← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 81

Sashe 33

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda already anriga da Anyi setling komai dake cikinsa, ank’awatasa da abubuwa masu kyau da burgewa Office din babbane mai yalwan kayan ƙawa.

Koda ya shiga cikin office din suit din dake jikinsa ya zare, tare da zama akan hamshakiyar kujerar da musamman take mallakinsa.

Wayarsa dake cikin al'jihunsa ya zaro.

Tare da kunnata kaitsaye ya saka numbern wannan motar da acikin kwana biyun take bibiyarsu.

Bayansa ya jingina da jikin kujeran, tare kuma da Dan lumshe Idanunsa.

“Road Safety.”

Ya fad’a cikin sanin makamar inda daya nufa.

*Jannart.*

Tsaye take agaban dressing mirror dinta, Wanda gabansa ke cike da tarin kayan kwalliya.
Yanayin yanda take sanye da towel ajikinta ne kuma, yake bayyana cewar fitowarta daga wanka kenan.

Atsanake take shafawa lallausan fatar jikinta mai, Yayinda zuciyarta ke cike da nishadi da kuma zumudin fitar da zatayi yau din.
Kasancewar tayi missing din gidan Abba Kabir din sosai.

Bayan ta gama shafa mai din ajikinta ne kuma, ta murza powder akan fuskarta, hade da gogawa red lips dinta shining lipgloss.
Sai kuma kajol da mascara da ta saka, Wanda suka kara fitar da kyaun fuskarta.
Batare kuma da ta sake goga wani abun akan fuskarta ba, ta k’arasa gaban wardrobe dinta,
Inda ta zaro wani had’add’en doguwar rigar material, wanda yasha dinkin fitted gown Wanda yana ɗaya daga cikin kayan da Barrister Kabir ke dinka mata, da Mom.

Koda ta sanya rigar ajikinta, kuwa ba karamin kyau yayi mata ba.

D’an kunnen gold marar nauyi tasa akunnenta, tare da daukan wani siririn mayafi ta yafa akanta.

Bayan ta zura half cover shoe akafarta ne kuma ta dauki wani baby hand bag Wanda yayi shige da kalan kayanta ta rik’e

Agogon dake sak’ale ajikin Bangon dakin ta kalla, ganin da tayi kuma lokaci na tafiya ne, yasa agurguje ta dauki wayarta ta fice daga cikin dakin.

Koda ta sauk’o afalon k’asa ta samu Momy.

Ganin yanda Jannart din tayi kyaune kuma yasa Momyn sakin murmushi, cikin nuna kulawa tace.

“A'a Jannart yau wacce rana ansaka kayan hausawa.”

Murmushi Jannart din tayi, tare da karasowa inda Momyn ke zaune, ashagwab’e tace.

“Momy kayan baimin kyau ba ko?.”

Dariya Momyn tayi had’e da cewa.

“Ya miki kyau mana sosai Jannart, ai yama fi miki kyau akan kowanni kaya.”

Murmushin daya bayyana fararen hakwaranta tayi, cikin yanayin dake bayyana jin dadinta tace.

“Nagode sosae Momy na, in sha Allah zan koyi saka irinsu.”

Cikin jin daɗi Mom tace.
"Kai Alhamdulillah da naji daɗi haka kuwa Boɗɗo na".

Sassanyan murmushi tayi tare da lumshe idonta kana tace.
“bari naje saina dawo.”

Kai Momyn ta jinjina tare da cewa tagaishe da Abba Kabir din da kuma matarsa, da yaransa.

Da “to.” Jannart din ta amsa, kana tasa kai ta fice daga cikin falon.

Tana fitowa compound din gidan kuwa ta samu Baba Ado driver da guard dinta na jiran ta.

Domin tuntuni Daddy da kansa ya Gaya musu cewa Jannart din zata fita.
Yayinda kuma ya jaddada musu kulawa da ita.

Kamar Koda yaushe kuma tana shiga cikin mota, guard din nata ma suka shishshiga cikin tasu motar, tare da rufawa motar da Jannart din ke ciki baya.

Jin da tayi sunhau titi ne kuma yasa ta d’an jingina bayanta da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunta.

Ahankali take sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda ayau din takejin kanta tamkar sakakkiyar tsuntsuwa.

Lallai watarana tana fata da burin samun yancin kanta, watarana tana fatan yin yawonta ita kad’ai batare da wani ko wata sun bibiyeta ba, haka kuma watarana tana fatan sauyawar rayuwarta gaba d’aya.

Yayinda kuma har acikin zuciyarta watarana take fata dason sanin kullin dake ƙule Cikin rayuwarta kamar yadda Barrister Kabir yasha faɗa mata.

Shin Meyasa Daddy’nta ya sanya mata tsaro maitsanani har haka duk da kuwa tana gamsuwa da irin soyayyar da yake nuna mata, ɗari bisa ɗari.

Meyasa Yah Junaid ke bibiyanta da munanan halaye? Da mugun manufa.

Yaushe ne canji zaizo cikin rayuwarta? Yaushe ne zatayi farinciki kamar kowa? Yaushe zataji kanta amatsayin Mace mai y’anci?

Lallai watarana zuciyarta kan gaya mata cewa Sauyin rayuwa zaizo.

Sai-dai yaushe zaizo? Da wani dalili zai taho a wanne yanayin duk bata sani ba.

Wani irin numfashi mai dumi ta fesar, adai-dai lokacin kuwa suka iso kofar madaidacin gidan Barrister Kabeer dake nan Nassarawa G.R.A

Wanda kuma isowarsu gidan yayi dai-dai da shigowar sak’o cikin wayarta.

Jin alaman shigowan Sakon da tayi ne kuma yasa ta d’ago wayartata ta duba.

Ganin sakon da aka rubuta mata dinne kuma yasa ta.
Jin wani irin bugun zuciya maitsanani.

Idanunta ta rumtse da k’arfi, cikin kuma muryarta da ke bayyana tsoro had’i da firgici Ta......

*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya saya ba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota akai miki state ɗin da kike, Duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune TA *D.H.L Office*🤝🏻cikin mako ɗaya kayanki zai isa duk ƙasar da kike, sai dai akwai ɗan tsada cajinki da zasuyi
sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 14
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE NE*

*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta dan Allah special Group 1k ne karamin group 500 bane kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na 09097853276*

Ta buɗe idonta ganin sunan Yah Junaid na bisa screen ɗin wayarta ne yasa, ta fidda numfashin a hankali tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna'ilaihi rajiun Yah Junaid Kuma?”.
Cikin tsoro ta buɗe text ɗin dai-dai lokacin kuma mai gadin gidan Barrister Kabir ɗin ya buɗe musu gate.
Suka kutsa ciki.
"Dan ubanki ina kiranki bazaki amsa ba.
Maza ki ɗaga ko in ɓaɓɓllaki in mun haɗu".
Cikin ƙarfin hali ta zuge zip ɗin Baby hand bang din ta cilla wayar kana ta zuge ta rufe.

Da sauri Aunty Dijat tace.
"Lah Hafiz ga Aunty Jannart tazo".
Ta ƙare mgnar tana nufar inda motarsu Jannart tayi parking.
Hafiz kuwa da sauri ya juyo jin ance Jannart, cikin ware ido ya nufi motarsu a guje yana cewa.
"Oyoyo my Aunty, Hafiza ga Aunty Jannart tazo".

Murmushi mai cike da jin daɗi Jannart tayi kana ta ƙarisa fitowa tare da ware musu hannayenta.
A guje suka abka jikinta su duka biyu.

Cikin jin daɗi da son yaran ta ɗaga Hafiza da bazata wuce 7 year's ba.

Ruggume ta sukayi duka suna farin cikin ganinta.
Cikin kula, so, ƙauna, da tausayawa Aunty Dijat ta iso garesu fuska ɗauke da murmushi tace.
“Oyoyo Aunty Jannart, yau munji daɗin mu kin tunomo”.
Cike da happy tace.
"My Aunty kullum kuna raina".
Hannu tasa ta amshi Hafiza tare da cewa.
"Zo nan kada ki karya min ƴata maza mu shiga daga ciki."
Aifa tana faɗin haka Hafiz ya ɗiba a guje yayi cikin gida.
Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta kalli Baba Ado dake gaisawa da Aunty Dijat.

Ita kuwa Aunty Dijat kamo hannun Jannart tayi suka juya suka nufi cikin gida.
Cikin murmushi ta juyo ta kalli Baba Ado dake cewa.
"Jannart muje ne ko mu jiraki".
“A'a Baba Ado ku jirani Awa uku Daddy ya bani".
Kai ya jinjina mata, kana ya koma wurin mai gadin gidan.
Su Sunday Kuma suka tsaya tamkar gumakan taɓo.

Daga bakin falon Hafiz keta rabkawa Barrister Kabir kira.
"Abba! Abba!! Kazo ga Aunty Jannart tazo".

Da sauri Ya miƙe tsaye, tare da katse wayan da yakeyi wanda kuma dama akan wani case ne da zasu shiga gobe,
Cike da farin ciki ya fara tako steps ɗin sauƙowa men falon su.

Ita kuwa Jannart Murmushin jin daɗi takeyi wanda ke bayyana tsantsan jin daɗin da take ciki.
Ita kuwa Aunty Dijat kitchen ta nufa.
Chapter 33 · 0% Book details