa gefe yana kallon Riyyam-nsra daketa lallatsa woya ya kifa kai har kamar zai hade goshinsa da wayar haka yasa ya tsareshi da ido yana nazartarsa.
Dan ko kasa inda take dinma bai kalla ba sai dai yana jin amon muryarta.

Barrister Kabir kuwa Mikewa tsaye, yayi tare da Kallon Jannart din, cikin tausasa murya yace.

“To Jannart ni zan wuce, dama sakon da nazo kawo miki kenan.”

Murmushi Jannart din tayi, cikin sanyi tace.

“Abba ka gaida gida, ka gaishemin da Aunty Dijat dasu Hafeeza.”

“Zasuji Insha Allah.” Abban ya fad’a, tare da juyawa yayiwa Mamy sallama.

A gaida gida Mamyn tayi masa, sannan suka fice shida Abba.

Ganin hakanne kuma Yasa Rayyern ma mik’ewa tsaye.

“Rayyern katsaya kayi breakfast tukun kafun ka fita, gacan abinci akan dining.”

Cewar Mamy tana me kallonsa.

Fuskarsa ya d’an ya mutsa, tare da Kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa, adan kasalance yace.

“Mamy banajin yunwa sosai, kuma Idan na tsaya break zan makara, saina dawo kawai ki ajiyemin lunch.”

Ya k’are maganan yana me nufar hanyar fita daga falon.

Wanda hakan yasa Mamy da Ramadan suka Bishi da kallo, Mamy kuwa har cikin ranta tana mamakin, yanda Rayyern din yake tafiyar da rayuwarsa, gaba daya sam cin abinci bai damesa ba sai dai wasu lokuta isasshen lokacin zaman cinnema yake rasawa, shiyasa idan ya tara yunwar tofa in ya samu ya ya zauna zaici da dama.

Rayyern kuwa Koda ya fito compound din gidan, ya samu tuni harsu Abba da Baba Maud’o sun tafi, Yayinda shima Barrister Kabir Yayi nasa tafiyar.

Motarsa ya shiga, Yayinda Hadi ya jasa suka fice daga Cikin gidan.

Acan falo kuwa, har Rayyern din ya fice Jannart bata iya sake dago Kai ta kalleshi ba, saboda tun Kallon farko da tayi masa, taji zuciyarta na bugawa, wanda kuma batasan dalilin hakan ba.

Bayan fitan nasa ne kuma ta d’ago kanta tare da Kallon Mamy, ad’an ladabce tace.

“Mamy yau me zamu dafa da rana.”

Murmushi Mamyn tayi, kana atausashe tace.

“A’a Jannart yau kam kihuta, ina nan zanyi komai, basai kin wahalar da kanki ba wannan fa aiki nane!!!.”

“Mamy ba wahalar da kai bane zanyi, na saba ko agida ma duk ranar da babu aiki Ina taya Momy duk wasu aikace-aikace gida, Dan Allah Mamy ki bari Ina tayaki ki dena cewa na bari.”

Jannart din ta fad’a cikin tausasawa.

Hakanne kuwa yasa Mamy jin sanyi acikin zuciyarta, saboda tasan Itakam tayi sa’ar suruka.

“Shikenan Jannart babu damuwa, na baki wuk’a da nama ki dafa mana duk abunda kikeso.”

Mamyn ta fad’a cikin sakin rai.

Riyyam nsra kuwa, cikin dokin cin abincin Auntyn tasa yace.

“Yauwa Aunty Jannart muje kitchine din, ni yau da kaina ma zantayaki aikin, amma mezaki dafa mana me dadi haka?”

Murmushi Jannart din tayi, tare da cewa.

“Muje zaka gani.” Yanayin yanda tayi maganan tana me mikewa tsaye ne, yasa Riyyam din rufa mata baya suka shiga kitchine.

Shida kansa yayi mata wanke wanke, Yayinda ita kuwa tayi greetting kwawa, saboda abunda ta tsara zata dafa musu shine.
Coconut rice, and onion sauce, sai kuma gas meat mai kayan kamshi, da salad cream, ab’angaren drinks kuma, Banana Milk shake zatayi musu.

Anutse ta fara aikinta, Yayinda Riyyam keta yi mata hira, daga gefe guda kuwa yana tayata da y’an wasu ayyukan, kama daga kan yanke yanke zuwa yan kananun abubuwa masu sauk’i dai.

Haka dai sukayi aikin cikin nutsuwa, almost 1hour kuwa ta kammala komai, tare da jeresu akan dining table.

Gaba d’aya gidan kuwa haka ya gauraye da kamshin girkinta.

Bayan sun kammala jere komai a dining table dinne kuma, ta kunna boner tare dasa turaren wuta mai dadin kamshi.

Mamy kanta ta yaba da aikin Jannart din, bayan sunyi sallan azahar ne kuma, suka zo kan dining table din sukaci abincin.

Saidai kuma Jannart din bata wani ci abincin sosai ba, ayanda Mamy ta fahimta kuwa shine, Jannart din irin Rayyern ce, kwata kwata basu dauki cin abinci serious ba sai dai tasan shi Rayyern in ya zaunawa abincin bai mishi da wasa ko dan yakan dade baici bane, ta lura ita kuma Jannart irin mutanen ne da zasuci kaɗan yanzu anjima su kuma cin kaɗan.

Bayan sun kammala cin abincinne kuma suka dawo falo, hira suka Dan tab’a, lokacin da Ramadan da Riyyam suka fita yawo ne kuma, Jannart ta tashi ta koma side dinta, tana kwanciya afalonta kuwa bacci ya dauke ta.
Chapter 78 · 0% Book details