← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 81

Sashe 2

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin yayi shiru ne yasa ta ɗan kalleshi kana a hankali tace.
"Ba phone number ɗinsane, ba picture dinsa? Ba address ɗin sane?".
MD ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
"Toh Jannart ai da akwai waɗannan abubuwan a ciki, toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba, kunsa duk abinda yake killace shine special."
Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa.
"Babu number sa, ba hotonsa ba adireshinsa. Kana ko akwai number sa, ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 ma-ban-ban-ta bazata shigaba, sabida yana amfani da App ɗin nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane, kiran bazai taba shigaba.
Kuma koda ya ajiye ya shiga, zaki kira a ƙalla sau goma bazai amsaba, sai dai ace mikin ki ajiye mishi voicemail.
Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya ɗaura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma, da yawan mutane suna matuƙar jinjina masa da mmakin kwazonsa, sabida aiyukan sun mishi yawa, kana matashine a tsakiyar dattijai.
To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba.
Sai dai a ajiye mishi saƙo, so nanne zakiji muryarsa, idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne, kuma kinyi hikimar faɗa mishi number ki to shida kanshi zai kira".

Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe.
Cikin karaya Jannart tace.
"My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin?".
Dariya Hajia Rabi'ah tayi tare da cewa.
"Jannart yar jaridar gaske wato, tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina".
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai.
MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta.
Cikin girma Hajia Rabi'ah tace.
"Toh gsky nima wurin PA'nsa na samu wannan bayanin.
Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba.
Akwai ɗan yayata, abokin ƙanin PA'n nashi ne, so nan naji wannan."

Cikin sauri ta miƙawa Hajia Rabi'ah wayarta tare da cewa.
"Samin number ɗan yayar taki".
Murmushi tayi ta amsa tasa mata number.
Kana tace.
"Sunanshi, Mahmoud".
“To” tace kana ta adana number.

Shi kuwa MD'n gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauye-sauyen programs ɗin nasu.

Sai kusan ƙarfe shida saura suka tashi a taron.

Suna fitowa, mafi akasari suka kama hanyar parking lot ɗinsu dan daukan ababen hawansu.

Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito, a take Escort ɗin ta suka miƙe suka mara mata baya.
A hankali ta ɗan juyo jin Aisha Lawal na kiranta.
"Jannart! Jannart!!".
Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka buɗa matan.
Da sauri A'isha Lawal ta iso, cikin sanyi tace.
"Zaki iya?."
Cikin jin tsoron rasa aikinta, ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi.
Tace.
"Na'am A'isha zan iya, in sha Allah. In ban iyaba naci gaba da zaman gida, Yah Junaid zai k’arasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna, wurin aikin nan shine duniyata, shine TUBALIn ɗan y’ancina, ya zanyi sakacin rasa aikina".
Cikin rauni da ƙara yin ƙasa da murya Aisha tace.
"Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya, kuma zai roƙi a baku cikekken dama, da zai biyoki sai ya tuna waɗannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake".
Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima.

Wasu dalla-dallan motoci ne guda, uku.
Ta tsakiya itace a baya.
Ta baya kuma ƴan tsaronta, hakama na gaba.
Tana baya a zaune.
Yayinda driver'n ta ke janta.
A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida, kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta.

Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi, da hayaniya, da kwata kamar ba cikin kano ba, sabida manya-manyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsi-mitsin nan ba.
A bakin wani tamfatsetsen gida mai ɗan karen girma da kyau, suka tsaya tare da danna hon.
Jiki na rawa mai gadi ya buɗe musu.
Nan suka ratsa cikin gidan.

Suna isa parking space ana kiran sallan magriba.
Wanda yayi dai-dai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi.
Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan.
Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota, alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi.
Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Ammina kin dawo kenan".
Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata, cikin sanyi tace.
"Eh Abba na dawo, ina Aunty Dija".
Ta k’are mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez d’in da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa,
Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can ƙasan zuciyarsa yace.
"Suna ciki shiga bari muje masallacin".
Da sauri tace to.
Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci...

*Ethiopia Addis Ababa.*

Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar ɗaukar hankali, matashine mai jini a jika.

Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta, nitsuwa, kamala, haiba, yakeyi, yana mai fitowa habarar wani kyakkyawan Asibitin.
(Tikur Ambess Teaching hospital Addis.)
Yayinda wasu manyan likitocin da ƙasar Ethiopia ke ji dasu ke biye dashi a baya, kana da Nurses.
Taku yakeyi cikin kamala da haiba, a hankali yake motsa lips ɗinshi bisa dukkan alamu, gajiya ce ta sashi hakan ɗin.

Fari ne mai masifar kyau irin farin mutanen ƙasar Ethiopia sai dai fatarsa tana da haske fiye data sauran dake biye dashi a baya bi'ma'ana ya ɗan fisu fari.
Yana da wani irin hanci mai ɗan karen kyau, da tsini, idanunsa masakaita masu masifar kyau da fari, irin idanun nan ne da in sun cicciko da hawaye in akwai abu a gabansu kalar idon kan iya komawa haka, wani irin kekkyawan saje ne mai masifar kyau ne kwance lib a fuskarsa yayi mishi ƙawanya, lips ɗinshi ƴan sirara jajaye masu kyau, sai girarsa masu kyau.
Wani irin askine mai ɗan karen kyau bisa kansa.
Sosai kamanninsa da Dheeraj-Dhoopar suka fito ras hatta tsawonsa da ɗan jikinsa kamar na Dheeraj-Dhoopar ne komansa dai-dai misali.
Daga shigarsa zata nuna wanene shi.
Wani irin masifeffen Suit ne a jikinsa mai ɗan karen tsada, red colour mai maiƙo, riga da wondo sai ɗigon fari-fari, kana necktei ɗin wuyanshi shima fari sai ɗigon ja-ja'n.
Haka takalmanta sau ciki, toms farare ƙira company'n Italy sai harafin R-M da akayi da red color. irin ta matasa. Masu kima da daraja sai agogon hannunsa ƙirar Gucci shima da harafin R.M a gefe da gefe. Shigar tayi masifar mishi kyau da kamala.
Taku yakeyi suna biye dashi a baya.
Har suka iso inda motocinsu ke jere.

*DR. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara kenan.*

Cikin nitsuwa ya juyo yana mai miƙa wa Dr Adeym hannu cikin nitsuwa suka ɗan yi mgna, kana duk sauran ma suka bashi hannu.
Kana ya shiga mota, Driver'n'shi dake ciki yaja.
Suka fita cikin asibitin.
Kai tsaye.
Hera Addis hotel Ethiopian, suka nufa.
A kan hanyarsu ne, suka bi kusa da wani babban masallacin.
Cikin sauƙe numfashi ya cewa, Driver'n'shi.
"Tsaya". A taƙaice
Da sauri yace to.
Kana suka tsaya ganin ya nufi cikin masallacin ne suka fahimci me zaiyu.
Nan suka mara mishi baya, dan yin sallan isha'i kasan cewar lokacin ta yayi daga nan kuma suka wuce.

A hankali ya maida kanshi ya jingine jikin kujerar idonshi ya lumshe tare da motsa lips ɗinshi a hankali yana sauke numfashin gajiys.
Yana jin wayarshi na ringing Amman ko idonsa bai buɗeba sabida tsananin gajiya, kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi mishi, bacci yakeji da kuma yunwa.
Shiyasa bai amsa kiranba.
Sai dai cikin zuciyarsa yace.
"Sulaiman!!!".
Sai kuma ya ɗan mirgina kanshi gefe.
Ganin sun iso.
Da sauri mutanen dake cikin motar dake biye dasu a baya suka fito ɗaya daga cikin sune ya matso.
Buɗe mishi marfin motar yayi kana ya matsa gefe.
A hankali yace.
"Bismillahi".
Numfashin gajiya ya ɗan fesar.
Kana ya zuro ƙafarsa woje.
Sai kuma ya ɗan kalli Usman PA'nshi dake tattaro System ɗin shi da wayoyinshi.
Kana a hankali yace.
"Ɗauko small bag ɗin can."
Da sauri Usman yace. To.
Kana ya ɗauko ɗan jakar leda mai ɗauke da tambarin Edna Mall Addis Ababa Ethiopian. yabi bayanshi suka nufi cikin HOTEL ɗin.
Kai tsaye inda masauƙinsu yake suka nufa.

Suna shiga ya juyo ya kalli Usman daya ajiye mishi kayyakin nasa bisa kujera.
"Sai da safe, bazanci komai ba, kada Sulaiman ya dameka kace zaka zo ka dameni". Yayi mgnar cikin gajiya.
Cikin sauri yace.
"Okay Sir".
Yana mai kunce net ɗinshi yace.
"Toh jeka".
Toh yace tare da juyawa zai fita.
Sai kuma ya ɗan juyo yana kallonshi jin yana cewa.
"Ramadan ya kira ɗazu".
Kai ya gyaɗa mishi kawai.
Ganin haka Usman ya juya ya fita.

Yana ganin ya fita, ya matso ya rufe ƙofar.
Yana juyowa yana cire Suit ɗin, bisa kujera ya cillata, kana ya cire ta cikin.
Sunkuyowa ya ɗanyi yana kunce belt ɗin ƙugunshi.
Yana daga tsaye ya zare wando .

Yana son sakewa shiyasa yake jin daɗin rayuwar kaɗaici.
Sabida yana masifar kunya da suturce surar jikinsa.
Ko dan yanayin halittar jikinsa mai gargasa ne, baya son koda Ramadan ne yaga koda damtsen hannunshi bare sharaɓarsa bare aje ga cinyarsa, da tattausan gargasa yayi masu ƙawanya.
So Amman in shi kaɗaine yana sakewa, wasu lokutan daga falo yake fatali da kayyakinsa kafin ya shiga bedroom ma daga shi sai boxes zai shiga.
Tattare kayan yayi ya wuce dasu Bedroom, bisa gado ya ajiyesu.
Kana ya wuce Bathroom.

Bayan ya fitone ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo iya guiwa farare ƙal.

Turare ya ɗan fesa, kana ya ƙara gudun A'C sannan ya koma parlon ya ɗauko ƴar jakar da yasa Usman ya ɗauko mishi wanda yake cike da chocolates kala daban-daban.
Masu sanyi a daskare.
Chapter 2 · 0% Book details