← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 81

Sashe 49

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya d’an fesar, kana Ahankali ya d’ago Kai ya kalli Mamyn, wacce har yanzu takeyi masa Kallon mamaki.

K’asa-k’asa yayi da muryarsa, yadda yasan koda akwai wani adakin To bazai tab’a iya juyo abunda yake fad’a ba, sai ita d’in kawai.

“Kiyi k’asa-k’asa da muryarki Ruk’ayya, kinsan komai babu wani abunda baki sani ba, Dama ce ta samu, hakika naji ajikina cewar komai yana gab da had’uwa waje d’aya, da yardar Allah abubuwa suna ta had’uwa waje d’aya.”

Idanu Mamyn ta zuba masa cike da d’an d’aurewar kai, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace.

“Har yanzu bangane abunda kake nufi ba, meke shirin faruwa ne?”

Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e tare da sake rik’o hannunta da kyau.

Again kuma Cikin yin k’asa da murya yace.

“Kintuna Barrister Abdulkarim Saleh Dakata?”

Kai Mamyn ta jinjina, cikin sauri kuma tace.

“Natuna shi mana, har abada kuma bazan manta shiba.”

Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, yace.

“To wannan bak’on da yazo wajena k’aninsa ne, shima kuma Barrister ne, sunansa Barrister Kabir Saleh Dakata.”

Idanu Mamyn tad’an zaro cike da tsananin mamaki, tace.

“Ikon Allah, Allah mai iko, mai kumayin duk yanda yaso, Lallai Tabbas kuwa na amincewa maganarka, Nesa na matsowa kusa, kuma haske zai bayyana Insha Allah.”

“Insha Allah kuwa.”
Abba ya maimaita cike da k’warin guiwa.

Acan b’angaren Rayyern kuwa...!

*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

By
*GARKUWAR FULANI*

In Sha Allah kuwa.
Abban ya maimaita cike da k’warin guiwa.

Acan b’angaren Rayyern kuwa, koda ya koma part d’insa, gaba daya kasa zaune yayi, Domin kuwa abubuwa da yawa ne keyi masa yawo acikin tunaninsa.

Direct kuma saman balcony d’insa ya koma, yana nan tsaye ne kuma yaga Barrister Kabir din ya fito.

Hakan yasa cikin sauri ya juya, tare da nufan falon k’asan nasu kaitsaye.

Koda ya fito falon, rashin Ganin Abba acikin falon Yayi masa dadi, wanda kuma hakanne ya bashi daman nufan waje kaitsaye.

Fitowarsa compound din gidan, kuwa yayi dai-dai da mik’awa Baba Maud’o hannu da Barrister Kabir din yayi.

Cikin aminci suka sake gaisawa, inda Baba Maud’o yace.

“Masha Allah har kafito zaka tafi, To mungode sosai a gaida gida.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa.

“Nima Nagode Baba.”

Dai-dai ya juya zai shiga cikin motarsa ne kuma, Rayyern ya k’araso wajen.

Kallon-kallo suka danyi da Barrister Kabir din, Yayinda Barrister Kabir din ke kallonsa cikin sakin fuska.

Shikuwa Rayyern yaken dole yayi, kana anutse yace.

“Har zaka tafi?”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina masa alaman.

“Eh.”

Shikuwa Rayyern kaitsaye bud’e murfin motar yayi, b’angaren mai zaman banza ya shiga ya zauna.

Ganin hakanne kuma yasa Barrister Kabir yin murmushi, tare da bud’e murfin motar shima ya shiga ya zauna.
saboda Lallai yasan cewa akwai magana.

Yana zama kuwa Rayyern ya fuskancesa.

Cikin muryar dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.

“Bansan me kake nufi ba, Bansan me kake nema da rayuwata ba, Bansan wani k’ulline kuke nufina dashi, kaida y’an uwanka da kuma abokan kasuwancinka akaina ba, inayiwa fuskarka kyakkyawan gani , da kuma kyakkyawan zato, amma why zakayi min haka? kayi min bayanin yarinyar, kuma na saka baki anbata taimakon daya kama ta a Hospital dina? To yanzu kuma me kuke nema awaje na? Meyasa dole saini zaku zab’a mainayi muku? Ina da yakinin Akwai dubbannin mutanen, da zasu iya taimaka muku akan matsalarku, bawai dole sai lallai niba, To Meyasa kuke son takuramin? Meyasa kuke bibiyata? Meyasa zaka zo da wannan maganan mai kama da tatsuniya? Wanda ko’a labarai ko a fina finai babu irin wannan al’amarin, ni nakan cire kaina acikin duk wani abu danasan babu ruwana, Meyasa kukeson sakani acikin abunda baidace dani ba??”.

Juyowa Barrister Kabir din yayi, ya kalli Rayyern d’in.
Domin kuwa acikin kalaman da yaji sun fito daga bakinsa babu wanda bai fahimta ba ya fahimci Rayyern yanayi musu kuɗin goro shi dasu Alhaji Idi Saleh Dakata dasu Dr Lukman da Abdu Tababa.

Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke tare kuma da kamo hannun Rayyern d’in, cikin fuskantar juna yace.

“Rayyern! Rayyern ka yarda dani, Rayyern ka aminta dani, bazan tab’a cutar dakai ba har abada, wallahi babu cutarwa tsakanina da kai, saidai ina tsananin neman taimakon ka, Ina neman taimakonka.
Dan tsiratar da ran Jannart, Jannart marainiya ce, Dr. Rayyern ba zaka gane halin da nake ciki ba, ba ni kuma da isashshen lokacin da zanyi maka bayanin da zaka fahimceni, fatana ayanzu shine Jannart ta kasance ak’ark’ashin inuwarka, ba naso asan ma tana tare dakai, Domin Kuwa auren da zakayi da ita, Aurene na sirri, haka kuma aure ne da zai zamo auren manufa, Dan Allah Rayyern ka amincewa buk’atata, ko badan niba Kodan maraicin Jannart..”

*”Manufa? Auren manufa Wanne irin manufa kenan?”*

Rayyern din ya tambaya, yana me tsare Barrister Kabir da ido.

“Manufa saboda ceto Rayuwarta, da kuma manufar fidda gaskiyar da take b’oye tsawon shekaru ashirin da biyu.”

Idanu Rayyern din ya lumshe, akaron farko cikin kuma halin ko inkula yace.

“To ni meye had’ina da wannan? Meya shafeni da hakan?”

Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e.

Kana cikin sanyi yace.

“Baka da had’i dashi, amma kuma abad’inance kana da had’i dashi, Domin idan kataimaketa Allah Zaibaka lada, kuma kayi taimakon musulunci.”

Barrister Kabir din ya fada idanunsa na ciko da k’walla.

Lips d’insa ya cije, tare da sake rumtse idanunsa, cikin yanayin dake nuna Kosawa da da maganan yace.

“Har dai yanzu bangane inda komai suka dosa ba.”

Still ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sake saukewa, kana ahankali yace.

“Nidai fatana shine ka amince, Idan ka amince ninasan yanda zan gudanar da komai.”

Kai Rayyern din ya girgiza Cikin kuma rashin gamsuwa, da abunda Barrister Kabir din ke fad’a yace.

“Wannan tatsuniya ne, ko kuma nace mafarkin da bazai kammala ba har gaban abadan, well yanzu me kaje ka fad’awa mahaifina mai kuka tattauna dashi?.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi.
Kana yace.

“Idan ka tambayeshi duk zai gaya maka na tabbatar da hakan.”

Kafad’ansa yad’an d’age, batare kuma daya sake yiwa Barrister Kabir din wata, tambaya ba ya bud’e murfin motar ya fice.

Hakanne kuma yasa Barrister Kabir sakin murmushi, tare da dan juyawa yana kallonsa.

Harsaida Rayyern din ya b’a cewa ganinsa, kafun ya yiwa motar key kaitsaye ya fice daga cikin gidan.

Rayyern kuwa kaitsaye part d’insa ya koma, gudun kada wasu banzayen tunanin abunda basu da muhimmanci arayuwarsa su dameshi ne kuma yasa shi, daukan laptop d’insa ya soma shigar da wasu bayanai.

Acan b’angaren Barrister Kabir kuwa, zuciyarsa cike da tsananin farinciki ya Baro gidan su Rayyern din.

Koda ya isa inda zaije kuwa ansoma kiraye kirayen sallan la’asar, bayan yayi sallan ne kuma ya ci gaba da sabgoginsa.

Yayinda acan b’angaren Jannart kuwa, yau din kusan wuni tayi tana bacci, kasancewar acikin magungunan da aka bata a asibitin Mai-nasara’n, akwai way’anda suke sa bacci sosai, babu laifi kuma tana samun kulawa mai kyau, daga wajen Momy da kuma k’aninta Abdull.

10:00 pm

Aunty Dijat ne wacce Tasha wanka cikin night gown, ta turo kofar dakin mijinnata, Ahankali Yayinda bakinta ke dauke da sallama.

Saidai kuma ganin abunda mijin nata keyi ne, yasa taja ta tsaya tare da kura masa ido.

Domin kuwa shigowarta cikin dakin, yayi dai-dai da dirowar Barrister Kabir din k’asa, wanda kuma fitowarsa daga cikin silin kenan.

Idanu Aunty Dijat din ta d’an zaro, cikin kuma yanayin mamaki tace.

“Barrister, yana ganka haka cikin silin fa ka shiga?”

Kansa ya jinjina mata alaman Eh.
Batare kuma daya motsa bakinsa ba, ya koma ya zauna, tare da baje tarin takardun dake hannunsa ak’asa, wanda duk sukayi kura ya soma kad’ewa.

Ganin hakanne kuma yasa Aunty Dijat din cewa.

“Barrister lafiya kuwa, way’annan tarin tsofin takardun duk na meye?”

Juyowa yayi ya kalleta, cikin kuma son samun nutsuwa yace.
Chapter 49 · 0% Book details