← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 81

Sashe 69

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin shiru ne kuma yasa Momyn juyawa ta fita, saboda atunaninta ko Jannart din tana cikin toilet ne.

Kaitsaye dining table ta dawo, tana zuwa kuwa, Daddy da Abdull suma suka fito suka zauna.

Momyn ce tayi saving dinsu, tana cikin saving dinnasu ne kuma, Junaid ya shigo cikin falon, yana fito, daga shi kuma sai t shirt da gajeren Wando.

K’arasowa dining table din yayi, batare daya gaisar da kowanne daga cikinsu ba, cikin iskancinsa irin na wasu masifaffun sojoji yace.

“Ina Jannart?”

D’agowa duk sukayi suka kalleshi.

Sanin halin rashin mutumcinsa ne kuma yasa Mom tace.

“Yanzu na dawo daga dakinta banganta ba, tun safe kuma bata sauko ba, amma Ina tunanin ko tana toilet ne.”

“Bawani bata gidan nanne ma gaba d’aya, y’ar iskar yarinya, jiya ma da dare ai naje dakinta amma bansa meta ba, wallahi Idan na kamata sainaci Uwarta.”

Baki Momy ta tab’e, tare da kallonsa cikin yanayin mamaki tace.

“To kai meya kaika dakinta da dare?.”

“Oho bansani ba, munafurci kawai.”

Junaid din ya fad’a kaitsaye, babu wani shakka ko shayi.

Duk da Abba yana jinsa kuwa, haka yayi shiru bai tanka masa ba, saima Kallon Momyn da yayi, yace.

“Kije ki duba toilet din, ko me ta keyi kice mata ta bari, injini tazo mu yi breakfast.”

“To.” Momyn tace, tare da juyawa tasake nufan dakin Jannart din.

Tana zuwa ta tura kofar, but still Jannart bata ciki, da d’an mamaki Momy ta karasa jikin kofar toilet din, tare da kasa kumnenta.
Waiko zataji karar ruwa, saidai bataji komai ba, hakan yasa Momyn ta tura kofar tana me kiran sunan Jannart.

Saidai meye, idanunta ba abunda suka gane mata, domin kuwa Jannart bata cikin toilet din.

Mamaki ne ya kama Momyn, saboda Sam bata taba tunanin Jannart bata cikin toilet din ba.

Juyawa tayi cikin sauri ya dawo falo.

“Alhaji Jannart fa batanan, na duba bata dakinta kuma bata bayan gida.”

Cak Alhaji Idi Sale Dakata yatsaida duk wani abu da yakeyi, cikin yanayin mamaki had’i da razana yace.

“Bangane mekike cewa ba, wannan wani irin maganar banza ce, tayaya zakice bata dakinta kuma bata bayan gida, wannan gashi anan dinma batanan, To ko tana dakinki ne?”

Kai Momy ta girgiza da sauri, tare da cewa.

“A'a wallahi bata dakina, tun Safe ma banga sauk’owarta ba, zaiyi wahala ace ma tana dakina.”

“Kije ki duba ta yanzu.”

Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Hakan yasa da sauri Momyn ta juya zuwa dakinta, kamar yanda ta zata kuwa hakanne, domin Jannart bata cikin dakinta.

Dawowa falon ta sakeyi, tare da Kallon Daddyn tace.

“Alhaji Jannart fa bata dakina.”

Idanu Daddyn ya zazzaro waje, Abdull kuwa da mamamki yace.

“Ha’a To Ina Aunty Jannart ta shiga ita da yawo ma bayinsa takeyi ba, amma bari na duba compound ko Garden ko tafita shan iska.”

Yana gama fadin hakan ya mik’e ya fita.

Kaitsaye garden dinsu ya nufa amma baiganta ba, hakan yasa ya dawo, fuskarsa dauke da damuwa yace.

“Daddy banganta ba.”

Kwafa Junaid yayi, tare dasa hannayensa a aljihun wandonsa, cikin bakar muguntan dake cinsa yace.

“Nifa Tunjiya na fada muku banganta ba, maybe yawon iskancinta ma ta tafi, dama ai ta saba tafiya kwanan gida.
Rijiyace kowanni dan iska yana iya zuwa ya zira gugansa yaja ruwa son ransa.”

Idanu Momy ta rumtse saboda har acikin zuciyarta bataji dadin bakar maganar da Junaid din ya fada akan Jannart d’in ba.

Daddy kuwa Wayarsa ya zaro daga cikin aljihun rigarsa, tare da lalub’o numbern Jannart din ya danna mata kira.

The first time akace masa wayan nata, is switch off, da Mamaki Daddy ya sake dialing airtel number dinta, still switch off, wani irin bugawa yaji kirjinsa yayi, cikin sauri yace.

“Junaid je maza ka duba side dina, watakila ko taje gaisheni ne.”

Juyawa Junaid din yayi, Inda kaitsaye ya nufi side din Daddyn, Koda ya karasa baiganta ba, har cikin bedroom na Dad din ya shiga amma babu ko alamarta.

Dawowa yayi yana ta kwafa, yace baiganta ba.

Mik’ewa tsaye Daddy yayi, cikin tsananin tashin hankali ya nufi kofar fita daga falon, batare kuma daya lura ba har tuntub’e yake.

Kaitsaye compound din gidan ya fito, tun daga nesa kuma ya soma k’walla kira.

“Ado! Ado!!”

Baba Ado dake bakin gate wurin Ashiru ne, Jin irin kiran da Alhajin keyi masa ne kuma yasashi tahowa da sauri.

Kallonsa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, kana cikin dan daga murya yace.

“Jannart ta fita ne?”

Kai Baba Ado ya girgiza kana cikin girmamawa yace.

“A’a Alhaji Jannart bata fita ba, kwata kwata tunsafe Ina zaune anan banga wani ma daya fita acikin gidan nan ba.”

Shiru Daddyn yayi, na yan wasu mintuna, kamar kuma Wanda aka tsikara yasoma k’wala k’iran Guards.

Su kuwa k’attin banzan ma sai yanzu suka tashi daga nannauyan baccin daya daukesu.

Jin kiran da Ogan nasu keyi musu ne kuma, yasa cikin sauri duk suka k’araso.

Kallonsu Daddyn yayi tsab cikin hade fuska yace.

“Ina Jannart, dawa ta fita acikin ku?.”

Kai suka girgiza dukansu, kana suka had’a baki wajen cewa.

“A’a bamuga Jannart ba, mu yanzu ma tashinmu wata kila tana cikin gida.”

“Wani irin cikin gida kuma, bayan babu Inda ban duba batanan, maza ku zagaye duka gidan nan ko zaku ganta.”
Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Nan take kuwa guard din suka bazu ako ina dake cikin gidan, amma ko alamar Jannart basu gani ba.

Hankalin Daddy yayi masifar tashi, musamman daya sake kiran wayanta yaji akashe.

Haka ya dawo falon afujajan, Yayinda Momy kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda abune kaman wasa amma yana neman Zamowa gaskiya.

Kallon Daddyn tayi, tare da Daukar wayarta tace.

“Bari na kira Barrister Kabir.”

Dialing number’n Barrister Kabir din tayi, bugu hudu kuwa Barrister Kabir ya dauka.

Bayan sun gaisa da Momynne kuma, cikin tashin hankali tace.

“Barrister bamuga Jannart bafa, munnemeta sama da kasa acikin gidan nan amma bamu sameta ba, munkira wayarta kuma akashe, Kodai tazo wajenka ne?”

Daga can b’angaren Barrister Kabir ya mik’e tsaye tare da daga muryarsa cikin nuna tashin hankali yace.

“What!! Wannan Wace irin magana ce, Ba’a ga Jannart ba, annemeta anrasa? Ita kudi ce da za’ace annemeta anratsa? Ko kuma ita din wayar hannu ce da za’ace an nemeta anrasa.”

Ya k’are maganar cikin yanayin tsawan, dake nuni da bazai iya tolerating nonsense akan Jannart ba.

Momy kuwa cikin tashin hankali tace.

“Wallahi Barrister bamuganta ba, body guards dinta da masu gadi duk sunce basu ganta ba.”

“Gani nan zuwa.” Barrister Kabir din ya fada agigice.

Tare da kashe wayar.

Bayan ya kashe wayartasa ne kuma ya saki wani irin murmushi tare da juyowa ya kalli Aunty Dijat dake zaune.

“Sakarkaru sai yanzu suka lura da cewar Jannart bata gidan, hmmm da sannu munafukan boye zasu fito fili, kowa kuma zai girbi abunda ya Shuka.”

Dariya Aunty Dijat tayi.
Yayinda shikuwa ya dauki key din motarsa ya fice.

Kaitsaye gidansu Jannart din ya nufa.

Yana isa gidan kuwa ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, ya fito.

Inda Daddy kuwa ke tsaye, gaba daya hankalinsa atashe yake sai safa da marwa yake, Yayinda kuma yake ta balbale guard din da fad’a, tankar zai hausu da duka, sai cewa yake, su je su nemo Jannart duk inda ta shiga ta fita.

Barrister Kabir kuwa agigice ya karaso, hankalinsa amatuk’ar tashe yace.

“Yaya ina Jannart? Waya dauke mana Jannart? Ina kuka kaita?.”

Kai Alhaji Idi Sale Dakata ya girgiza, cikin tsananin damuwar da yake ciki yace.

“Bansani ba Kabir, bansan Ina Jannart tayi ba, munduba ko ina amma babu ita babu alamanta.”

Hannu Barrister Kabir ya daura akai, lokaci daya kuma ya jujjuya idanunsa sukayi jajur, ahaukace ya soma neman Jannart din, tare kuma da soma zagaye cikin gidan yana leka har cikin followers, sunan Jannart din kawai yake kira da iyaka karfinsa.

Daddy kuwa bala’i da tashin hankali ne ke cinsa, cikin zafin nama kuma ya kalli Ashiru.

Afusace yace.

“Ashiru Ina Jannart waya bude mata kofa ta fita, ka fadamin nace ko kuma yanzu nasa bindiga na harbe kanka.”

Yakare maganar atsawace tare dasa hannu kuma ya dauke Ashirun da lafiyayyen Mari.

Kai Ashiru ya girgiza, cikin shanye zafin marin yace.

“Alhaji banganta ba, tun jiya gidannan akulle yake, gaba daya jiyama kowa ya sani bataje aiki ba, tunjiya bata fito ba, ga guards dinta nan suma shaidane.”

Sake hasala Daddyn yayi, Wanda hakan yasa ya sake gallawa Ashiru mari, tare da juyowa ya soma balbale Body guards din.

Cikin fushi yake cewa.

“Aikin banza k’attin banza kawai, angaya muku ahaka kawai na daukeku aiki ne, sokaye kun kwanta bacci sai kace matattu, yan iska kusan duk inda zaku ku nemomin y’ata.”

Barrister Kabir kuwa, zuwa yanzu har muryarsa ta Dishe, saboda yanda yake ta k’wala kiran Jannart.

Gaba daya lokaci daya jikinsa har karkarwa yakeyi, hankalinsa ya matukar tashi, inda yake reaction tankar da gasken gaske shima baisan inda Jannart din take ba.

Cikin kuma tashin hankalin daya nuna yana ciki ne kaitsaye ya nufi dakin Jannart din.

Yana shiga kuwa ya soma wargaza komai dake cikin d’akin, ananne fa kuma idanunsa suka sauka akan wayarta.

Da sauri ya dauki wayar dake kashe ya kunna, batare ma daya jira wayar ta karasa kawowaba ya dawo cikin falon, inda dukansu ke tsaye, cikin kuwa harda Junaid dake zukan shisha.

Wayar nata na kawowa Barrister Kabir ya shiga cikin dialing call dinta.

Aikuwa last sunan wanda tayi waya dashi Ne ya bayyana.

“Yah Junaid”

Idanu Barrister Kabir din ya zazzaro cikin matukar hasala, kuwa ya karasa cikin falon, batare da wata wata ba, ya Ware yatsunsa biyar ya zabgawa Junaid zazzafan Mari.

Tare kuma da juyawa afuce ya nunawa Dady screen din wayar Jannart din.

Cikin tsananin fushi yace

“Ba gashi ba, shine last mutum din da tayi magana dashi awaya, koma meye shi yasan inda take, Ina ya kaita? Yaya ka tambayeshi Ina ya kaita nace!!!!!!”.

Barrister Kabir din ya fada amatuk’ar tsawa ce, tsawan kuma daya saka hantar cikinsu kadawa.

Shi kuwa Barrister Kabir kuwa cikin fushi Ya...!

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
Chapter 69 · 0% Book details