← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 81

Sashe 52

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali take taka k’afafunta, Yayinda kowanni taku da zatayi yake dauke da jan hankalin mai Kallon ta.

Azahirin gaskiya kuma awajenta tafiya takeyi normal, Yayinda duk wani mai Kallon ta kuwa, ke ganin tafiyar tata tamkar tafiyar hawainiya, saboda komai nata na dabanne, tana da wani irin tsarin halitta mai matukar burgewa, wanda kuma ko ita kanta batasan cewar tana dashi ba.

Tura kofar babban office dinnasu tayi ta shiga bakinta dauke da sallama.

Jin Sauti da amon zazzakar muryar nata ne kuma yasa, duk mutanen dake cikin office din juyowa suka kalleta.

Wani dogon tsaki Asiya taja tare da kauda kanta daga kallonta.

Ita kuwa Jannart Sam hankalinta ba a kanta yake ba, duk da irin Kallon da taga tanayi mata kuwa Amma bata damu ba.

Fuskarta d’auke da murmushi ta k’arasa wajen, Aysha Lawal da kuma Salman wanda suke zaune awaje daya suna duba wasu takardu.

Murmushi Aisha Lawal din ta sakar mata, tare da cewa.

“Jannart Idi Saleh Dakata yau kinyi lattin zuwa wajen aiki, saboda haka sai munciki tara.”

Murmushi mai kama da dariya Jannart din tayi, har saida fararen hak’waranta suka bayyana, hakan kuwa shiyasa dimples dinta duk suka lotsa.

Kafad’an Aysha’n ta d’an buga, kana cikin muryata da babu hayaniya sosai tace.

“Kai Aysha kwata-kwata fa mintuna 10, na kara akan yanda nake zuwa kullum.”

“Eh duk da haka dai.”

Ayshan ta fad’a tana murmushi.

Jannart kuwa zama ta d’anyi agefe dasu, tare da dawo da Kallon ta ga Salman Wanda ya saki idanu da baki yana Kallon ta.

Had’a idanu da sukayi ne kuma yasa shi saurin janye idanunsa daga kanta.

Itakuwa Jannart batare da ta fahimci komai na daga Kallon da Salman din keyi mata ba tace.

“Good morning colleague.”

Gashin kansa ya d’an Sosa kana awayance yace.

“Morning Colleague, fatan kin tashi lafiya ya jikin naki.”

“Da sauki sosai, Domin nama warke yanzu babu wani abu dake damuna.”

Jannart din ta fad’a tana me ajiye Jakarta,
Adai-dai lokacinne kuma Hajia Rabi'ah da Aunty Fauziya D Sulaiman suka shigo, cikin sashin su Jannart din.

Ganin Jannart din da sukayi acikin office dinne kuma yasa, Aunty Fauziya D Sulaiman sakin murmushi, kana cikin jin dadi da kamala da mutuntaka tace.

“Masha Allah gaskiya Jannart ansamu lafiya, tunda har an fara fitowa office.”

Murmushi Jannart din tayi, cikin kuma jin dadin kulawan da yan office din nasu ke bata tace.

“Alhamdulillah my Aunty Fauziya naji sauki, kuma Ina saka rai da fatan cewa Insha Allah Gobe ma zan gudanar da program dina.”

Kai Aunty Fauziyan ta jinjina, tare kuma da matsowa kusa da Jannart din sosai.

Cikin yin k’asa da murya irin ta maganan sirri tace.

“Masha Allah, amma Jannart kinaga kuwa Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din zaizo.”

Kanta tad’an langwabar tare kuma da juyawa, ta kalli Salman wanda shidinma kuma Kallon ta yake.

Kai Salman din ya jinjina mata, cike dason bata karfin guiwa yace.

“Karku damu Insha Allah Zaizo.”

Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da daura hannayenta akan kafad’an Jannart din.
Murya atausashe tace.

“Karki damu Jannart, ko da ma ace bai samu zuwa goben ba, ai kina da sauran chance harna tsawon one week, Insha Allah kuma muna saka ran dacewa.”

Kai kawai Jannart din tad’an jinjina, tare da komawa ma zauninta ta zauna, lokaci daya kuma duk jikinta yayi sanyi, domin tasan gobenne kawai last hope dinta, kasancewar bata da tabbacin cewa, wani satin zata kasance available, musamman ayanzu da Abba Kabir yake kokarin fara shirye shiryen b’oyeta.

“Yah Allah Kabani sa’a.”

Tafad’a k’asa-k’asa, tare da maida idanunta ta lumshe, saboda gaba daya yanzun ta karaya da komai.

Salman kuwa daya karanci tarin damuwa akan fuskar Jannart din, ji yayi komai na Office din baya yi mishi dadi, duk yanda yaso ya daure zuciyarsa akanta kuwa baya tab’a iyawa.

Haka yake d’agowa time to time yana satan Kallon ta.

Itakuwa Jannart samma batasan yanayi ba.

Aysha Lawal ce kawai take lure dashi, fahimtar abunda ke ran Salman din agame da Jannart dinne kuma ya sakata sakin murmushi.
Batare kuma da tace komai ba taci gaba da ayyukanta.

Haka dai Jannart ta kare gaba d’aya wuninta a office din, duk yanda kuma taso kawar da fargaban dake ranta ta kasa.

K’arfe 5 dai-dai tayiwa su Salman da Aysha Sallama,kaitsaye ta wuce gida.

Koda suka iso gidan nasu, haka ta fito daga cikin mota gaba daya duk jikinta asanyaye.
Direct falonsu ta nufa, inda tana shiga cikin falon kuma wayarta dake rik’e a hannunta ta soma kara.

Kallon ta ta mayar kan screen din wayar.
Lokaci daya kuma murmushi ya bayyana akan fuskarta, saboda sunan Yah Azeez da ta gani.

Picking call din tayi, tare da kara wayar akan kunnenta.

Sallaman da tayi dinne kuma yasa Daga can b’angaren Yah Azeez ya amsa mata, tare da cewa.

“My y’ar k’anwa Jannatuwa, bari na fara bada hakuri kafun ki shigo da korafin rashin kiranki da wuri da banyi ba.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan shagwab’e fuska, tamkar Yah Azeez din yana ganinta. Tace.

“ai saura kad’an nayi maka fushi Yah Azeez, kuma da baka kirani yau ba ko hmmm, ko kakira bazanji rarrashi ba.”

Murmushi Yah Azeez din yayi, cikin tsananin so da Kaunar yar uwartasa yace.

“I’m sorry Jannart wallahi aikine yayimin yawa kuma na kira sau biyu Mom ke ɗagawa tace kina bacci, yanzu ya jikin naki, Ina fata kinji sauki sosai.”

Kanta ta jinjina had’e da cewa.

“Naji sauki sosai Yah Aziz, Domin yau har wajen aiki naje, yanzu shigowa ta ma gida.”

“Masha Allah Lallai jiki yayi kyau, To Allah ya kara afuwa, sannan kuma ki kara hakuri kinji Jannart, Insha Allah watarana sai labari, komai da Junaid keyi miki zaizo ya wuce, kuma Allah zai saka miki akan duk wani cutarwa da Junaid keyi miki, shima kuma zai ga sakamakon abunda ya aikata.”

Idanunta ta d’an lumshe, saboda har acikin zuciyara taji sanyi da dadin kalaman Yayan nata, inama da ace shine akusa da ita ba Junaid ba, Lallai da taji dadin duniya, Domin ko ayanzu da baya kasar, yana iyaka kokarinsa wajen bata kulawa, da nuna tausayawansa agareta.

Numfashi ta d’an fesar kana Asanyaye tace.

“Nagode Sosai Yah Azeez, kuma Insha Allah zan kara hakuri akan wanda nakeyi.”

Murmushin Jin dadi Yaya Azeez din yayi, Domin dama yasan tuncan k’anwartasu mai biyayyace, akan duk wani abu daka umurceta.

Still cikin nuna kulawa yace.
“Yauwa y’ar k’anwata, yanzu fad’Amin akwai wani abun da kike buk’ata ne, ko kud’i sai na tura miki ta account, ki saya duk wani abu da kikeso.”

Murmushi tayi, hadi da cewa.
“A’a Yah Azeez bana buk’atar komai.
Domin last week Abba Kabir yayimin shopping, sannan kasan akwai kudi da yawa a account dina, ko salary na Idan anturomin bana sayan komai dasu.”

Ajiyar zuciya Yah Azeez din dake kan wayan ya sauk’e.
Nandai suka d’an tab’a hira kafun daga bisani sukayi sallama.

Bayan ta kashe wayar nata ne kuma ta lek’a kitchine ko zata ga Momy, saboda tunda ta shigo babu motsin kowa agidan.

Ganin kitchine din bakowane kuma yasa kaitsaye ta wuce bedroom dinta, saboda tanason yin wanka Tsarkin data samu.
Akwai kuma wasu bayanai da zata had’a acikin system dinta.

Acan B’angaren Dr. Rayyern Muhammad Mai-nasara kuwa zaune yake akan wata had’add’iyar royal chair, Yayinda yake sanye da wani had’add’en suit mai kalan ruwan k’wai ajikinsa.

Daga gefe guda kuwa drinks da kuma Chocolate d’insa ne, sai kuma sabuwar wayarsa Iphone daya k’ara saya, dake rik’e ahannunsa.

Inda kaitsaye ya shiga cikin contact d’insa, yana neman wani numbern tsohon abokinsa, Salisu, saboda yanason yiwa Salisu din ta’aziyya kasancewar yaji labarin rasuwar Baban shi.

Yana cikin tsaka da duba contact dinne kuma, idanunsa suka sauk’a akan numbern Salman.

Numbern da Idan bazai manta ba, sune wanda suke son ganinsa, ya kuma yi musu alk’awari zuwa.

Saurin sanya hannunsa yayi ya dafe kansa, saboda sai ayanzu ne ma abun ya fad’o masa, gaba daya kwata kwata ya manta ma dasu.

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da dan cije Labb’an bakinsa.

Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Allah Nagode ma daka tunatar dani, Allah kada ka bani ikon daukan al'k’awarin da bazan iya cika shi ba.”

Jawo wayarsa yayi ya duba date da kuma rana.

“Today is Wednesday, gobe ne al'k’awarin dana d’auka kenan zai cika, Insha Allah zanyi kokari naje, kodan yaronnan ya tsira da aikinsa, ya kuma samu abunda zai ciyar da iyalansa.
Tabbas zanyi cancelling duk wani schedule dina na Gobe, har sai na samu naje tv station dinnan, bazan tab’a zama mai karya alk’awari ba Insha Allah bazan zama sanadin rasa aikinsa ba.”

Ya fad’i hakan, yana me mik’ewa tsaye, tare kuma da d’aukan laptop d’insa.

Kaitsaye ya koma wajen zamansa da yake na musamman, acikin katafaren office din da yake new company’n’ sa.

Tahir Quest Palace.

Riyyam nsra ne kwance akan makeken gadon dake dakin hotel din, wanda kuma yanzun gama wayarsa da Mammy da kuma Zaiton.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da juyowa ya kalli, matashiyar budurwar dake kwance agefensa.

Almost 1hour kenan yanzu da zuwan ta wajensa, wanda kuma itama sun had’u ne da ita anan Tiktok, Yayinda itama take cikakkiyar celebrity ce a Tiktok din, sannan kuma yar asalin Nigeria ce cikin Kano tayi shuhura a iya tiƙa rawa da bin waƙa, ga iya sa fitinennun suturu masu bayyana tsiraici hakan yasa kasuwarta ke ci.

Idanu Riyyam din ya zuba mata, Domin kuwa Wannan shine Karonsa na farko daya fara mu’amala da wata mace y’ar Nigeria.

Yarinyar dake kwance agefen nasa, kuwa ganin irin Kallon daya ke mata ne, yasa ta kashe masa Ido, tare da turo masa kirjinta gaba, wanda ko kaya babu ajikinta.

Hakan ya faru ne kuma saboda sheke ayarsu da sukayi ita da Riyyam nsra din.

Wani irin nishadi takeji acikin zuciyarta, kasancewar Riyyam din yayi mata hundred percent.

Shikuwa Riyyam da baya gajiya da tab’ewa, hannunsa yasa ya shafo kirjinta, cikin kuma yin k’asa da murya hadi da kashe mata idanunsa yace.

“Are you ready?.”

Idanu ita dinma ta kashe masa, hade da jinjina masa Kai alaman she’s ready.

Batare kuma da ta bari ya kawo kansa ba, ta hade bakinsu waje daya.
Chapter 52 · 0% Book details