Sashe 37
Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gidan Barrister Kabir kuwa.
Cikin tsoro Jannart ta kalli wayarta inda ta samu miss call 17.
13 daga ciki na Yah Junaid ne biyu na Daddy ɗaya kuma Salman ɗaya Hajia Rabi'ah.
Murya na rawa tace.
"My Aunty zan tafi kawai kinga har yanzu Abba bai dawoba ga Daddy ma nan yanata kirana ga kiran Yah Junaid goma sha".
Ganin yadda jikinta ke rawane yasa cikin sanyi tace.
“Toh gsky kam harda kiran Daddy kam kije, in ya dawo zaije yaji ko lfy".
Ledan da take miƙa mata ta amsa tare da cewa.
"Nah shiga uku kinga yanzuma ga Yah Junaid yana kira”.
Ta ƙare mgnar tana nufar woje, Dijat na biye da ita a baya.
Tana fita sakarkarun suka muƙe da sauri ta shiga mota jiki na rawa Baba Ado yaja jin yadda take ce mishi.
“Baba Ado mu tafi mu tafi, awa uku Daddy ya bani gashi har biyar nayi.”
Ajiyar zuciya Dijat ta sauƙe lokacin da suka fita.
Jiki a mace ta koma cikin gida.
Su kuwa a 360 suka nufi gidan.
Cike da Mamaki Usman yake kallon Dr Rayyern Mai-nasara daya fita cikin motar fuska a murtuƙe yacewa mai gadin.
"Ina Ubangidan naku?”.
Cike da mamaki mai gadin ya kalleshi kana ya juyo ya kalli ƙofar babban falon Alhaji idi Saleh Dakata wanda daga nan bakin gate ana iya hangoshi.
Baya buƙatan ƙarin bayani sabida yadda mai gadi yayi ya tabbatar masa ogan nasu na ciki.
Kana kuma ga tarin takalma alamun da mutane a cikin.
Cikin wani irin taku mai cike da haiba ya nufi falon.
Yana zuwa yasa yatsunshi biyu ya ɗan bugi ƙofar.
Da sauri duk suka juyo suka kalli ƙofar Junaidu dake baƙin kofarne yasa hannunshi ya buɗe dai-dai lokacin kuma shima ya turo ƙofar.
Ganin Dr Rayyern Mai-nasara na kutso kai cikin falon ne yasa Junaid matsowa tare da cewa.
"Kai lfy ina zaka je waye kai!?”.
Ya ƙare mgnar yana tsare gaban Dr Rayyern Mai-nasara din.
Wani irin kallon daya hautsina hanjin cikin Junaidu.
Rayyern ɗin ya watsa mishi, tare dasa hannunsa ya dafe gefen kafaɗun Junaid da yatsu biyu kana ya tureshi da ƙarfi, har saida ya bugi gini kana yace.
"Matsa yaro ba wurinka nazoba wurin tsohonka nazo”.
Ya ƙare mgnar yana nufan cikin falon gadan-gadan.
Wani irin kallon mamaki shakka mai haɗe da tsoro Alhaji idi Saleh Dakata, da Alhaji Abdu Tababa, da Dr Lukman suke mishi kamar idanunsa zasu faɗo ƙasa.
Da karfi ya jawo kujerar dake gefenshi kana yasa ƙafarshi ya tureta guuuu ta tafi har gaban Daddyn Jannart cikin rashin tsoro ya zauna bisa kujerar tare da jawota ya motso shi da kyau suna fuskantar juna cikin kakkausar murya yace.
"Meh hakan! Me kake nemana kana tura waɗan can karnu kan naka nemana, gani gabanka, ka gaya min me kake buƙatar inyi maka da kake sawa ana bibiyata.
Nace me kake son inyi maka!!!”.
Ya ƙare mgnar da masifar ƙarfi tare da buga santer table ɗin dake gabansa har saida cups ɗin saman suka kwanta suka gangara ƙasa.
Kana hakan yasa duk suka kame jikinsu da zazzaro idanunsu.
Da sauri Alhaji Idi Saleh Dakata ya ɗagawa Junaidu hannu dan ganin ya yunkuro zai kama Rayyern.
Shiru sukayi baki ɗayansu, shi kuwa Rayyern cikin tafasan zuciya yace.
“Da ka barshi ya isoni ai.”
Yayi mgnar yana tsare Daddy da idanu.
“Mitssssss”. Yaja wani dogon tsaki tare da cewa.
“Ina da aiki mai mahimmanci ka sani na baroshi nazo nan dan inji uzurinka sannan kayi shiru kana zaro min jajayen idanu kamar na (DUJI) to wlh hawainiyarka ta kiyayi Ramata.
Kada kasa in juyo kanka na wuni ɗaya wlh zaman kasar Kano zaifi karfinka.
Ya za'ayi ina girmama furfurarka kana kaucewa, to muddin baka kiyayeni ba tabbas zaka rasa gemun naka gaba ɗaya.”
Da sauri ya juyo ya watsawa Dr Lukman wani kallon da yasa shi jin zufa tun daka cikin naman jikinsa dan masifar tsoron da idanun Dr Rayyern Mai-nasara din ya bashi.
Cikin sauri yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
"Yaro man kaza lallai ka bimu a hankali dan wlh in kace zaka ja damu to wlh.
Ko na'urar jin bugun zuciya ka dena riƙewa.”
Wani irin gigitaccen tsawa ya dakawa Dr Lukman har saida ya miƙe tsaye dan firgita.
Da yatsa ya nuna shi kana ya jujjuyata sannan yace.
"Mu zuba Ni da kai magwaji ya gwada ya gani”.
Sai kuma ya kalli Alhaji Idi da Alhaji Abdu Tababa da suka zuro mayun idanunsu suka kafesa da ido suna masu nazarin wanne irin kisa ya kamata su yiwa yaron nan ne mai shegen taurin kai ko wani irin illa mafi muni za suyi masa rayuwarsa.
Cikin gargadi ya nunasu da yatsa kana yace.
"Wlh idan kuna cin ƙasa, to ku kiyayi ta curi.
ina mai tabbatar muku in baku kiyayeni ba zaku shiga uku.
Tun wuri ka gayawa waɗan can karnukan naka su dena bina, in kuwa ba hakaba zaka rubta rami.
Kada ku mance na gaya muku.
Idan nace zan taka mutun bashi da GARKUWA a kaina zan takashi domin tsakanina daku faɗane tsakanin gsky da ƙarya.”
Gaba ɗaya jikinsu tsuma yakeyi.
Yayinda Junaidu kuma zufar tsoro ta keto mishi.
Dai-dai lokacin kuma motocinsu Jannart suka shigo gidan.
Da sauri ya juya ya fita sabida hango sun da yayi kasan cewar ƙofar a buɗe take.
Yana isa wurin Jannart na fitowa kasan cewar ta bayanta yazo bata san ya isoba.
Wani ƙauuuuu taji lokacin daya yarfa mata wani irin masifeffen mari ta bayanta kuma kan kunneta.
Wani irin dummmm taji ya biyo bayan kauuu ɗin cikin gigita ta juyo...
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kabir ke tsaye gaban Dijat dake mishi bayanin abinda yasa Jannart ta tafi.
Ta kara da cewa.
"Ɗan Allah Abban Hafiz ka bita, kaga meke faruwa kada Junaidu ya mata wani abu”.
Cikin sauri Barrister Kabir yace.
"Zai matama maza ku koma ciki bari inje”.
Ya faɗi mgnar yana komawa cikin motarsa.
Ita kuma taja hannun Hafiza tayi gaba Hafiz na biye dasu a baya.
Shi kuwa Barrister Kabir cikin gudu yake tuƙib ya nufi gidan yayan nasa.
A gidansu Jannart kuwa.
A falon Daddy cikin wani irin masifeffen hatsala Dr Rayyern Mai-nasara ya juya zai fita.
Har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya kallesu kana yace.
"Wallahi Ni nan Muhammad Rayyern wargine dai-dai da ƙugun ko wanne mugun tsohon ɗan riba”.
Yana faɗin haka ya sako kai ya fito.
Dai-dai lokacin kuma Junaid yayiwa Jannart wani irin shaƙa mai ƙarfi kana ya wurgata ƙasa.
Hakan yasa ta saki wani irin raunataccen kuka mai masifar wahala tare da yunƙurawa ta kuma tasowa.
Tana mai yarfa hannun tare da ja baya gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Wani irin gigitaccen mari ya kuma zuba mata kan kunneta wanda yasa ta buga wani irin tsalle tare da ihun wahala a tare.
Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya iso parking lot ɗin.
Da sauri ya juyo ya kalli gefen da yaji ihun sabida karadin ihun ya cika masa kunne da ƙarfi har saida yaji kansa ya sara.
Siraran idanunshi ya zubawa fuskar yarinyar tabbas ya ganeta.
Kai ya rausayar ya juya tare da taɓe bakinsa alamun.
Oho yama kasheki in yaso kunfi kusa ai.
Barrister Kabir kuwa gudu yakeyi sosai sabida kiran Jannart da yayi har sau uku bata amsaba ya tabbatar masa ba lfy ba.
Shi kuwa Junaidu cikin tsananin mugunta da son huce haushinsa ya kuma shaƙo wuyanta.
Wanda yasata yin wani irin kakari tare da zazzaro idanunta woje.
*Dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki fitar min da littafina dan kin biya kudin karantawa bawai yana nufin kin mallakeshi bane, na roƙeki da isar zatin ubangiji daya bamu rai da lfy, don soyayyar manzon tsira dan mutuncin iyayenki kasa ki karantamin littafina in baki biyaba, tun forko kunsa littafina na kuɗine, kada ku tauye hakkina kuji tausayin maraicina*
Wanda kuma su Baba Ado da Ashiru mai gadi kab suka rumtse idanunsu da ƙarfi sabida ganin yana son kashe baiwar Allah.
Wani irin kallo Rayyern yayiwa Usman P.A dake cewa.
“Innalillahi zai kashe tafa".
“Toh me ruwanka ba gidansu ɗaya ba”.
Dr Rayyern ɗin ya fad’a,
Waɗannan ƙattin samudawan kuwa suma cirko-cirko sukayi to ya zasuyi.
Ɗan uwanta ne wa zai hanashi in ba mahaifinsu ba.
Su kuwa su Alhaji Abdu suna jin ihunta amman basu fitoba hakama Daddy.
Mom kuwa dake wonka sauri-sauri takeyi dan ta samu ta fito.
Abdul kuwa gefe ya tsaya yana zubda hawaye.
Wani irin gigitaccen duka fa Junaid ya fara yi mata tamkar zai ɗauke ranta.
P.A kam tuni shima hawayen tausayin yarinyar ya cika masa idanu.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara cikin yanayin halinsa na babu ruwansa da shiga harkar da bata shafeshi ba,
yayiwa motar key kana ya tada ya juya akalarta zuwa bakin gate.
Hon ya danna amman ina Ashiru mai gadi baima san yanayi ba.
Cikin jan tsaki ya kuma danna horn still Ashiru baima san yanayi ba.
Shi kuwa Junaid cikin huce haushinsa ya daddage ya yarfa mata wani irin marin.
Da yasa ta saki ihu da ƙarfi.
"Wayyo wayyo Allah na Wayyo Mom Wayyo Abba Yah Junaid zai kasheni Daddy”.
Bata ida rufe bakinta ba ya kuma zabga mata wani marin azabebben mari.
Wanda yasa jinin haɓo ɓallo mata ta hancinta.
Da k’arfi Dr Rayyern ya rumtse ƙwayar idanunsa, kana ya bud’esu a hankali.
Dai-dai lokacin kuma Abba ya iso bakin gate ɗin, ganin yanata dannan hon ba'a buɗe mishi bane yasashi.
Buɗe mota ya fito.yana fitowa yana jin ihunta.
Haka yasa ya kutsa kanshi da gudu cikin gidan ta ƙaramar kofar.
Dr Rayyern kuwa kashe motar yayi ganin ba'a buɗe mishi gate ba.
A hankali ya meda bayanshi ya jingina da jikin kujerar kana yasa hannunshi ya dafe saman marfin motar sabida yayi ƙasa da glasss ɗin.
Tallabe kanshi yayi da tafin hannunsa kana a hankali yace.
"Bari muga ƙarshen Game ɗinnan ko P.A”.
Cikin tausayi P.A yace.
"Sir zai kasheta fa”.
Ganin kallon da ya mishi da idanunsa da suka time zuwa launi jane ne kuma yasa yayi shiru.