Sashe 50
Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Dijat dan Allah kid’an hakurtamin, Domin ayanzu bani da amsar da zan baki, bincikene akan abunda ya shafi aikina, please kije anjima zanne meki, yanzu Idan kika tsaya zaki iya disturbing dina.”
Ya fad’i hakan yana me Dan tausasa muryarsa.
Aunty Dijat kuwa sanin irin yanayin aikin nasa ne yasa batare da ta musa masa ba, ta juya ta fice daga cikin dakin, saboda tasan watarana Idan tension din aiki Yayi masa yawa, To kwata kwata bayason damuwa.
Shikuwa Barrister Kabir Ganin Dijat din tatafi ne, yasa shi soma bubbud’e takardun dake zube agabansa.
Yayinda kowacce takarda Idan ya bud’e, sunan Barrister Abdulkarim Saleh Dakata ne ke bayyana, da kuma sa hannunsa.
Yayinda acan gefe guda kuwa, kan wani file me kaman document aka yi rubutu da manyan bak’i.
*”Bashir Muhammad Mai-Gaskiya”* shine abunda ke rubuce ajikin file din.
Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya shiga saukewa akai akai, Yayinda kuma yake ci gaba da kimtsa takardun awaje daya.
Saida hakan kuwa ya d’aukesa kaman tsawon 30mn kafun ya kammala.
Kana anutse yasake maida takardun inda ya d’auko su, ma’ana cikin mab’oyansu na musamman.
Acikin zuciyarsa kuwa wani irin k’warain guiwa yakeji, tare da sake yiwa Allah Godiya, saboda ayanzu yasan kowanni shaida yana hannunsa.
Bayan kuma ya kimtsa wajenne, ya shige toilet kaitsaye alwala ya dauro, bayan ya fito ne kuma ya shumfud’a sallaya, tare da tada sallah ya d’anyi nafilfilu, hade da sake godemawa Allah.
Koda ya idar da sallan hannayensa ya d’aga sama.
Kana cikin aminci yace.
“Alhamdulillah Allah Nagode ma, daka bani Aron raida lafiya, har kuma ka kawoni tsawon wannan lokacin, da ake gab da samun nasara akan Jannart, da kuma ida bunne duk wata hujja, kuma ya Allah kataimakeni kabani sa’a, in tono duk wata hujja na bayyanata, gaskiya tayi halin ta..”
Shafa addu’ar tasa yayi, bayan wasu yan mintuna ne kuma ya tashi kaitsaye ya nufi dakin Dijat d’insa.
*Washegari*
Tuesday.
Jannart 8 am dai-dai ta bud’e Idanunta Ahankali, tare kuma da tashi ta mike zaune.
Tabbas taji karfin jikinta sosai yau din, tasan kuma hakan bai rasa nasaba da magungunan da Tasha.
Cikin kuzarin data dan samune kuma ta mik’e tare da fad’awa bathroom tayi wanka.
Koda ta fito, mai kawai ta shafa, batare da ko powder ta kuma mutstsukawa fuskarta ba, ta bud’e drawer dinta, hade da zaro wata Brown din jallabiya na mata, mai kyau da Tsushi ta zura ajikinta.
Sosai kuwa rigar tayi mata d’as ajikinta.
Normal perfume din da ta saba shafawa, ta shafa ajikinta, batare kuma da ta tsaya wani jikiri ba, ta d’auki wayarta kaitsaye ta fice daga cikin dakin.
Direct falon k’asa ta nufa.
Koda ta karasa cikin falon, Momy da Abdull kawai ta samu akan dining table suna breakfast.
Ganinta ne kuma yasa dukansu sakin murmushi.
Inda Cikin tsananin kulawa Momy tace.
“Masha Allah Jannart tayi sauk’i, Alhamdulillah hinyau Lallai kinji karfin jikinki.”
Murmushi Jannart din tayi, adai-dai lokacin da ta karaso dining table dinne kuma tace.
“Good morning Momy, Alhamdulillah naji sauki sosai.”
“Alhamdulillah ai haka akeso, dazu na shiga ai naga kina bacci shiyasa kawai ban tasheki ba, amma tunda kintashi yanzu zoki zauna kici abinci.”
Momyn ta fad’a cikin kulawa.
Abdull kuwa Kallon yayartasa yayi, kana fuskarsa dauke da murmushi yace.
“Sannu Aunty Jannart ya jikin naki, Ina fatan ace yanzu kin gama warkewa har tsere zaki iyayi.”
Dariya duk sukayi Yayinda Jannart din tace.
“Momy Daddy fa?.”
Ajiyar zuciya Momyn ta sauke, kafun daga bisani tace.
“Yau ai Daddynku tun sassafe ya fita, yace yana da ayyuka sosai.”
Kai kawai Jannart din ta jinjina, batare kuma da ta sake cewa komai ba, ta soma cin soyayyen chips and ketchup din da Momy ta saka mata, hadi kuma da fruit salad.
Bayan sun dan tab’a hira ne kuma, Abdull ya mik’e ya tafi makaranta, saboda yau din yana da lecture 10 am.
Itakuwa Jannart falo ta dawo ta zauna, tana falonne kuma Aisha Lawal da kuma Salman suka zo duba ta.
Har cikin falon kuwa ta shigo dasu, sosai kuma zuwan nasu ya debe Mata kewa, Yayinda Momy kuwa tayi musu tarba ta mutumci.
Ita dai Jannart kam yau tana cikin farinciki, saboda har yau Junaid enemy dinta baidawo gidan ba.
Acikin hirar tasu dasu Aisha Lawal dinne kuma, take tambayar Salman, ko wannan mutumin ya kirasa.
Numfashi Salman din yadan fesar, kana Cikin son kwantar mata da hankali yace.
“Har yanzun dai baikirani ba, amma nasan zai kira Insha Allah, karki damu ai daganinsa yasan muhimmancin alkawari, kuma ko yanzu ma da zamu taho saida muka biya wajen wasan polo’n, nayi tunanin zan hadu dashi kamar wancan ranan, amma kuma saidai ko mai kama dashi bangani ba.”
Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e, tare da karyar da wuya cikin, sanyi tace.
“To Allah Yasa ya Kira.”
Da “Ameen.” Suka amsa dukansu.
Ganin yanda Jannart din ta damu ne kuma yasa, Aysha Lawal dafa kafad’anta, cike da son bata kwarin guiwa tace.
“Please Jannart karki damu kanki, Insha Allah komai zai tafi dai dai, kuma Koda ma ace baku samu ganinsa yanzu ba, ai ba matsala saboda MD yace ya k’ara miki one week, saboda rashin lafiyarki, kinga before nan ma kin sake warwarewa.”
Jin abunda Aishan ta fad’ane yasa, Jannart sauke Ajiyar zuciya mai karfi.
Cikin Jin dadi tace.
“Alhamdulillah, amma duk da haka nafison naganshi nan kusa, saboda muyi hira dashi asatinnan,kinga hakanne kad’ai zai karamin nutsuwa.”
Kansu suka jinjina dukansu, tare da sake bata kwarin guiwa akan cewar Lallai zata ga DR. Rayyern Bashir Muhammad Mainasara.
Haka dai suka ci gaba da hira, saidai kuma basu wani jima sosai ba, sukayiwa Jannart din sallama suka tafi.
Bayan tafiyar tasu ne kuma Jannart din tabi Momy kitchine Dan Tayata aiki.
Ganin Jannart din acikin kitchine ne kuma yasa Momy cewa.
“A’a Jannart bazaki fara aiki daga yanzu ba, kwata kwata ma yaushe ne kika samu sauki, ki koma ki zauna ni zan karasa komai.”
Jin abunda Momyn ta fad’ane yasa ta k’wab’e, fuska cikin sigar shagwab’a tace.
“Dan Allah Momy kibari nayi aikin ko kad’anne Allah naji sauki sosai.”
D’an Jim Mamyn tayi, saidai kuma ganin yanda Jannart din ta matsa yasa, ta bata bleending na pineapple.
Haka kuwa suka shiga yin aikin suna hira.
Bayan sun kammala ne kuma Jannart ta koma daki koda tayi sallahn Isha kwanciya kawai tayi.
*Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ne kacal karamin group kuma 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in kuma babu halin turawa ta banki ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp number na. Babbancinsu a yawan posting ne, dan girman Allah da Manzonsa kada ki karanta min littafina in baki biya, in kin biya kuma kiyiwa Allah kada ki fitarmin da littafina domin ba kuɗin mallakansa kika biyaba kuɗin samun damar karanta littafin kika bada*
Acan b’angaren Dr. Rayyern kuwa gaba daya sabgogin gabansa yake, musamman ma yau din da duk baisamu zama ba, Domin gaba ɗaya wuninsa acikin Hospital yayi sa, saboda wasu patients da aka kawo masa, masu heart attack yayi musu operation.
Adangane da batun Barrister Kabir kuwa, tuni ya watsar da duk wasu maganganun da sukayi da Barrister din acikin kwandon shara, impact ma shiya manta da wani batun maganan aure da aka fara.
Domin ko yanzu daya dawo gida, bayan yayi sallan isha ko dinner bai tsaya yiba, kaitsaye ya wuce bedroom d’insa.
Bayan ya sake wankane kuma ya dauro alwala, tare da kimtsa kansa cikin wasu tausassun fararen kaya.
Chocolates d’insa masu dadi yaci har kusan Leda uku dake ledan ƙananane, kafun ya daura da ruwa.
Ko takan laptop d’insa bai kuma biba, baccin gajiya ya daukesa.
Ahakama Acan b’angaren Riyyam-nsra, duk wunininsa na yau acikin dakin hotel din Tahir Guest Palace yayi sa.
Yayinda yake manne da wayarsa tsawon awanni kenan yanzu daya ke bad chat da wata sabuwar babe yar k’asar Morocco daya samu.
Kwata kwata yarinyar bata da kunya, da kamun Kai.
Wanda hakanne kuma yasa gaba daya Riyyam nsra ya susuce akanta, tare da b’ata duk wasu lokutansa na yau din akan yarinyar.
Domin kuwa Koda Ramadan ya kirasa akan yazo suyi dinner, cewa yayi sai Gobe da safe zaizo suyi breakfast, saboda yau din bacci yakeji sosai.
Akasin hakan kuwa saida yakai 2 am a online inda suke vedio chat da yarinyar ta Instagram.
Wanda ko kaya babu ajikinta.
Haka take zaune agaban wayarta single, Yayinda shi kuwa Riyyam keta susucewa akanta, Koda suka fara video sex chat, kusan gigicewa yayi, saboda yarinyar ta fisa tsaurin ido da iya iskanci sosai.
Saboda zaucewar da Riyyam din yayi kuwa, harji yayi inama da ace yayi tsuntsuwa ya gansa a Morocco, manne ajikin abokiyar tab’ewar tasa.
Haka dai ya hana idanunsa bacci. Har sai 3am kafun bacci ya daukesa ba kuma ibada yakeyi ba.
*Washegari.*
Kamar kullum kuma kamar Koda yaushe.
8 am dai-dai gaba ki dayansu zaune suke akan babban dining table din.
Abba, Mamy, Rayyern, Ramadan da kuma Riyyam nsra wanda kallo daya zakayi mishi kafahimci cewar bacci bai ishesa ba, saboda yanda idanun nasa sukayi luhu-luhu.
Rayyern kuwa da tun zamansu awajen yake lure da yaron, tass ya fahimci cewar yaron baya bacci da wuri, saboda wani dalili dayayi imani cewa ba dalili mai kyau bane.
Abinci sukeci cike da nutsuwa.
Yayinda Abba kuwa ya dago kansa ahankali ya kalli Riyyam-nsra.
Cikin kuma son sake sanin da wanda suke tare.
Ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Riyyam”.
Da sauri ya amsa tare da kallon Abban.
Shi kuwa Abba cikin tsareshi da ido yace.
"Mahaifinka yana raye? shima Acan ethopian yake da zama ne?.”
Abban ya kare maganar yana me kafe yaron da ido.
Riyyam kuwa daya Kai loman abinci bakinsa, Jin abunda Abban ya tambayeshi ne yasa shi d’ago kansa Ahankali.
spoon din dake hannunsa ya ajiye, lokaci d’aya kuma idanunsa suka cicciko da hawaye.
Labb’an bakinsa ya motsa ahankali, cikin sanyi yace.
“Mahaifina ya rasu.”
Gaba daya dagowa sukayi duk suka kalleshi.
Tare dajin wani irin matsanancin tausayin sa, musamman ma Rayyern da hakanan yaji wani iri acikin jikinsa.
Riyyam-nsra kuwa da gaba daya zuciyarsa tayi rauni, hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunsa.