← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 81

Sashe 57

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*

By
*GARKUWAR FULANI*

D’an gyara zamanta tayi, tare da sake fuskantar cameras din dake shooting fuskarta.

Ajiyar zuciya ta d’an sauke tare da nemo jarumtarta dake suɓuce mata,
cikin Taushi da kuma amon muryanta zakin tace.

“Assalamu Alaikum Masu kallonmu, sannunmu da arzikin sake saduwa, acikin shirinmu mai farinjini wanda mukeyi Domin farincikin ku, wato Bak’onmu na Mako, To ayau dai shirin namu ya gam da katar yayi babban kamun gayyato muku wani babban bak’o, wanda nasan idanuwanku suna cike da dokin ganinsa. Wannan bako kuwa ba kowa bane face. Dr...!”.
Sai ta kuma datse sunan tare da sakin murmushi.
Wanda hakan yasa kab masu kallo suka ɗokanta da son jinnwayene baƙon makon.
Mayafin kanta ta ɗan gyara tana mai jin harshen ta bazai iya furta sunansa ba, cikin nitsuwa ta tare da lumshe taci gaba da cewa.
“Sanannen mutumin da sunansa yayi shuhura acikin kasarmu Nigeria dama wajenta baki daya, nasan da yawan masu kallo basu tab’a Ganin wannan bak’on namu ba.
Dan yauce rana ta farko daya amsa gayyatar wata kafar sadarwa ta jarida, da TV. Alhamdulillah sai namu a yau.
Kasancewarsa Babban Doctor kuma babban d’ankasuwa da duniya ke damawa dashi, saboda haka yau dai gamu gashi, zakuma mu haska mukushi, inda zai fayyace mana koshi din waye.”

D’an tsagaitawa da maganan nata, tayi tare da juyowa Ahankali ta fuska ce sa.
Cikin muryarta mai taushi tace.

“Doctor barkanka da zuwa, barkanka kuma da shigowa cikin wannan tasha tamu mai Al'barka, da fari dai munaso ka gabatar da kanka ga masu kallonmu.”

Numfashi ya d’an sauk’e, batare kuma da wani sakin fuska ba, ya dago da kansa ya d’an kalli cameran a fakaice, cikin muryarsa da ako yaushe yake kara bayyana asalin wanene shi yace.

“Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.”

Ya k’are maganan atak’aice, Cikin kuma halin nitsuwa.

Kai Jannart din ta jinjina, tare da hade yatsunta awaje daya, cikin tsananin kwarewa da sanin makamar aikinta tace.

“Masha Allah to Dacta, yanzu dai ka gabatar da kanka awajen al’umma, saura kuma mu shiga cikin shirin namu ka'in da na'in,.
Dai-dai lokacin kuma aka ɗan ɗauke fuskokinsu aka sa ɗan sautin tambarin tashar Arewa 24 din.
Kana aka dawo dasu.
Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi a fakaice kana a hankali tace.
“Shin amatsayinka na cikakken Likita, wanda kasa keji dashi, wacce irin shawara zaka bawa al’umma dan kula da lafiyarsu da matakan kariyar riga-kafi?.
Sannan kuma ya kake Ganin irin yanda al’amarin k’asarnan yake, ma’ana irin halin da al’ummar k’asar take ciki, da kuma irin k’alubalen da muke fuskanta more Especially wurin kiwon lafiyar kananan yara da mutanen karkara da tsofaffinmu, Sannan wani irin hanya da kuma mataki zamu bi, Domin mu samu nasara akan yaƙar cututtukan dake addabar al'ummar ƙasar mu?
Then menene matsalarmu aharkar malaman kiwon lafiya?”.

Kanshi ya ɗan kauda gefe tare da yamutsa fuska, ɗan gajeren tsaki yaja.
Ji yadda yarinyar nan take zuba babu ƙaƙƙautawa kamar carbi ya tsinke ko numfashin bata ja.
Ta wani jero min tambaya kusan goma, a dungule.
Ni Radio ne ko ni parrot ne da zan iya haka.
Duk yayi tunanin cikin second 5.
Numfashi ya ɗan fesar kana cikin haiba da dakewar murya yace.
“Privet Hospital!!!
Sune matsalan kiwon lafiyar kasarmu.
Domin sune suke dak’ushe asibitocin gwamnati, har suke zama ba masu inganci ba.”

Ya fad’i maganan kai tsaye, batare kuma da wani dar ko shakka ba.

Jannart kuwa Kai ta d’an jinjina, tare da sake rik’on wani farin card dake hannunta, saboda acikine duk wani tsare tsaren tambayoyin da zatayi masa suke.

Kanta ta d’ago daga Kallon takardar da takeyi, still kuma Cikin muryarta da akoda yaushe take fitar da daddad’an sauti tace.

“To Dakta. munji abunda kace. Kuma al'umma zata iya gamsuwa da hakan.
Toh amma kamar wani mataki za’abi, Domin asamar da ingancin asibitocin Gwamnati da kiyaye lfy?.”

Numfashi ya ɗan fesar a hankali kana yace.
“Dole gwamnati ta tsaya ta gyara asibitotin ta, ta ingantasu hade da kawo nagartattun kayan aiki, da kuma kwararrun ma’aikata, baya ga haka kuma ta rika biyan likitotin isassun kudaden da zasu iya biya musu bukatunsu, saboda mafi akasari acikin kasar bawai Nagartattun Doctor’s dinne bamu da suba, kawai dai basa samun yanda suke sone, hakanne kuma yasa suke fita wasu k’asashwn suje su fara aiki Acan, ko kuma kowannensu saiya zaga gefe yaje ya bud’e asibitin kanshi, saboda baisamu yanda yake so a gwamnati ba, wannan dalilin yasa ayanzu asibitocin gwamnati suka lalace suka zama kara zube,, Domin anriga da ancire Tubalin abunda aka gina asibitin akai haka yasa duk mai ƙarfi da yar wadata bazaibi ta kan asibitin gwamnatin ba, wanda kuma da al'ummar ƙasa aka ginasu.
Sannan yana da matukar muhimmanci ga iyayen yara suke kula da tsabtar jikin raya da muhalli da abinda zasuci domin shine babban rigakafi.”
Ya k’are maganan yana me gyara zaman necktie din dake wuyansa.
Sosai yayi masifar kyau yadda yake dan jujjuya fararen yatsunshi

Inda Jannart kuwa ta ci gaba da cewa.

“To Doctor yaya za’ayi agyara matsalar Government Hospitals din domin in ƙantasu ta yadda al'ummar ƙasa zasuje garesu da kekkyawan yaƙini!?.”

Dan muskutawa yayi still kuma cikin rashin tsoro ko fargaba cikin yaƙinin da Kekkyawar manufa yace.

“To Da farko dai asibitotin gwamnati abunda zai gyarasu abu maisauki ne!?”.
Da sauri ta ɗan fuskanceshi tare da cewa.
“Duk da lalacewar da sukayi gyaran mai sauƙin ne? Ta yaya ko kuma ta ina gyaran zai fito da sauki!?”.
Cameras din ya ɗan kalla kana ya gyara zamanshi tare ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin masakaicin amo yace.
“Idan har gyara akeso ta yadda zasu in ƙanta tofa dole daga kan, Shugaban k’asa, Governors, Ministers, senator's har zuwa kan ciyamomin kana kama daga Sarki, Waziri, Galadima, Wambai, Chiroma, Durbi, Garkuwa, Ɗan buram, Majidadi, Ma'aji, dama duk wasu masu fad’a aji, na siyasa da masarautun gargajiya. suyi kokarin daina zuwa asibitotin kudi, ko fita kasashen waje Dan duba lafiyarsu, su tsaya su ingata asibitotin Gwamnati, ta hanyar dasu kansu asibitotin zasuna basu Kekkyawar kulawa,
Ya zama asibitin da Sarki zaije.
To shi fadawan sarki zasuje.
Kana asibitin da shugaban kasa zaije ya zama shine na talakawa, ta hakane zai sa shugabanni su san halin da asibitocinsu suke ciki, da inƙancin likitocin da kayan aikin.
Haka zai sa a kula da in ƙancin asibitocin.
Domin duk wani asibitin gwamnati matukar akwai ingantattun Doctor’s da kayan aiki da watar tsabtacewa.
Toh dai-dai yake da duk wani asibitin kudi, hakanne kuma zaisa asibitotin kudin su dakushe, su durkushe.
saboda yawnacinsu bawai anginasu Dan taimakon al’umma bane, anginasu ne kawai saboda neman kudi irin na yaki haram yaki halal, tayanda talaka bazai tab’a amfana dasu ba sai dai su cika aljihunsu.”
Da sauri Jannart ta juyo ta kalleshi.
Ido cikin ido sukayi da juna,
Bakinshi ya taɓe tare da yimata wani irin munafukin harara, hakane yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta
Kai ta jinjina, cike kuma da gamsuwa da kalaman nasa tace.

“Tabbas maganarka tatafi Kan hanya mai kyau, sai-dai kuma amma baka ganin yin hakan zai dakushe mutane da dama, musamman ga masu privet hospital kamar yanda ka fad’a!!!.”

Kansa ya d’an girgiza, sannan kuma akaro na farko da tun zamansa awajen ya dago kansa da nufin ya kalleta da kyau dan tambayar da tayi masa.
Saidai ko secan daya bai dauka yana kallontan ba yakau da kansa gefe.

In don’t care manner yace.
Chapter 57 · 0% Book details