← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 81

Sashe 35

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin gate kuwa Usman PA ne ya shigo da motarsa bayan Hadi ya buɗe masa.
Da sauri ya nufi wurin Baba Mauɗo bayan ya fito.
"Barka da yamma Baba Mauɗo”.
Cikin kulawa Baba Mauɗo yace.
"A'a Barka dai Usmanu! Kwana biyu shiru tunda kuka dawo bana ganinka ka bar Rayyanu shi ɗaya lfy dai ko?”.
Cikin son dottijon yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah Baba Mauɗo, wlh da muka dawo ne Mama, ba lfy ashe ba ciwone matsalar ba, wai tayi kewan ƙannenta tofa dole ranarda muka dawo washe gari ta sani muka tafi Gombe bamu dawo ba sai jiya da dare da yake bamu taso da wuriba”.
Cike da kulawa yace.
“Masha Allah. Allah ya bada ladan ziyara, sai kuyi ta haƙuri damu, iyaye in an fara girma tamkar yara ake zama.
Allah yayi muku al'barka”.
Amin Amin yace.

Kana ya nufi cikin gida.
Da sallama a baki shi ya tura ƙofar falon.

Da sauri Ramadan yace.
"Wa alaikassalam, Yah Usman mutanen Gombe Kun dawo kenan".
Murmushi yayi tare da cewa.
“Oyoyo Ramadan Alhamdulillah”.
Sai kuma ya juya.
Da sauri Usman ya nufi inda Abba ke tsaye rusunawa yayi tare da gaidashi.
Cikin kula Abba yace.
"Usman kwana biyu shiru”.
Cikin girmamawa yace.
“Wlh kuwa Abba sai jiya muka dawo”.
Ya faɗi haka tare da juyawa ya kalli Ramadan dake miƙo mishi hannu.
Musabiha sukayi kana ya kalli Mamy cikin mutuntaka yace.
"Barka da yamma Mamy".
Barka dai tace tana mai nunawa Ramadan Fridge alamun ya kawo masa abin motsa baki.
Da sauri kuwa Ramadan ya nufi Dinning area juice and bootle water ya kawo mishi.
Kana yace.
"Yah Usman bari in haura sama in ɗan watsa ruwa”.

Toh yace.
Kana ya haura.
Shi kuwa Abba ne ya dawo tsakiyar falon.
Mamy kuwa abinci ta kawo mishi.
Kana ta nufi Bedroom ɗin ta.

Yanaci suna hira da Abba.

A can tahir hotel kuwa.
Riyyam-nsra ne zaune bisa kujerar dake gefe.
Video call yakeyi da Mammynsu cikin sauƙe numfashi yace.
"Alhamdulillah Mammy duk abinda muke zato hakane, wlh kuma duk abinda ya tsananta tsawon shekaru yana gab da sauƙaƙa.
Sai dai ta ina? Ta yaya? Da yaushe? Zamu fito da manufarmu ta yaya za'a fahimcemu?”.
Ido Mammynsu ta limshe sai ga wasu irin zafafan hawaye kana a hankali tace.
"Riyyam-nsra nima kaina bani da sanin tudun dafawa
Kuma zuciyata ta ƙara kwaɗaituwa da tsatsonta.
Ta ina? Ta yaya? Yaushe? zamu samu nasara".
Cikin ƙarfin hali yace.
"Mammy keda kike da Riyyam-nsra, kada ki damu ki bada yaƙinin ki a kaina in sha Allah zan kusanto miki da nesa kusa dake cikin aminci".

Yadda yayi mgnar with full confidence ne yasata sakin sassayan murmushi.
Riyyam-nsra akwai ƙarfin hali da yarda da kai, idon ta ita nema da bazaima je Nigeria'n ba amman bisa ƙarfin halinshi yaje.
Kai ta jinjina mishi tare da yin murmushi, ganin ya sata farin cikine yasa shi cewa.
"Ina Deeda tsohuwa da Zayton?”.
Cikin sanyi tace.
“Sun tafi asibiti".
Ya buɗe baki da nufin yin mgna kenan kuma wani kiran ya shigo ɗaya wayar tashi.
Da sauri yace.
"Yauwa Mammy sai anjima zamuyi mgn”.
Kan ta fargama ya katse kiran.
Kana ya amsa wannan kiran wanda shima video call ne.

Wata iriyar fitinenneyar miƙa yayi tare da zaro harshensa ya ɗan lashi lips ɗin shi.
Sabida gamo da katar da yayi da wata kekkyawar baby mai cikar haiba kalar Ethiopia'n Girl's
Tana mishi Ethiopia'n dance.
Wanda take jujjuya mishi ƙirjinta da karkaɗa mishi su da karya kafaɗu irin dai rawar su nan ta sai kaci ka ƙoshi kan ka iya yinsa.

Ido ta jujjuya mishi tare da tsagaita wa da rawar kana cikin yin ƙasa da murya tace.
"I miss you very very very so much sweetheart”.
A hankali ya miƙe ya koma bisa gado.
Idanunshi da suke juye sabida ganin ɗaya daga cikin abokan masha'arsa da suka haɗu sanadin TIKTOK cikin sanyi da kasalar wani irin masifeffen feelings da ya ziraro mishi kamar zai tsinke mishi jijiyoyin jiki yace.
"Nace muzo Nigeria kika ƙi, sannan kuma kina son tarwatsa min kwanya da begenki”.
Cikin iya shege ta zame wuyan rigar ta ta ɗanyi ƙasa dashi.
Kana tasa hannunta cikin rigar ta zaro mishi... Tare da cewa.
"Lollypop"....! Ɗaga nan sukaci gaba da lalatacciyar hirarsu, haka yasa Ramadan nata kira bai amsawa.

A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.
Cikin hatsala Junaidu ya leƙo falon yana mai rabkawa Jannart kira kamar zai yage bakinsa.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ya ida kiran da ƙarfi wanda yasa.
Mom dake Kitchen ta leƙo cikin taɓe fuska tace.
"Menene kake ta ihun kiran wacce bata gidan ma, sai ka tafi gidan Abbanku ai”.
Kwaffa yayi tare da watsawa Mom ɗin harara kana ya nufi Part ɗin Abbansu dan sai yanzuma ya tuno cewa bata gidanma.

Yana isa bakin ƙofar falon.
Dr Lukman da Alhaji Abdu Tababa suna isowa suma da alamun yanzu suka iso.
So kusan a tare suka shiga.
A falon suka samu Daddy wanda dawowarshi kenan shima nan suka zauna.

A gidansu Rayyern Mai-nasara kuwa, Ramadan ne ya fito riƙe da foodflakcs mai kyau. Usman na bayanshi.

“Eh ba asibiti ba yake Campany ya tafi tun safe bai dawo bama”.
Ramadan ya bawa Usman amsa wanda ya biyoshi da nufin zasu tafi asibiti.
Numfashi Usman ya sauƙe tare da cewa.
"Toh ni kam bari kawai in wuce can inda yake ɗin”.
Toh yace kana shi ya nufi hotel ɗin da Riyyam-nsra yake.
Shi kuma ya wuce campany.

Yana isa da mai a dai-dai-ta sahun ya tsaida shi bakin gate ya sallameshi.
Kana ya shiga cikin kamfanin.
Mai napep ya juya.

Kasan cewar duk ma'aikatan wurin sun san PA duk wanda yasan Dr Rayyern Mai-nasara zai iya saninshi da PA hakan yasa kai tsaye ya wuce Office ɗin sa.

Cikin gajiya ya ɗago kansa ya kalli ƙofar Office ɗin da ake bugawa cikin sauƙe numfashi gajiya yace.
"Yesss coming".
Cikin nitsuwa PA ya turo ƙofar.
Numfashi ya fesar tare da meda bayanshi ya jingina da kujera tare da kallon Usman murya can ƙasa yace.
"Sai yau?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Wlh kuwa sai yau fa".
Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin zama.
Sai kuma ya tsaya ganin uban gidan nasa ya miƙe tsaye.
Hannunshi yasa ya tattare system din ogan nashi da wayarshi kana yabi bayanshi dan tuni ya tafi.

Da sauri yabi bayanshi.
Bisa. libta ya hangoshi tanayin ƙasa dashi, da sassarfa ya mara mishi baya.

A haka har suka sauƙo hawa na biyu.

Suna sauƙa yayi maza yabi bayanshi ganin ya nufi hannun damanshi.

Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka isa wani wuri mai ɗauke da manya-manyan store's masu masifar girma da faɗin gaske.

Wanda sun kai goma sha biyu.

Gaba ɗaya a rufe suke tsayawa ya ɗanyi kana ya juyo ya kalli PA tare da cewa.
"Muje ƙasa".
To yace kana yabi bayanshi.
Suna sauƙa ƙasan kuma wasu stores ɗin suka samu kamar na sama.

Sai dai waɗannan su anata loda buhunan shinkafa shanshera ne buhu-buhu".
Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa kana suka sauƙo ƙasa gaba ɗaya.
Inda suka nufi can gefen baya wani ƙaton hall ɗin cike da enginer's anata kafasu da haɗasu babu ƙaƙƙautawa.
Cikin nitsuwa yace.
"Lokacin salla yayi abar aiki aje ayi sallan la'asar”.
To sukace cike da jin daɗin kana suka bar aiyukansu.
Kana suka firfito.

Shi kuwa yayi gaba PA ya mara masa baya.

Suna isa parking lot Usman ya buɗe mishi mota gefen baya.
Kai ya jujjuya mishi kana ya shiga gaba mazaunin driver'n kana ya nunawa Usman gefenshi.
Yana son yayi tuk’i da kansa ne dan sanin akwai masu bibiyarsa.

Ana buɗe musu gate ya fita a nitse.
Karatun ƙurani ya saki sautin muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa, (GARKUWA) Sassanyan sautinsa mai sauƙar da nitsuwa ya saki.
Kana ya saita hancin motar bisa titi ya fara takata a guje.
Dan so yake su samu jam'i sallan la'asar a Masallacin ƙofar gidansu.

Ana tada iƙama suna isowa.
Da sauri sukayi al'wala kana sukabi jam'i Allah yasa ba'a kere musuba.

Ana idar da sallan suka shiga cikin gida.
Tare da Abba da Baba Mauɗo, Hadi, Ari da Ramadan da Riyyam-nsra wanda suka juyo tare.

A bakin gate Usman ya zauna wurinsu Baba Mauɗo.

Su Ramadan kuwa a babban falon suka zauna.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara bayan Abbansu yabi har falonsu na ciki.
Gefenshi ya zauna tare da sauƙe numfashin gajiya kana ya kalli Abba dake cewa.
"Ya ka samu aiyu kan?”.
Cikin nitsuwa ya tonƙoshe sawunsa kana a hankali yace.
“Alhamdulillahi komai na tafiya dai-dai da izinin ubangiji.
Shinkafar nan ma da muka saya ta manoman Adamawa can wajajen Gurin ta iso, kuma shinkaface mai kyau da in ganci dan Jamila ce sai kuma mahanga kaɗan ita tafi kyau a barta a ɗaya.”

Uhumm yanzufa wasan zai fara daga PAGE din gobe.

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Chapter 35 · 0% Book details