← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 81

Sashe 31

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba kuwa bud’e katon gate din yayi, Inda Rayyern ya tura hancin motar tasa cikin gidan, saidai kuma ganin da yayi cewa Abban nasa da kansa ya bud’e gate din gidanne yasa, batare daya kutsa can ciki ba yayi parking motar.
Tare da bud’e murfin motar ya fito.

Cikin dan girmamawa hade dayin kasa dakai yace.

“Abba Baba Maud’o barkanku da dare, amma Abba da ka bari ai na fito da kaina ma zan iya bud’e gate din.”

Kai Abban ya girgiza tare da cewa.

“A’a ai hakanma baiwuce motsa jini bane, Baba Maud’o ma da kansa yace zai bud’e amma nace masa ya bari, sannunka da dawowa ya hospital din?”
Abba Yayi masa tambayar cikin kulawa.

“Alhamdulillah Abba,".
Kana ya kalli Baba Mauɗo cikin kulawa yace.
"Baba Mauɗo gsky ni na gaya maka bana son kana aikin nan naka, zamu Ari ya rinƙayi aikin gadin, wlh bana jin daɗi inga kana buɗe mana gate.”
Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da cewa.
"Rayyanu kenan to me a ciki ai motsa jiki ne kawai”.
Kanshi ya jujjuya kana ya kalli Abba tare da cewa.
“Ramadan yana ciki ko.”

Kai Abban ya jinjina masa, tare da cewa.
“Eh shima Ramadan din yanzu ya dawo ya maida wancan bakon yaron masaukinsa.”

Dan jinjina kai yayi kana kaitsaye ya wuce cikin gidan.

Ahankali ya tura kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama.

Ramadan da kuma Mamy dake zaune acikin falonne suka amsa masa.

Cike kuma da farincikin ganinsa Mamy tace.

“Masha Allah Rayyern ka dawo.”

Kansa ya jinjina tare da cewa

“Eh.”

“Barka, ya hospital din.”

“Alhamdulillah.”ya fada yana me karasowa cikin falon.

“Hamma Rayyern sannu da dawowa, tun dazu Riyyam ke jiran dawowanka, amma ganin baka dawo da wuri ba, yasa na maidashi masaukinsa dan yaƙi ya tsaya yaci abinci ma, sai zuba mishi Mamy tayi ya tafi dashi.”

Cewar Ramadan Wanda yake Kallon Hamman nasa.

Gajiyayyun Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma da gyad’a kanshi ahankali, cikin yanayin kasalan daya saukar masa ya nufi stairs din dazai haurar dashi sama zuwa d’akinsa.

Da kallo Mamy da Ramadan suka bishi har saida ya b’acewa ganinsu, kana Mamy taja dogon numfashi tare da sauk’e ajiyar zuciya...!

*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 13
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE ne*

*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama da aminci special Group 1k ƙaramin group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in Kuma baki da halin turawa ta account sai ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp 09097853276*

Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻

Yayinda acikin ranta take fata da kuma burin ganin auren d’an nata, Tabbas tana matuk’ar son ace mata Rayyern dinnata yayi aure, domin kuwa ko babu komai zai samu macen da zata kula dashi, Wanda zata jib’anci duk wani al’amuransa, kama daga ci da sha zuwa farin cikinsa kula mishi da tsabtan muhalinsa ko Ramadan ma ya huta.

Sai-dai kuma amma ya zata yi, tunda duk sun fahimci cewar ba son auren yake ba, baya shiga harkar mata, balle harsu saka ran cewar watarana zai samu wacce zata yi mishi.
Ido ta zuwa Ramadan wanda kiran wayarsa da akayi yasa ya miƙe ya nufi Dinning area, bisa kujera ya zauna.
Bisa alamu duk.
Raihana ce ta kirashi budurwarshi.

Rayyern kuwa yana isa cikin bedroom din, kayan jikinsa ya rage tare da shigewa cikin bathroom ya sakarwa kansa ruwa.

Idanunsa ya lumshe adai-dai lokacin da yaji Sauk’an Sassayan ruwan showern akan fatar jikinsa.

Haka yakejin wani irin nutsuwa na musamman na sauk’ar masa.

Ahankali kuma yakejin duk tarin gajiyar da yayi yana sauka.

Atsanake ya kammala wankan nasa, inda ya fito daga shi sai towel dake daure a kugunsa, ad’ayan hannun nasa kuwa mini towel ne Wanda yake tsane jikinsa dashi.

Bayan ya kammala ne kuma ya Shafawa jikinsa wani had’add’en mai, tare da men spray mai dadin kamshi.

Sabin riga da wandon da ya ciro daga cikin drawer d’insa ya sa.

A hankali ya fito dan sauƙa ƙasa, coffee yake so ya ɗan sha.

Yana fita falo kuwa ya samu Abba da Ramadan a tsakiyar falon da alamun mgnar Aure Ramadan yakeyiwa Abba.
Shi kuwa Abba idanu kawai ya zubawa Ramadan yana kallonsa, ya sani a zatonsu bai damu da mgnar auren Rayyern bane.
Shi kuwa yasan sunada babban buri da manufa da shi yakeso yaga Rayyern ya cimmawa, so ganin bai damu da harkar mata bane yasa ya zuba mishi ido, tunda shi nuna musu yake baima san me akeyi da maceba shi kanshi yasan aiyukan daya ɗaurawa Rayyern sun mishi yawa sunfi ƙarfin shekarunsa kawai ƙarfin hali ne da ƙwazo da jarunta yasa yake iya leading komai yadda ya kamata, amman ya rasa lokacin kansa, yana son ya sashi ya saki aikin asibitin ya fuskanci kasuwanci su, to kuma yasan likitancin shine burinsa badon hakaba ai da sai ya bawa Ramadan sashin asibitin duk da dai yanzuma shi bai cika zuwaba.

A hankali ya ƙara so kusa dasu.
Ganin haka ne yasa suma
suka miƙe suka karasa kan dining table danyin dinner.

Shidai Rayyern kamar kullum baiwani ci abincin kirki ba, ya tashi tare dayi musu sallama ya wuce side d’insa.

Yana shiga kuwa ya murzawa kofar tasa key.

Toilet ya koma ya sake dauro alwala, bayan ya fito ne kuma ya sanja kayan jikinsa izuwa payjamas mararsa nauyi.

Wata yar jaka da yake ajiyan chocolate d’insa ya dauko, tare da bud’e cikin jakan ya dauki babban ledan chocolate na milka & oreo, bayan ya Bare ledan ne kuma yasa chocolate din abakinsa, tare dayin switchoff na wutan dakin ya kwanta.

D’an mirginawa yayi, kana ya dauki wayarsa dake aje akan gadon.

Sak’onnin Email da ake turo masa ya shiga dubawa atsanake, time to time kuma yake lumshe ido saboda yanda yake jin dadi da kuma zakin chocolate din na game bakinsa.

Ya dauki sama da 30minute kuwa yana duba sakonnin, inda yake replies na wasu sakonnin da suka zama dole, sauran sakonnin kuwa da basu da buƙatar amsa sharewa yayi tare da kashe datansa ya ajiye wayar.

Yana gama shanye chocolate din nasa kuwa, ya daura kansa akan pillow tare da jawo blanket ya rufawa jikinsa.

Addu’an kwanciya bacci yayi, kamar kuma yanda ya saba yi akowacce rana, haka yau dinma Yana me ambaton sunan Allah bacci ya daukesa.

10:30 pm.

Jannart.

Sake had’e jikinta waje d’aya tayi, tare da rungume dan k’aramin pillown dake Manne akirjinta.

Ak’alla yanzu kusan mintuna 20 kenan da takeson bacci ya dauketa amma ya kasa, duk yanda takai ga rumtse Idanunta kuwa, To wasu kalan tunani ne ke bijurowa cikin k’wak’walwarta.

Yayinda ƙamshin turaren dake fita ajikinta Yana me Ratsa cikin hancinta ya hana ta sakat.

Akasalance kuma cikin yanayin shagwab’a takai hannun ta dake kamshin turaren zuwa kan hancinta, Sam batasan taya akayi kamshin dake jikin al'kyabban nasa ya kama jikinta ba har hakaba.
Chapter 31 · 0% Book details