← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 81

Sashe 38

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kana ya zuba musu ido ta cikin mirror motarsan sabida zuwa yanzu sun dawo bayanshi kusa da motarshi ƙanƙance idanunsa yayi tare da zubasu kan madubin yana kallon duk yadda Junaid ke mata.

Isowarsu bakin motar tasa ne kuma, yasa Junaid damk’o tarin sumar kanta, wanda gaba ki daya ya watse akan gadon bayanta, saboda tsananin wahalan daya bata, irin damk’an da yayiwa fashion nata ne kuma yasa ta sakin wani irin azababben ihu, batare da ko gama rufe bakinta tayi ba, ya bugata da jikin motar.
Wanda hakan yasa Ta fad’a kan motar, atake kuwa jinin dake zuba daga hanci da bakinta ya tsananta ya fara zurarowa har kan motarsa.
Da ƙarfi ya rumtse idanunshi tare da kame jikinsa.
Da yaji zuciyarshi tana wani irin masifeffen harbawa da wani irin masifeffen tsalle kamar zata fito woje.
Dai-dai lokacinne kuma Abba Kabir ya shigo cikin gidan hankalinsa amatukar ta she.

Ashe kuwa baimaga komai ba a tashin hankali ba, saida yaga yanda Junaid din ya buga Jannart ajikin mota.

Wanda hakan yasa ko ihu mai karfi ta kasa fitarwa, ga kuma jinin dake ci gaba da fita ta hancinta ba ƙaƙƙautawa.

Cikin wani irin tashin hankali kiɗima maitsanani Abba Kabir ya nufosu a guje.

Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara wani irin masifeffen tsuma yaji naman jikinshi nayi gaba ɗaya babbar yatsarshi da Jannart ta fasa mishi had’uwarsu ta forko sai wani irin karkarwa takeyi.

Abba kuwa yana gudun nufosu yana.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Junaid! Junaid!! Junaid!!! Baka da hankali ne kasheta zakayi ne. Kai wanne irin azzalumi ne!?”.
Ya ida mgnar yana isa inda suke.
Batare da wani jinkiri ba kuwa ya d’auke Junaid da wani irin gigitaccen Marin da yasa Junaid yayi tagal-tagal ya koma baya,
Cikin tsananin fusata da makatar ido da zuciya yasa hannunshi duka biyu, ya hankaɗeshi, saida ya faɗi ƙasa.
Abu da ɗan giya dama ba ƙarfi ba.

Jikinsa na rawa kana kuma Ransa amatukar bace yace.

“Baka da hankali ne Junaid wannan wani irin dabbanci ne, ko kasheta kakeson yi?”

Abba din ya fada amatuk’ar tsawace.

Tare kuma da sunkuyowa kan Jannart dake kwance akan motar Dr Rayyern jini na ci gaba da fita ta hanci da bakinta.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.
Ya kirata da azaban ƙarfi cikin tarin ruɗani.
Wanda sautin kiranta da yayine yasa Dr Rayyern Mai-nasara buɗe kwayar idanunshi da suka sauya launi daga fari zuwa jazir.
Idon ya zuba musu ta cikin madubin yana ganin yadda Barrister Kabir yake jijjigata a gigice yana mai cewa.

“Jannart Bud’e idanunki nine Abbanki ne yazo bud’e idanunki Jannart!!!”

Barrister Kabir din ya fada da muryarsa wacce tayi rauni sosai, kana kuma yana me dan jijjigata tuni ya gama gigicewa gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi rauni mai tarin yawa ya rufeshi.
Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali.

A dai-dai lokacin ne kuma Rayyern ya bud’e murfin motar tasa ya fito, wanda ya fito ne kuma saboda yiwa Junaid warning, akan jinin daya shafa masa ajikin sabuwar motar sa.
Kana kuma ya sashi ya wonke mishi jinin daya zuba mishi jikin motarsa, in ba wani salon sharri bane yake neman sa dashi.

Barrister Kabir kuwa dake dukufe akan Jannart jin motsin mutum da yayi abayansa ne yasashi saurin juyawa, inda idanunsa suka sauka akan Dr Rayyern Bashi Muhammad Mai Nasara din koda yana cikin gigita ya gane waye ne shi.

Aikuwa azabure ya mike tsaye, batare kuma da wani dogon tunani ba ya kamo hannun Rayyern d’in, cikin muyarsa dake rawa yace.

“Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kalli Jannart jini take ta zubarwa, Dan Allah Kataimaka kada ta rasa rayuwarta.
Dan Allah ka ceceta ka ceci tsohuwar gsky itace hujja ɗaya gareni...”

Yanayin yanda yaji maganar mutumin dake rik’e da hannunsa ne, yasa akaron farko yakai dubansa, ga Jannart d’in dake kwance, kan motarsa jini na zuba mata ta hanci da baki.

Idanunsa ya d’an k’ank’ance saboda, yanda yaga numfashinta na sama da k’asa.
Lallai Tabbas yasan cewa Idan bai taimaka mata ba, To zata iya fad’awa cikin wata matsalar daban kana ya lura wannan mutumin mutum ne mai daraja da Kekkyawar zuciya, a hankali ya kuma kalli yadda hancinta keta zubda jinin haɓo.

Da sauri ya Juya.
tare da kutsa kansa acikin motarsa, cikin sauri ya d’auki wannan bottle water din nasa mai matukar sanyi.
Sabida muryar Barrister Kabir da yaji yana kuka da kiranta.
Da sauri ya juyo ya
K’arasowa kan Jannart din wacce.
Yanzu Barrister Kabir ya ɗagota daga kan motar ya tallabeta a jikinsa yana kiran Daddy.
“Yaya! Yayah Idi !!!”.

Da sauri ya ƙara so gabansa tare da murɗa marfin gorar faron mai masifar sanyin nan.

Kanta da Abba ke tallabe dashi ya saita tare da d’an sunkuyowa ya soma zirara mata ruwa mai bala’in sanyi a tsakiyar akanta.
Yayi hakanne kuma saboda bata taimakon gaggawa sabida yasan idan ya zuba mata ruwan sanyi akanta, Lallai jinin dake fita a hancin nata zai tsaya.

A dai-dai lokacin da yake tsaka da zuba mata ruwanne kuma, Alhaji Idi Sale Dakata, da kuma aminansa da suke cikin babban falonsa suka fito zuwa tsakar gidan, ganin abunda ke faruwane kuma yasa suka nufo kansu gadan-gadan.

Jannart dake kwance akasa kanta bisa cinyar ƙanin mahaifin nata kuwa sanyin ruwan da Rayyern din ke zuba mata ne yasa ta, jan wani irin dogon numfashi, lokacin ɗaya kuma jinin dake zuban ya tsaya.

*Kiyiwa Allah da Manzonsa kada ki fitar min da littafina, in kin San kin sayane dan ki fitarmin da littafina ki gaya min in meda miki kuɗin dan girman Ubangiji ɗayae haliccemu, kada ki karantamin littafina in baki biyaba ganan account na 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp*

Ganin jinin ya tsaya ne kuma yasa.
Dr Rayyern Mai-nasara juyawa sauran ruwan ya zuba a jikin motarsa inda junin yake ya gangara yayi ƙasa.
Kana ya juya ya shiga motarsa tare dayi mata key da danna horn.
Cikin sa'a kuwa Mai gadin ya fara kiciniyar buɗe mishi gate yanayi yana sharce hawayen tausayin Jannart.

Ita kuwa Jannart Lokaci ɗaya kuma gaba daya jikinta ya d’auki karkarwa, take ta soma fitar da wani irin numfashi mai kaman sheshshek’a alamun kuma athsman ɗinta yana tasowa.

Idanu duk suka zuba mata, Yayinda Abba kuwa ya tsaida idanunshi kan ƙirjinta.

Inda yake Kallon yanda bugun zuciyarta ke tayin k’asa.

Adai-dai lokacin da bugun zuciyar nata ya tsaya cak ne, kuma Idanunta suka soma kakkafewa, lokaci d’aya ta saki wani irin nishi’n daya saka Abba firgici.
Dai-dai lokacin kuma k’irjin Dr Rayyern Mai-nasara yayi wani irin masifeffen harbawa.

Take kuwa numfashinta ya d’auke D’ibbbbbb.....

_Dan Allah ba danniba dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenku nace kada ku fitarmin da littafina in kin sayane don ki fitar kiyiwa girman Allah ki gaya min in meda miki kuɗinki, dan Allah kada ki karantamin. In baki biya kuyiwa Allah kada ku watsa min littafina baku san wahalar da nake sha kan rubutun nanba._

BY

*GARKUWAN FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 16
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE NE*

*FREE PAGE sunzo karshe, daga gobe zamu gama FREE PAGE, ki biya ki karanta. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na. Special people group 1k ne karamin group kuma 500 ne, wanda bonus ne wa fan's na, asalin kudin littafin 1k ne saukine ga masoyana in an gama kuwa document 1k ne*

Cikin tsananin tashin hankali, da kuma tsananin rud’ewa, Barrister Kabir ya sanya hannayensa duka biyu ya tallafo Jannart d’in.

“Jannart! Jannart!! dan Allah bud’e idanunki Jannart!!! innalillahi wa inna Ilaihirraju’un! Yaya Idi Jannart ta suma, bata numfashi!!!”

Barrister Kabir din ya fad’a yana me.
Kallon Yayan nasa, wato Alhaji Idi Saleh dakata, cikin matsanancin tashin hankali.

Shima kuwa Alhaji Idi Saleh Dakata'n tashin hankali ne, kwance akan fuskarsa, cikin yanayin rud’ewan da yayi, ya kalli Dr Lukman dake tsaye, tare da cewa.

“Dr. Lukman ka duba mana ita dan Allah.”

Jin hakanne kuwa yasa Dr Lukman dake tsaye, d’an matsowa kusa dasu,
dan duba Jannart din, wacce ita yanzu bata masan duk wata Waina da ake toyawa acikin gidanba.

Idanu Barrister Kabir ya d’ago tare da watsawa, Dr Lukman din muguwar harara, cikin kuma yanayin fushi da tsananin b’acin rai yace.
“Kada kayi kuskuren tab’a min y’a.
Domin kuwa na jima da sanin muguwar cutar da kakeyi mata ta karkashin k’asa.”

Cak Dr.Lukman din ya tsaya, tare da matsawa gefe batare kuma daya karaso wajen ba, saboda jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a.

Barrister kuwa sungumar Jannart din yayi, kaitsaye kuma cikin sauri ya nufi hanyar fita daga cikin gidan.

Da hanzari kuwa maigadi ya bud’e masa dan madaidicin kofar dake jikin gate din gidan ya fice.
Koda ya fito kuwa murfin motarsa na gidan baya ya bude, tare da tura Jannart din ciki ya kwantar da ita.

Batare kuma daya jira komai ba, ya zagaya ya shiga b’angaren driver, ahanzarce ya tada motar, tare kuma da cillata kan titi, kaitsaye yabi bayan motar Dr Rayyern Mai-nasara dake ta sharara gudu, akan shumfud’add’en titin kofar gidan daya mike santa yana mai jin jijiyoyin kansa na tsananta harbawa sabida ihu da hayaniyar da akayi tayi a kanshi .

Shi kuwa Barrister biye dashi yake a hamzarce.
Wanda kuma yayi hakanne saboda sanin matsayin Rayyern da yayi, na likita zai iya taimaka musu.

Yayinda ab’angaren Rayyern kuwa tuk’in motar yake, yana maijin wani irin b’acin rai acikin ransa, badan komai ba kuwa saidan b’ata masa rai da lokaci da akayi agidan Alhaji Idi Salte Dakata, Tabbas yasan cewar.
Koda ace yaje asibitin nasa yanzu, babu wani abu da zai iya aikatawa, Domin yafi kowa sanin kansa Idan ransa na b’ace baya tab’a iyayin komai, koda ma kuma ace yayi din bisa dole, to abun bazai zama hundred percent yanda yake so ba ga kuma alamun ciwon kansa da yake ji.
Chapter 38 · 0% Book details