← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 81

Sashe 62

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin wani kallon da Abban ya watsa masa ne yasa shi yin shiru, tare da sunkuyar da kansa k’asa, asanyaye yace.

“Abba yanzu ba kudi ajikina, a daga auren sai na samu kudin.”
Cike da mmkin mgnar tasa Abba yace.
“Eh munsani fa baka da kuɗi.
Amman kada ka damu ko transfer ne kayi mana.”

Saurin dagowa yayi ya kalli Abban nasa, lokaci daya kuma ya kwab’e fuska, Murya araunace yace.

“Ni wayata ba charge, amma muje sama da Ramadan dakina in bashi kuɗin ya kawo muku.”
Ya ƙare mgnar yana yunƙurin tashi.
Alamun guduwa da yake son yi.
Murmushi ɓoye Abba yayi tare da danne kafaɗarsa kana yace.
“Zauna”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Abba Kudin zan bashi”.

Ya k’are maganar tamkar zai zubda hawaye.
Cikin tsare fuska yace.
“Ina kuɗin suke?”.
A sanyaye yace.
“Cikin bed side drower”.

Kallon Ramadan Abba yayi kana cikin, bada umarni yace.

“Ramadan jeka ɗebo kudin koma nawane kawosu.”

“To“ Ramadan din yace, tare da mikewa cikin sauri ya haura sama.

Inda Rayyern kuwa ya bishi da Harara kasa kasa.

Mintuna biyu kacal kuma saiga Ramadan ya dawo da bandir din yan dubu dubu, na dubu dari biyu, Dan kowani bandir dubu dari ne.

Mik’awa Abban nasu yayi.
Tare da komawa ya zauna.

Abba kuwa duka dubu dari biyun din ya mik’awa, Dr Sajo tare da cewa.

“Ni Alhaji Bashir Muhammad ina nemawa, d’ana Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yar wajenka Jannart Idi Sale Dakata, akan sadaki naira dubu dari biyu.”

Karb’an kudin Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa cikin mutumtawa yace.

“Ni Dr Sajo Umar, na bawa danka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yata Jannart Abdulkarim Saleh Dakata akan sadaki naira dubu d’ari biyu.”
Daga nan kuma sukayi duk abinda ya dace na tsarin daurin aure bisa koyarwar musulunci.

“Alhamdulillah! Alhamdoulillah!! AURE Ya D’auru jama’a muyi salati goma ga Annabi.”

Cewar Baba Maud’o, cikin tsananin farinciki.

Adai-dai lokacin kuwa Rayyern ya rumtse idanunsa da karfi, tare da dafe dai-dai saitin zuciyarsa cikin rudu hadi da bugawar zuciya Ya......!

*Dan Allah ki saya ki karanta littafina na kuɗine special Group 1k ƙaramin group 500 yawan posting ne banbancinsu, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in ba halin turawa ta account ki sayi katin MTN ki kofi number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp.*

By

*GARKUWAR FULANI*

Danne jajayen labb’ansa.
“Innalillah wa innailaihi rajiun.
Oh ni Rayyern wannan wacce irin rayuwace? Wannan wanne irin ƙaddara ne mai tafe da jarababbe .ayataccen kuma lik’akk’en aure ne, shikenan dai ni.
Bani da freedom din kaina, dolen-dole sai an sako min wata acikin rayuwata!!!.”
Yayi maganar azuciyarsa, yana mejin tamkar ya mike tsaye, yace sam shi baiyarda da wannan auren ba.

Su Abba, Ramadan, da kuma Riyyam-nsra, kuwa gaba d’aya farinciki ne ya lullub’e zuciyoyinsu, more especially Ramadan da ayanzu yake Ganin shima ya samu chance na auren Rayhanna’n sa.

Baya ga haka kuma abun farinciki ne awajensu ace yau Hamma Rayyern din nasu yayi aure.

Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe tare da soma sauke ajiyar zuciya akai akai, Lallai yasan cewa yau din ya bawa Jannart Garkuwa, da kuma mafakar da babu wani mahaluki daya isa ketare ta, Allah Sarki Jannart marainiyar Allah, akullum Allah shike zama gatanta.

Dr. Sajo ne ya gyara zama, tare da somayin addu’a, bayan ya kammala addu’an ne kuma yace.

“Ina rokon Allah madaukakin sarki daya sanya al'barka da kuma al'khairi mai tarin yawa acikin wannan auren, Allah ya kade duk wata fitina da zata kunno Kai, Kai kuma Rayyern Allah Ubangiji ya baka ikon sauke nauyi da kuma hakkin dake kanka.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa amma banda Rayyern wanda yakejin kamar yasa musu kuka, Dan takaici, Yayinda acikin zuciyarsa kuwa yace.

“Ni babu wani nauyi daya hau kaina.”

Barrister Kabir ne kuma ya d’an kallesu, kana. Cikin taushin murya yace.

“Nagode Kwarai da irin karamcin da kukayi mana, kun amince damu, sannan kuma kun karb’i auren y’armu da daraja, nagode Kwarai abu na karshe kuma da zan rokeku dukanku shine, Dan Allah wannan magana ta daurin auren ya zama sirri atsakaninmu, Domin nima dole ce ta sani yin hakan.”

Kai duk suka jinjina, Yayinda Abba Kuwa ya gyara zamansa tare da fuskantar Barrister Kabir din yace.

“Karka damu Barrister, nayi maka al'k’awarin bayan mu babu wani wanda zaisan da batun auren, haka kuma babu wanda zaisan da zaman Jannart acikin gidannan.”

Kai Barrister’n ya jinjina cike da gamsuwa, Yayinda Abban kuwa ya dawo da kallonsa gasu Ramadan din, cikin tsare gida yace.

“Dukanku ku tashi ku bamu waje.”

Aikuwa Rayyern kam dama kaman jiran hakan yakeyi, Domin bakin Abban ko gama rufewa baiyi ba ya mik’e zumbur, Da sauri Abba ya kalleshi har ya buɗe baki zaice banda kai.
Sai kuma kawai yayi shiru ya bishi da ido har ya haura sama.

Ramadan kuwa hannun Riyyam-nsra ya kama, suka nufi side d’insa, Tabbas suna cikin farinciki, amma daga wani b’angare tsananin mamakin yanda auren Hamman nasu ya kasance sukeyi, auren bazata, auren da ba tsammani kuma auren sirri auren shaidu goma.

Suna shiga cikin side din Ramadan din ne kuma, Riyyam-nsra ya zaro wayarsa, Yayinda shi kuwa Ramadan kaitsaye ya wuce toilet.

Riyyam kuwa numbern Mammynsa ya kira, bugu biyu kuwa ta d’auka, bayan sun gaisa ne kuma Riyyam din, ya dan jujjuya ya kalli kofar shigowa data Bathroom, tare da karyar da wuyansa gefe, bakinsa cike da tarin maganganu kala-kala yace.

“Mammy kinsan me yake faruwa?”.
Da sauri Mammy ta jujjuya mishi kai tare da cewa.
“A'a sai ka faɗa!”.
Numfashi ya ɗan fesar kana a hankali yace.
“Yau ɗinnan a yanzun nan aka d’aurawa Hamma Rayyern aure.”

Idanu Mammyn ta d’an zaro cike da tarin mamaki, tace.

“Aure kuma Riyyam, wanne irin aure haka?.”
Gyara zamanshi yayi tare da sauke nannauyan numfashin yace.
“Aure dai da kika sani Mammy irin dai wanda ake daurwa tsakanin mata da miji”.
Lumshe ido tayi cike da al'hini tace.
“Ikon Allah”.
Shi kuwa Riyyam-nsra ci gaba da cewa yayi.
“Mammy kinsan meye ma kuwa? acikin falo fa aka daura auren, kuma kwata-kwata bamu wuce mu goma ba, wa y’anda aka daura auren agabanmu”.
Da sauri tace.
“Toh wannan wanne irin aurene meke ɓoye a ƙasa, tabbas akwai manufar auren!”.
Da sauri yace.
“Uhumm ai baki sani, bama Mammy Hamma Rayyern fa bayason auren wallahi Mammy, karki ga yanda ya had’e fuska, kamar zai daki babu.
Domin shi kanshi baisan cewa za’a d’aura masa aure yau ba.”

Ajiyar zuciya Mammy’n ta sauke, cikin yanayin mamaki kuma tace.

“To Riyyam Allah Ubangiji yasan hakan shine mafi al'khairi, ya kuma basu zaman lafiya yasa kuma wani matakin nasara ne.”

“Ameen.” Ya fad’a, Ganin fitowar Ramadan daga cikin toilet ne kuma, yasa shi katse kiran, inda yacewa Mammyn nasa zai kirata anjima.

Acan falon Abba kuwa tafiyar su Rayyern dinne, yasa Usman P.A, Hadi da kuma Ari mikewa duk suka fice daga cikin falon, suna mai fadin Allah ya sanya alkhairi acikin auren.

Baba Maud’o kuwa Kallon su Barrister Kabir yayi, cikin muryar dake bayyana farin cikinsa, yace.

“Barrister mun gode da kyauta mai daraja.
Yanzu yaushe ne za’a je d’auko mana diyar tamu.”

Gyara zama Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutumtawa yace.

“Insha Allah ni dakaina zan kawo muku diyar ku, bama sai kunje d’auko ta ba.
Domin kamar yanda aka daura auren nan, asirrance haka kawo amaryar ma zai kasance asirrance, saboda nima acikin hikima zan samu na fita da ita daga cikin gidan da yake gab da zame mata kabari, bisa taimakon maigadin gidan, da kuma driver’nta, saboda mun shirya akan da misalin k’arfe sha d’aya zata fito daga gidan, Idan ta fito ni kuma zan dauketa na kawota.”

Kai duk suka jinjina, Yayinda Baba Maud’o kuwa yayi murmushi, tare da cewa.

“Masha Allah hakan ma yayi, Allah Ubangiji ya taimaka.” Da “Ameen” duk suka amsa.

Batare daya sake cewa komai ba, kuma ya tashi ya tafi.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, yana haurawa sama, babbar rigar dake jikinsa ya zare, tare da hayewa saman gadonsa ya kwanta.

Idanunsa da sukayi ja, ya rumtse da karfi tare kuma da soma fitar da wani irin numfashi mai zafi ta bakinsa.

Shikam acikin rai da zuciyarsa ya rasa wannan wanni irin fitinannen aure ne da aka lik’a masa, gaba daya suna neman dagula masa rayuwarsa, wanda bai kuma San dalilin yin hakan ba, dududu acikin kwanaki goma da dawowarsa daga Ethiopia, acikin kwanaki takwas na cikin gomanne kuma, abubuwa mabanbanta suka faru dashi, aciki kuwa harda babban abu daya kasance Aure.
Auren da bai shirya masa ba, auren da yazo da wani irin k’ulli.
Sam arayuwarsa shi bai tab’a kawo tunani ko maganar aure cikin k’wak’walwarsa ba.
Fact Shi baima tab’aji ajikinsa cewar zaiyi aure ba.

But why yanzu suke son sanja masa rayuwa?

Yar karamar tsuka yaja, tare da gyara kwanciyarsa, cikin takaici kuma abayyane yace.

“Koma meye nidai bazan sanja tsarin rayuwata daga yanda na saba ba, babu wata mace agabana, haka kuma babu wata wanda zan tsaya kulawa da ita ehe inji da kaina ma mana.”

Ya kare maganan yana me jawo murfin bedside drawer’nsa, inda ya d’auko ledan chocolate d’insa na kinder bueno, bayan ya bare ledanne kuma yasa chocolate din abakinsa yana sha.

Acan falon kasa kuwa, su Abban suna gama tattaunawa ne, Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo suka mik’e Daniyar tafiya, har bakin mota kuwa Abba ya rakasu.

Bayan yaga tafiyarsu ne kuma ya dawo gida, kaitsaye kuma dakin Mamy ya nufa, Dan sanar da ita abunda ke wakana.

*Jannart*

Zaune take akan lallausan carpet dake, cikin falon nasu, Yayinda ta duk’ar da kanta k’asa, nail cutter ne hannunta, tana gyara yan fara tun yatsun kafarta, Yayinda Momy da kuma Abdull ke zaune agefe.

Azahirance Idan ka kalleta zakayi tunanin, cewa hankalinta ya tafi ne Izuwa kan nails dinta da take gyarawa, saidai kuma awajenta sam ba hakan bane.
Domin tunaninta ya tafine izuwa wani waje na daban, wani abu takeji na musamman yau din, Domin kuwa abubuwa uku ne suka hade acikin rai da zuciyarta, Wanda kuma batasan dalilin jin hakan da takeyi ba.
Chapter 62 · 0% Book details