Sashe 45
Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fita su Ramadan na fita da kulolin ƙarshe.
Riyyam-nsra ne ya buɗe mishi gate ya fita.
Kana ya rufe sannan suka dawo cikin gida.
Bayan duk sun zauna kan table.
Mamy ta kalli Ramadan tare da cewa.
"Kira Abbanku”.
To yace kana ya miƙe ya sauƙo steps ukun tare da cewa.
“Abba breakfast is ready”.
Wani dogon numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe a hankali kana yace.
“Toh”.
Sannan yazo saida ya zauna ya kallesu cikin kulawa yace.
“Rayyern fa!?”.
Cikin nitsuwa Riyyam-nsra yace.
“Abba ba yanzu ya fita kai abincin al'majirai ba”.
Kai ya jinjinawa Riyyam-nsra.
Ita kuwa Mamy cikin fahimtar halin da yake ciki ta zuzzuba musu breakfast ɗin kana suka fara ci.
Mai-nasara Hospital.
Suna cikin hirar Jannart ta ɗan gyara konciyarta tare da lumshe idonta lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba da ita.
Hakanne yasa Abba koma gida.
Aka bar Aunty Dijat.
Abba na tafiya ba dadewa Mom da Abdul suka iso.
Kasan cewar tana baccine yasa suka koma gefe suka zauna suna ɗan taɓa hira sama-sama gudun kada su tasheta.
Yayinda Abdul yake riƙe da wayarta.
Yana mgna da Salman.
Nan ya gaya mishi suna asibiti.
Koda Dr Sulaiman yazo ya dubata.
Ganin tana bacci ya shaida musu jikin da sauƙi sosai.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara.
A hankali yayi parking a gaban tsangayar malam Mai-nasara.
Kana ya fito,
Cike da Mamiki Uncle Mustapha da shima yanzu ya iso da abincin al'majirai da yake kawowa daga gidansan.
Dan al'majiran malam Mai-nasara basa yin Bara shi da yaransa suke ciyar dasu.
Da sauri ya nufi Dr Rayyern cike da mamaki yake cewa.
“Ikon Allah wa nake gani kamar Dr Rayyern Mai-nasara?”.
Da sauri ya juyo suka fuskanci juna, musabiha sukayi cikin jin daɗi yace.
“Ya Malam da jiki?”.
Cikin jin daɗi yace.
“Masha Allah mu isa ciki, malam na nan jiki yayi lfy sosai fa!.”
Ya ƙare mgnar yana miƙawa wani Gardi key ɗin motarsa tare da cewa.
“Yauwa Yayana gashi fito muku da abincinku”.
Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara shima ya miƙa masa key ɗin motarsa tare da cewa.
“Ga wannan ma ka duba baya ka fito muku da abincin”.
Cikin jin daɗi Wanda Uncle Mustapha ya kira da yaya ya amshi key ɗin. Tare dayi musu godiya.
Shi kuwa Uncle Mustapha jagora yayiwa Dr Rayyern Mai-nasara,
har cikin gidan Malam Mai-nasara.
Kana suka nufi wannan falon.
Yana mai cewa.
"Duk ranar jumma'a Malam bai fiye amsar baƙiba, amman nasan kai na musamman ne, mu shiga”.
Ɗan guntun Murmushin yayi kana suka kutsa kai tare da sallama a baki.
Can Dr Rayyern Mai-nasara ya hango Malam Mai-nasara, zaune tsakiyar falon.
Yayinda wata kekkyawar tsohuwa ke gefenshi, da alamun abin karin kumallo take zuba mishi.
Ganin Dr Rayyern Mai-nasara ne yasa Malam yunƙurawa ya tashi zaune.
Cikin yalwataccen murmushi ya miƙo mishi hannu tare da cewa.
“Masha Allah. Wa nake gani kamar Dactana mai Nasara”.
Hannunshi ya miƙa mishi ya jawoshi ya zaunar dashi kusa dashi.
Yayinda ya kalli Uncle Mustapha dake cewa.
“Ai kuwa shine dai Malam”.
Hannunshi ya ɗaura tsakiyar kan Dr Rayyern Mai-nasara tare da cewa.
“Lallai.kuwa yau ka amsa sunanka Mai-nasara dunda kayi nasarar ganina da safiyar jumma'a.”
Cikin son dattijon yace.
"Alhamdulillah Nasara ta haɗu da nasara kenan”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu.
Yayinda tsohuwar nan kuma ta zuba mishi ido tana mai mishi wani irin kallo.
Kai ya juyo ya kalleta tare da cewa.
“Barka da safiya”.
Gyara zamanta tayi tare da sauƙe numfashi kana cikin kulawa tace.
“Barka dai Mai-sa'a. Yau dai da Malam zakayi karin kumallo”.
“Sosai ma kuwa”.
Malam Mai-nasara yace yana mai gyara zamanshi.
Ita kuwa tsohuwar kekkyawan akoshin dake tururin danderun naman ragon ne, ta turo tsakiyarsu.
Kana ta jawo ɗayan kuma tuƙeƙen tuwon alkmana ne mai kyau.
Da miya a kanshi miyar ɗanyar kuɓewa mai kyau tana ƙamshin man shanu, da ƙamshin ɗumamen.
Sai kuma bread mai kyau na masu ciwon sugar sai flask. Da cups biyu.
Misa alamu dai da basu zoba da tare zasuci abinci da tsohuwar.
Kai Rayyern ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Alhamdulillah fa malam kaci kawai”.
Cikin kula Malam yace.
“Ina muci dai, ai dole kaci, tunda ba giya bace, ko kyamar tsoho kakeyi ne?”.
Da sauri ya jujjuya kanshi alamun a a.
Ita kuwa tsohuwar nan ɗan ƙaramin kwaryar dake gabanta da ruwa a ciki ta tura masa tare da cewa.
“Toh wonke hannunka kuci”.
Abu kamar wasafa dole suka matsa mishi.
Allah ya sani yana son tsohon haka yasa ya ɗan gyara zamanshi,
cikin nitsuwa yace.
"To a bani tea”.
Da sauri ta haɗa mishi tea.
tare da amsar akoshin danderun da Malam ke miƙo mishi.
Dole yasa hannunshi cikin kwaryar ya wonke.
Kana ya gyara zamanshi tare da kallon Malam yace.
“Malam ya jikin naka kuma?”.
Loman tuwon daya sa a baki ya haɗiye kana yace.
“Alhamdulillah Rayyanu naji sauƙin jikina sosai sai yawan ci”.
Juyowa yayi ya kalli Uncle Mustapha dake cewa.
“Dan Allah Dacta kaci girkin Innayinmu, zaka jishi da banne dana sauran matan duniya”.
Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye.
Yayinda ita kuwa Innayi tayi murmushi tare da cewa.
“Kwarai kuwa har matarsa ma”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Toh ki bari a yaba miki mana”.
Dariya sukayi duka.
Kana su suka fita.
Ya rage dagashi sai Malam Mai-nasara.
Wanda ya maida hankali kan cin abinci.
Shi kuwa tea ɗin ya ɗan zuƙa a hankali.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗe su.
Tabbas Mamynshi ƙarshece a girki amman daga shayin tsohuwar nan yaji da ban.
A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Malam dake cewa.
“Dan Allah Rayyanu kaci naman nan zakaji dadinshi”.
Kai ya jinjina kana yasa hannunshi cikin akoshin.
A nitse ya ɗan yagi tattausan tsokar kana ya kai bakinshi.
Wani irin tsinkewa yaji yawunsa yayi tare da amsar saƙon ɗanɗanon naman nan mai cike da ƙamshi.
“Ya Salam”. shine abinda ya faɗa a zuciyarshi.
Tea ya kurɓa kana ya ɗan kalli Malam cikin hikima yace.
“Ni ko Malam sunan kakanka ne Mai-nasaran ko?”.
Kai malam ya jujjuya mishi alamun a'a.
Cikin jin daɗi ya gyara zamanshi tare da ɗan ture akoshin gefe.
Sosai naman ya mishi daɗi to amman matsalar bazai iya cin abincin nama da sassafe hakaba.
In yasha tea ɗin kawai ya gamsu sai irin 11-12 haka zai iya cin wani abu kuma.
“Kaci mana”.
Malam yace.
Kai ya gyaɗa kana ya kafe kofin a baki ya zuƙe team ɗin kana ya ajiyeshu gefe, tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah na ƙoshi”.
Murmushi kawai malam yayi tare da wonke hannunshi.
Shi kuwa a hankali yace.
“Toh Malam menene Tubalin sunan naka”.
Toro mishi kwaryar malam yayi tare da yin dariya sosai.
Hannunshi yasa yana wonkewa yana kuma kallon tsohon yana murmushi ganin yadda yake dari.
Cikin tsagaita dariyar Malam yace.
“Lallai kam ka nemi jin tsohon lbri”.
Sai kuma ya ɗan kishingiɗa.
Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara yace.
“A'a Malam tashi zaune, ba'ason mutun ya kwanta bayan cin abinci a take, anfi son ka ɗan zauna koma motsa jiki, ko ga masu lfy kwanciya da zaran an gama cin abinci yana haifar da cutar sugar.”
Da sauri Malam yace to kana ya zauna tare da cewa.
“Tubalin sunana ya samo asaline tun ina yaro ɗan shekaru tara a duniya, da aka kaini al'majiranci.
Anan na samu sunan Mai-nasara nawane na kaina bana Babana bane ko kakana”.
Sai kuma ya ɗanyi shiru ganin hakane yasa Dr Rayyern cewa.
“Tah yaya aka sama sunan?”.
Numfashi ya ɗan fidda kana yace.
“Asalina ɗan jihar Adamawa state ne, yankin Jada al'majiranci iyayena suka kawoni jihar Kano.
Nazo kano bani da kowa sai Allah sai malamina, wanda a ƙalla yakeda ɗalibai sun kai ɗari biyu,200 baya shayar damu bare ci damu.
Mafi akasari ranaku ɗalibai kaso 100 cikin 200 da yunwa suke kwana da wuni.
Wasu kan shiga gidaje 7 ba'a kirasu ba, cikin ikon Allah ni kuma duk gidan dana shiga sai an kirani kuma sai an bani abinci.
Haka yasa abincin da nake samu yafi ƙarfin cikina, sai nake rabawa yara kamata.
Yayinda wasu manyan ma ke zuwa suna roƙata inje musu Bara, duk wanda ya bani akoshinsa sai na cika mai nake dawowa.
Toh fa daga nan ɗalibai suka samin Mai-nasara. Cikin ikon Allah kuma nasarar ta bini. Nayi karatu na tsawon shekaru goma sha biyu na haddaci al'ƙur'ani mai girma da tarin littattafai.
Daga nan kano ta zamemin uwa goya marayu, malam ya bani yarsa itace wannan data tafi yanzu na aura.
Kana na fara kasuwanci Allah cikin ikonsa ya samin al'barka a harkar kasuwanci na.
Na ƙara mata biyu ƙannena suka dawo gareni da iyayena.
Allah ya azutani da yara sama da 37.
Kaga ai nasara ta yiwu, duk da bayan nasarar na fuskanci ƙalubale akan d’a mafi soyuwa a gareni”.
Cikin gamsuwa Dr Rayyern Mai-nasara yace.
“Allah sarki”.
Da sauri ya katse shi da cewa.
“Kai kuma menene TUBALIn sunan naka”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Nima ɗalibai ƴan uwanane suka samin shi.
Sabida duk jarranawar da zanyi bana faɗunwa.
Kuma duk abinda nasa gaba sai na cimmasa”.
Shigowar Uncle Mustapha ne yasa suka tsagaita da hirar, kana akaci gaba da hirar dashi.
Har sai tara dai-dai suka sallami Malam suka tafi
A bakin gate suka samu wannan gardin ya basu keys ɗin su suka tafi.
Daga nan kai tsaye gida ya koma.
~0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 special Group 1k karami kuma 500~