← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 81

Sashe 41

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr. Sulaiman daya shaida fuskar yarinyar ne ya sharce gumin dake goshinsa, tare da d’auko wani abu mai kaman dutsin guga guda biyu ya manna akan kirjin Jannart din, ganin da yayi batayi motsi bane kuma, yasa shi jin wani irin fad’uwar gaba, saboda sanin da yayiwa abun, sau uku kawai ake dannashi ak’irjin mutum, Idan aka dannawa mutum sau daya, ya farfado ya koma, aka kuma na biyu still bayan ya farfado ya sake komawa, To Idan akayi na uku mutum baiko motsa ba, Lallai alamace dake nuna cewar bashi da rai.

Sake danna mata abun Dr. Sulaiman yayi akan kirjinta, cikin sa’a kuwa yaji taja wani irin numfashi, saidai kuma kafun su ankara numfashin harya koma.

Kallon-kallo sukayiwa junansu, kafun Dr. Sulaiman ya sakeyin shahadan danna mata abun da karfi akan kirjinta.
Wani irin dogon numfashi maikama da shak’uwa taja, tare da mimmik’e jikinta, lokaci daya kuma bugun zuciyarta ya...!

*littafin TUBALI na kuɗine, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU*

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta,
akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki ta karkashi D.H.L. in dai kin cika jakarki baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*

By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 17
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE NE*

*LITTAFIN TUBALI NA KUƊI NE, KI SAYA KI KARANTA BA TARE DA HAKKIN WAHALATA A KANKIBA, SPECIAL GROUP 1K AKWAI KUMA KARAMIN GROUP 500 KACAL A YAWAN POSTING NE BABBANCINSU YAKE, 0661110170 GTBank AYSHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in Kuma baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN! MTN!! Mtn!!! Ki copy number's din sai ki turo min ta whatsApp 09097853276. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭😭😭 Na rokeku da girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenku tsarkin al'ƙur'ani mai girma, kada ki karan littafina in baki SAYABA! In kuma kin saya dan soyyarki da Nabiyi rahamati kada ki rink’a fitarmin da littafina, mutanen dake karanta Audio books da masu posting a wasu wuraren kamar Facebook wattpad da kuyiwa girman Allah da isar mulkinsa da soyeyyarku da manzo mu Muhammad Rasulullah, kada ku taɓa min book har sai da izinina ga number wayata 09097853276, ka/kiyi min mgn ta whatsApp in mun dai-dai ta na lamunce miki/ka sai ka karanta ko ka saka domin wannan littafin dama kab sauran littattafai na hakkin mallakarsa nawane ɗan Allah kiyiwa Allah ba danniba sabida bana ɗin tashin hankali da fitina bare akai ga babin hatsaniya🤗🤝🏻🙏🏻😭😭😭*

_Special Group 1k ƙaramin group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU_

Ya harba ya fara aiki.
Ajiyar zuciya Dr. Sulaiman Dr Fatymah, da kuma Dr. Imran suka sauk’e, tare kuma dajin wani irin farinciki saboda, taimakon da Allah ya basu iko da dama wajen iya ceto rayuwar Jannart d’in.

Dr. fatymah ce ta soma treating duk inda Jannart din taji ciwo, bayan ta kammala ne kuma, Dr. Imran yayiwa Jannart din wasu allurai, wanda zasu taimaka mata wajen samun ingantaccen bacci, da kuma k’warin jiki idan ta farka.

Bayan sun kammala yi mata duk wani abunda ya dace ne kuma, Dr. Sulaiman da kansa ya turo gadon da Jannart din ke kwance, zuwa wani d’aki dake gefen Emergency’n na musamman.

Fitowarsu daga Cikin Emergency room dinne kuma, yasa Barrister Kabir ta sowa, cikin sauri ya nufesu, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Dr. Yaya ya jikin Jannart din? Dan Allah ku fadamin halin da take ciki, kada ku b’oyemin.”

Ya kare maganan yana me hade hannayensa biyu, waje daya alaman roko.

Dr. Sulaiman ne ya dan matso tare da cewa.

“Calm down jikinta da sauki sosai, Domin da taimakon Allah munyi nasaran samo numfashinta, yanzu dai haka tana dakin hutu.”

Wani irin kakkarfan ajiyar zuciya Barrister ya sauk’e, tare da d’aga hannunsa sama cikin matsanancin farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah Nagode ma, Yah Allah ina rokonka da ka cigaba da bawa Jannart kariyarka akoda yaushe.”

Dr. sulaiman kuwa kallon Barrister din yayi, cikin kuma tausasa murya yace.
“Idan babu damuwa zan iya ganinka a office dina, saboda akwai maganar da nakeso muyi.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da cewa babu wata damuwa.

“Dr muje.”

Hakan kuwa akayi inda Dr. Sulaiman ya shige gaba, shi kuwa Barrister Kabir ya take masa baya.

*Alhaji Idi Saleh Dakata House.*

Dr. Lukman ne ya d’ago da kansa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata dake tsaye, fuskarsa dauke da bacin rai da kuma zallan rashin jin dadin abunda ya faru yace.

“Alhaji Idi Saleh Dakata, kana ga abunda k’aninka yayimin yau, ya hanani duba Jannart, bayan yafi kowa sanin cewar nine likitan da yake dubata tun tana yarinya, kana ga fa har tsawa yayimin wai kada nayi kuskuren tab’a ta, har yana cewa wai yasan abunda nake shiryawa takarkashin k’asa.
To Meya sani kenan? Yanaso yace ban iya aikina bane?”

Dr. Lukman din ya tambaya yana sakin hucin iska.

Shikuwa Daddy hannu ya d’agawa Dr. Lukman di, Domin ayanzu kwata kwata baya bukatar jin korafin kowa, abun dake cikin zuciyarsa kawai ya ishesa.

Wani irin numfashi mai zafi ya fesar, tare da d’agowa ya kalli Alhaji Abdu Tababa, da kuma Dr Lukman din.

“Kuje zan ne meku daga baya.”

Yana gama fad’in haka ya juya, zuciyarsa amatukar hasale ya nufi cikin falonsa.

Ganin hakanne kuma yasa Alhaji Abdu Tababa kama hannun Dr Lukman suka shiga mota, bayan maigadi ya wangale musu gate ne kuma, kaitsaye suka fice daga cikin gidan.

Daddy kuwa Koda ya karasa cikin falon nasa, Sam kasa zama yayi, shi d’ayansa yake ta safa da marwa atsakiyan falon, Yayinda ya had’e hannayensa duka biyu awaje d’aya.

Lallai Tabbas akwai aiki babba a gabansa, wanda kuma dole saiya tashi tsaye.

Babban abunda yake tambayar kansa kuma shine, Tayaya akayi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yagane cewar, shine wanda yasa ake bibiyansa?.
Ya akayi ma yasan gidansa, har tsaurin ido irin na yaron ya kawosa?

Tayaya akayi ya yi wannan saken?

“Wani irin shegen yaro ne wannan? Mai tsaurin ido da taurin kai da rashin tsoro?”

Yayiwa kansa tambayar, yana me sharce gumin daya keto masa.

Dai-dai lokacinne kuma Mom ta shigo, cikin falon, hankalinta amatuk’ar tashe, batare kuma da fahimci din da Daddyn yake ciki ba tace.

“Alhaji Ina Jannart d’in, Ina aka kaita wanni hali take ciki dan Allah ku fadamin.”
Chapter 41 · 0% Book details