Sashe 30
Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shidai kam Sauda yawan lokuta yana mamakin, yanda wasu matan ke yawo haka sakaka, babu wata kulawar kirki da suke bawa kansu ina iyayensu?.
Yar gajeriyar tsuka yaja, tare da bud’e idanunsa.
Dai-dai lokacin kuwa suka iso cikin farfajiyar katafaren asibitin nasa.
Anan cikin babban parking lot, Hadi driver yayi parking motar.
Yana gama dai-dai-ta parking din motar, kuwa Dr Rayyern ya bud’e murfin motar ya fito, fuskarnan tasa kuwa babu alaman murmushi akanta.
Dan Kallon Hadi driver din yayi, kana cikin yanayin dake bayyana, rashin iya tsawaita maganarsa yace.
“Kaje gida ka huta idan na tashi zanyi driving din da kaina .”
Kai Hadi ya jinjina, kana cikin girmamawa yace.
“To Ranka ya dad’e nagode.”
Karb’an makullin motar yayi, batare kuma daya sake cewa Hadin komai ba, ya kutsa kansa cikin asibitin.
Saboda mood din daya samu kansa aciki ne kuma yasa, ko iya amsawa tarin ma’aikatan dake gaishesa baiyi ba, kaitsaye ya wuce office d’insa.
Yana shiga cikin office dinnasa kuwa, ya murzawa kofar key.
Saboda ayanda yakejin kansa kwata kwata bayason damuwa.
Karasawa gaban dan madaidaicin fridgen dake cikin office din yayi, tare da zaro bottle water mai sanyi ya kafa abakinsa.
Bai dauke goran daga kan bakinsa ba kuwa har saida yasha fiye da Rabin ruwan dake cikin goran.
Take kuwa ya soma sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda yakejin sanyin ruwan na mamaye kirjinsa.
Wanda hakan yasa acikin kaso 10 na b’acin ransa, kaso 6 yayi kaura.
K’arasawa yayi ya zauna akan wata had’add’iyar leather sit dake cikin office din.
Cikin kuma son rage tarin ayyukan dake gabansa, ya jawo laptop d’insa dake kan desktop.
Atsanake ya soma shigar da wasu bayanai akan Campany'shi da aketa aikinshi yanzu, wanda yafi duk sauran na jahohin girma.
Still kuma time to time yake sauke ajiyar zuciya.
Acan b’angaren su Jannart kuwa, daga wajen buga wasan Polo’n, basu wani dau lokaci mai tsawo suna tafiya ba, cikin mintuna kalilan suka iso gidan television din nasu, na Arewa24.
Kamar yanda suka fita asace kuwa haka yanzun ma suka dawo asace.
Inda Salman yayi parking motar tasa acan baya, inda babu wanda zai gansu.
Hakanne kuwa yasa cikin sauri Jannart ta fito daga motar, tare da sanya hannayenta duka biyu ta gyara zaman al'kyabban dake jikinta.
Ahankali ta soma tafiya sai-dai kuma taku daya zuwa biyar kawai tayi ta tsaya cak, tare da juyowa ta kalli Salman wanda ya zuba mata idanu baya ko kyaftawa.
Murmushin daya kara bayyana kyawun fuskarta tayi, batare kuma da ta fahimci ma’anan irin Kallon da Salman din keyi mata ba tace.
“Nagode sosai Salman, nagode da taimakonka, tabbas ka taimakeni awannan tafiyar, saboda nasan cewar badon kaiba dana rasa wannan babbar daman dana samu ayau.”
Idanu Salman din ya lumshe, cikin kuma nuna mata girman matsayinta awajenshi yace.
“Akoda yaushe bana buk’atar godiyarki Jannart, domin Ina tabbatar miki da cewar kin wuce haka awajena, kamar kuma yanda kikeson aikinki, haka muma mukeson aiki dake, bamason rasaki Jannart, saboda haka duk wani abu daya shafeki ya shafeni.”
Ya fadi hakan yana mai bayyana iya gaskiyar abunda ke kwance acikin zuciyarsa.
“Bazan iya daina gode maka ba Salman, saboda akoda yaushe kana iya kokarinka wajen bani kwarin guiwa, thanks alot ni zan wuce gida sai munyi waya.”
Ta kai karshen maganan nata tana me juyawa, kaitsaye ta nufi wajen da guard dinta suke.
Shikuwa Salman da idanu ya rakata, har saida ta b’acewa ganinsa, kafun ya juya ya nufi cikin office d’insu.
Yayinda itakuwa tana isa bakin motarta, gaba daya guard dinnata suka mimmik’e, Shashashai duk acikinsu kuwa babu wanda yasan cewar ta fita.
Bud’e murfin motar tayi, bayan ta shiga ta zauna ne kuma driver’nta yaja sukayi gaba, Yayinda sauran guard dinnata suka rufa mata baya.
Kwata kwata kuwa Tafiyar 40 minute ne ta kawosu katafaren gidansu Jannart din.
Inda suna shigowa compound din gidan motar Junaid ma na shigowa.
Ganin motar yah Junaid dinne kuma yasa zuciyar Jannart bugawa da wani irin karfi, lokaci daya kuma taji duk fargaba da tsoro ya lullub’eta.
Tabbas ita kanta tasan cewar tana matuk’ar tsoron Yah Junaid, wanda kuma hakan ya samo asali ne saboda yawan takurawan da yakeyi mata.
Al'kyabban da yake jikinta ta kalla, sanin da tayi kuma cewar idan Yah Junaid din ya gani, zai iya fassarata da wata manufa tasa ta daban, yasa cikin sauri ta zare al'kyabban daga jikinta, tare da sauko da ita ta daura akan waist dinta.
Cikin yanayin tsoro da kuma fargaban dake kwance acikin ranta, ta bud’e murfin motar ta fito.
Hannunta rike da jakanta ta soma tafiya ahankali.
Dai-dai lokacin kuwa Junaid ya fito daga Cikin motarsa, hannunsa rike da karan sigari yana zuk’a tare da tankadi alamun a bige yake yayi tatil da barasa, dishi-dishi yake ganin komai hakan ke sashi tangadin
Idanunsa ya dan kurawa Jannart din, Yayinda yakejin kamar ya rufeta da duka, dan tsananin takaicin rashin samun Galaba akanta da bayayi.
“Daga Uwar Ina kike?”
Ya tambaya cikin kakkausar murya tare da son gano meke daure a kugunta kuma ya kasa.
Jannart kuwa da sautin fitar muryar tasa, yasa hanjin cikinta kad’awa Idanunta ta rumtse, kana cikin muryarta dake bayyana zallan tsoronsa tace.
“Daga wajen aiki nake.”
“Wajen aiki? Munafuka makaryaciya sai yanzune ake tashi daga wajen aikin karfe shida saura?
Makaryaciyar yarinya wato kinje kin gama rabawa kattin banza jikinki kin more sun more, shine sai yanzu zaki dawo ko, tafi daga nan wajen kona tattakaki nayi kasa-kasa dake.”
Ya fad’i maganar amatukar tsawace da maye.
Hakanne kuwa yasa Jannart d’in, Cikin yanayin sassarfa ta nufi cikin gidan kaitsaye, domin tasan ba karamin aikinsa bane yayi kasa kasa da itadin kamar yanda ya fad’a.
Sam tasan baya mutumta duk wani abu nata.
Yayinda akullum take sake ganin wutar mugunta acikin idanunsa.
Duk da kasancewarsa dan Uwanta amma yana muzantata, kwata-kwata babu ruwanshi da cewar ita k’anwarsa ce.
Komai yazo bakinsa furta mata yake.
Harsai yaushe ne zata tsallake rashin mutumcinsa? Harsai yaushe ne Yah Junaid din zai mutum tata amatsayinta na kanwarsa?
Yaushe zai daina gwada mata kiyayya da kuma tozarci?
Wasu siraran hawaye masu zafi ne suka silalo daga cikin idanunta, adai-dai lokacin da ta karasa bakin kofar da zai shigar da ita babban falonsu.
Hannu tasa ta share hawayen nata, kana ahankali ta murda handle din kofar ta shiga.
Rashin ganin kowa acikin falonne kuma yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, batare kuma da ta.
Nemi Mamy ko Abdull ba, kaitsaye ta wuce bedroom dinta.
Tana shiga bedroom din kuwa ta soma rage kayan jikinta, tare da shigewa cikin toilet ta kimtsa kanta.
Koda ta fito kwanciya tayi lub akan gado, tana me tunanin yanda halin rayuwa keyi da ita.
Sam babu wani farinciki da take samu acikin gidan nasu.
Kullum Cikin fargaba da tsoro take, awaje daya kawai takejin dadi, shine wajen aikinta, ananne take yin farinciki batare da wani ya tsangwameta ko ya harareta ba.
Idanunta dake dauke da danshin hawaye ta lumshe.
Kana cikin sanyin murya tace.
“Allah Kazama gatana akoda yaushe.”
*Dr Rayyern Mai-nasara.*
Ajiyar zuciya ya sauke tare kuma da mikewa tsaye, ahankali ya soma tattare tarin takardun dake gabansa.
Bayan ya kammala had’a takardun ne kuma ya d’auki waya da makullin motarsa dake aje akan desktop.
Kaitsaye ya fice daga Cikin Office din.
Koda ya fito compound din asibitin, bai wani tarar da yalwan mutane ba, kasancewar lokacin magriba ta fara yi.
Direct wajen da motarsa ke fake ya nufa.
Bayan ya shiga ya zauna ne kuma yayiwa motar key, tare da cillata kan shumfud’add’iyar Titin dake cikin asibitin har zuwa waje.
Tuk’i yakeyi cike da nutsuwa, Yayinda ahankali kuma yake bin karatun Alminshawy dake tashi acikin motar.
Da fitansa acikin Hospital din kuwa, yanzu ak’alla yakai 18minute, inda kai tsaye ya nufi masallacin Al'furƙan dake Cikin unguwarsu ta Nassarawa G.R.A.
Dab da zai shiga cikin layin masallacin kuwa, ahankali ya d’ago kansa ya kalli madubin dake Cikin motar, kasancewar kuma aikin madubin shine bayyana maka wanda ke bayanka, hakan yasa idanunsa suka gane masa wata bakar mota mai tint dake biye dashi.
Kawar da kansa gefe yayi tare da ci gaba da tukinsa, isowarsa Cikin layin dinne kuma yasa shi shiga wata kwana.
Aikuwa d’aga kan da zaiyi sai yaga wannan motar dake bayansa itama ta shigo kwanan.
Idanu ya d’an tsurawa motar, fuskarsa dauke da mamaki, saboda zuwa yanzu ya tabbatar da cewa motar shi take bi.
“Bibiyata akeyi.”
Ya fad’a fuskarsa d’auke da dan murmushi, ba tare kuma da tsoro ko fargaba ba ya cigaba da tafiyarsa, inda tuni ya d’auki numbern motar dake bayansa din ya rike akansa.
Isowarsa gaban babban masallacin Al'furƙan dinne kuma ya sashi parking motar, tare da bud’e murfin motar ya fito, domin zuwa lokacin an soma kiraye kirayen sallan magriba.
Fitowarsa daga cikin motar ne kuma yasa, motar dake biye dashi din, yin reverse cikin sauri matukin motar da ba a iya ganin fuskarsa, ya Karkata akalan motar zuwa wani waje daban.
Dr Rayyern kuwa ganin wanda yake bibiyannashi ya juya ne, yasa shi sakin Murmushin dake dauke da ma’anoni daban daban.
Wayarsa ya maida cikin motar, bayan kuma yayi alwala da bottle water’n da ya d’auko acikin motar ne, kaitsaye ya wuce cikin masallacin.
Koda aka idar da salla’n bai fito daga cikin masallacin ba saida ya kammala addu’o’insa kana akayi sallan isha'i sannan ya fito.
Daga masallacin Al'furƙan din kuwa kaitsaye gidansu ya nufa.
Yayinda acan gidannasu kuwa Abba da Baba Maud’o ne zaune acikin compound din gidan, inda suke hira cike da girmama juna da Kekkyawar mu'amala.
Dai-dai lokacinnne kuma Rayyern din ya iso bakin tankamemen gate din gidan.
Horn din motar tasa ya danna.
Wanda hakan yasa Baba Maudo tashi da dan sassarfa.
saurin dakatar da Baba Maudon Abba yayi kana cikin girmamawa sanin tabbas Baba Mauɗo ya girmeshi yace.
“A'a Baba Maud’o zauna ka huta, yau bari in taya ni zan bud’e gate din.”
Cike da mamaki Baba Maud’o ya koma ya zauna, ganin da yayi kuma har Abban ya karasa jikin gate dinne yasa shi komawa ya Zauna tare da zuba mishi idanu.
Kana a hankali ya lumshe su tare da sauke nannauyan numfashin.