← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 81

Sashe 76

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan dai suka shiga d’an tab’a hira, Yayinda Riyyam-nsra da Ramadan keta jan Jannart din da hira.

Suna nan azaune kuwa, cikin abunda bai wuce 15mn ba saiga tailorn yazo.

Bayan sun gaisane kuma Mamy ta basa, k’atuwar ledan da ta Ware kayayyakin dinkin aciki, kana cikin sakin fuska tace.

“Fahad ga y’atanan dan Allah kayi mata dinkuna masu kyau, way’anda zasu sake fito da ita sosai, sannan kuma akan kari muke buk’atar kayan.”

Murmushi Tailan da Mamyn ta kira da Fahad yayi, kana Cikin bata girma yace.

“Insha Allahu Hajiya za’ayi mata dinki dai-dai da zamani, kafun nan da sati biyu kuma zaku samu dinkin Insha Allah.”

“Yauwa to Allah yasa, yanzu za’a baka size dinta ne, ko zaka gwada ta?”

Mamyn ta fad’a tana me Kallon Jannart da kanta ke sunkuye.
Kanshi ya ɗago ya ɗan kalli Jannart kana yace.
“A’a basai na gwada taba, ai naganta kuma Insha Allah zanyi mata komai yanda ya dace.”

Fahad din ya kare mgnar yana sake harhad’a kayan waje daya.

Mamy kuwa kaita jinjina cike da gamsuwa tace.

“To nawa ne kudin dinkin naka.”

D’anjim Fahad din yayi, saboda shi kansa baisan nawa zaice ba, kasancewar kayan suna da yawa, dole sai ya nutsu ayi total tukunna.

Fahimtar hakanne kuma yasa Mamy mik’ewa tsaye, tare da cewa.

“Kad’an jirani inazuwa.”

Kaitsaye sama ta haura, tana shiga cikin falon saman kuwa ta hango Rayyern zaune, ya daura kafarsa daya kan d’aya, Yayinda idanunsa kuwa ke lumshe, sai kuma goran swan dake rike a hannunsa.

“Rayyern.”
Mamy ta kira sunansa.

Jin sautin muryar Mamynnasa ne kuma yasashi bude idanunsa.

Tare da gyara xamansa yace “Mamy.”

“Na’am tunanin mekakeyi?” Mamyn ta tambaya cike da kulawa.

Kansa ya dan juya, kana cikin sanyi yace.

“Babu komai Mamy, kawai dai nagaji ne.”

“Da kyau.
dama kudin dinki nazo karb’a awajenka, yanzu na kira taila kuma yazo, zai tafi da kayayyakin da muka sayo zaije ya dinkosu.”

Mamyn ta fad’a tana me tsaresa da idanu.

Wanda hakanne kuma yasashi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, kana akasalance yace.

“Eyyah Mamy ai duk kun kwashemin y’an kud’ad’ena, kuma fa bana da wani kudi sosai, sannan ba atm dina yana hannunku ba naga shima yadda kuka yasheni kamar ba gobe.”

Murmushi Mamy tayi, saboda tasan maganar cewa ma bashi da kudi ba gaskiya bane.
Sai dai al'adarsa ce bai cika son almobazaranci ba, yana fadin hakanne kawai saboda kaucewa mgnar da suke ta lika mishi

“Cash mukeso yanzu ba wai transfer ko wani abuba, tailor ne yazo, ko atm card din kakeso mu bashi yaje ya cire?”

Cewar Mamyn.

Rayyern kuwa da sauri ya kalleta tare da cewa.
“Atm card na din zaku bawa wani, uhumm lallai Mamy abun ya magaga”. shi bawai kudin bane bayason bayarwa, a'a kawai dai shi ayanda aka lika masa auren ne baiso ba, saboda dama yasan dolene sai antakurasa akan hakan.
Ita kuwa Mamy ido kawai ta zuba mishi.
Mik’ewa tsaye yayi, tare da nufan d’akinsa, kaitsaye gefen bedside drawernsa ya nufa, Koda ya ya karasa bud’e drawern yayi ya d’auko, bandir din kudi, Rafa daya inda kuma kowani Rafa daya 50k ne.

Juyowa yayi ya dawo falon, tare da damk’awa Mamyn kudin.

Cikin shagwab’a da kuma turo baki yace.

“Mamy gashi yanzu a barni in huta ko. Kuma a kamo min ATM na kin san Ramadan ba mutuncine dashi ba, in ya samu kudi.”

Karb’an kudin Mamy tayi, batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin.

Koda ta sauko kasa, duka 50k din ta bawa Fahad.

Da ya tashi tafiya ne kuma ta had’ashi da Hadi ya kaisa har zuwa babban shagonsa.

Sauran kayan da suka rage din kuwa, Mamyn da kanta ta Taya Jannart suka shigar dashi, can cikin bedroom din Jannart din.

Cikin kulawa kuma haka Mamyn ta Taya ta suka shirya duka sauran kayan acikin wardrobe, kayan shafa kuwa anan kan dressing mirror Jannart din ta jere su.

Bayan sun kammala komai ne kuma, suka sake dawowa nan cikin main falon.

Zama sukayi inda Riyyam da Ramadan kuwa suka shiga sana’arsu ta buga game, ganin yanda Game din ke dadi ne kuma yasa, Jannart maida gaba daya hankalinta garesu.

Mamy kuwa kallonsu take fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi, saidai kuma ganin yanda hankalinsu duk ya tafi akan game dinne yasa, ta mik’ewa.
Anutse ta nufi sashin Abba.

Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, bakinta dauke da sallama.

Abba dake rike da wani littafi na Tafsir, ne ya amsa mata sallaman tare da d’ago kansa ya kalleta.

Itakuwa Mamy fuskarta dauke da murmushi ta k’arasa shigowa cikin falon, cikin muryar dake nuna tautasawa tace.

“Allah yasa bankatseka daga abunda kakeyi ba.”

Murmushi Abban yayi, cikin fadada fara’ar dake kan fuskarsa kuwa yace.

“Sam baki katseni ba, kamar kinsan cewar kuma dama ina nemanki.”
Abban ya fad’a yana me jawo wata leda dake gefensa.

Mamy kuwa k’arasowa inda yake zaunen tayi, tare da durkusawa ta zauna agabansa.

Abba kuwa Ledan dake hannunsa ya mik’a mata, atausashe yace.
“Waya ce wannan d’azu na sayowa Jannart ita, ki kai mata, duk na sha’afa shiyasa d’azu da kika shigo ban baki ba.”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mamy, cikin farinciki kuma tace.

“Kai Masha Allah, amma gaskiya Jannart zataji dadin hakan, Allah ya kara bud’i.”
Mamy ta fad’a tana amsar ledan.

“Ameen.” Abban ya amsa, Yayinda ita kuwa Mamy ta mik’e, tana fad’in.
“Bari nakai mata wayar na dawo.”

Abban kuwa Kai ya jinjina alaman “To.”

Haka Mamy ta fito daga sashin Abban fuskarta d’auke da murmushi, ta karaso nasu sashin.
Har yanzun kuwa su Jannart na zaune.

Akusa da Jannart din Mamyn ta zauna, kana cikin tausasawa tace.
“Jannart ga sak’o inji Abbanku.”

Jin hakanne kuma yasa Jannart, d’ago Kai ta kalleta, tare kuma dasa hannayen ta bibbbiyu ta karb’i ledan, da Mamyn ke mik’o mata.

Ahankali ta warware ledan, tare dasa hannunta ta zaro kwalin dake cikin ledan.
Idanunta ta d’an zaro waje, saboda Ganin kwalin waya da tayi, kirar Samsung Galaxy S21 ultra.

“Wow Samsung galaxy S21 ultra, gaskiya Abba yanaji dake Aunty Jannart.”
Riyyam-nsra ya fad’a, Cikin nuna jin d’adinsa.

Jannart din kuwa, itama tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskarta, wanda saboda jin dadin kyautan da tayi ne kuma yasa, har hakwaranta suka bayyana alokacin da take murmushi.
Cikin tsananin jin dadi, da kuma nuna yaba kyautar da Abban yayi mata tace.
“Nagode sosai Mamy Allah ya kara arziki, ya kuma kara rufa asiri, Allah ya jik’an magabata.”

“Ameen Ameen Jannart, ba komai ai duk yiwa kaine, yanzu ke tamuce komai mukayi miki basai kinyi mana godiya ba.”
Mamy ta fad’a ciki kulawa.

Jannart kuwa rungume wayartata tayi, cikin jin dadi da kuma duk’ar dakai tace.

“Mamy nagode sosai, kuma inason yiwa Abba godiya.”

“Bakomai Jannart, taso muje to sainayi miki iso zuwa wajennasa ko.”
Cewar Mamy tana me mik’ewa tsaye.

Ganin hakanne kuma yasa Jannart itama mik’ewa tsaye, tabi bayan Mamyn, Yayinda tabar wayar nata awajen Ramadan, wanda tuni harya cirota ya kunna, domin shikansa wayar tayi masa kyau.

Mamy kuwa ahankali ta murd’a handle din kofar falon Abban, tare dasa kanta ciki, hakanne kuma yasa Jannart dake biye da ita, itama ta shiga bakinta dauke da sallama.

Abba dake zaune kuwa, ganinsu ne yasashi fad’ad’a fari’arsa, cikin sakin fuska yace.

“A’a Jannart.”

Murmushi Jannart din tayi, tare da k’arasowa dan nesa da Abban, ta durk’usa tare da zube guiwowinta ak’asa, kanta ta duk’ar k’asa, cikin muryar dake nuna girmamawarta agaresa tace.

“Abba naga waya, nagode sosai, Allah ya kara budi da arziki, ya jikan magabata.”

“Ameen summa Ameen Jannart, idan kina buk’atar wani abu ki sanarwa Mamynku, kinji kada kiji nauyi ko kunyarmu, muba iya surukanki bane kawai mu matsayin iyaye muke a gareku.”
Abban ya amsa, yana murmushi.

Itama Jannart din murmushi tayi, tare da mik’ewa cikin sakin fuska, ta fice daga cikin dakin.

Direct falo ta dawo, zama tayi akan sofa, tare da karb’an wayan nata ta soma dud dubawa.
Sosai wayar tayi mata kyau, musamman da colourn wayan ya kasance bak’i.

Hira suka dan tab’a dasu Ramadan, din kafun daga bisani ta tashi ta shiga ciki.
Kasancewar tana danjin gajiya ajikinta ne kuma yasa, kaitsaye toilet ta wuce tayi wanka.

Bayan ta fito ne kuma ta shafa, daya daga cikin mayukan da Mamy ta seyo mata, tare da binjikinta da Body spray mai dadin kamshi.

Direct wardrobe dinta ta bud’e, daya daga cikin dogin rigunan da Mamyn suka sayo mata ta saka ajikinta, kamar kuwa tun can dominta akayi rigar, saboda yanda rigar ta zauna mata d’as ajiki.

Dai-dai lokacin kuwa aka soma kiraye kirayen sallan la’asar, kasancewar kuma tayi alwala tun acikin toilet shiyasa kawai hijab dinta ta zura tare
da tada sallan, bayan ta idar ne kuma ta kwanta.

Acan cikin gidan kuwa Rayyern tunda ya shiga daki baifito ba, sai yanzu da yaje yayi sallan la’asar, still kuma sake dawowa gidan yayi, tare da komawa daki yayi kwanciyarsa, kasancewar yau din weekend ne shiyasa yakeson morewa hutunsa.

Su Ramadan kuwa Koda sukayi sallan la’asar, cikin gari suka kutsa shida Riyyam.

Haka dai sukayi wunin wannan ranar.
Mamy na mai jan Jannart a jiki sosai, ba laifi kuma ta ɗan sake.

Washegari

Acan gidan Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, tashin hankali kam sun shigesa k’arara sun wuni sun kwana cikinsa, musamman awajen Alhaji Idi Sale Dakata, dako zaman kirki ya kasa yi, hankalinsa amatukar tashe yake, badon komai ba kuwa, face sanin da yayi cewar, b’acewar Jannart babban tashin hankalinsu ne, haka kuma kaman wani kalubale ne dake fuskantarsu, wanda ba zasu tab’a iya tsaidashi ba kwana yayi baiyi bacciba a wannan daren.

Mom kuwa tayi hawaye har saida idanunta suka bushe, gaba daya ta shiga damuwar rashin Ganin Jannart din, Yayinda duk wani zarginta ta d’aurashi akan Junaid, saboda sanin da tayi cewa, ba k’aramin aikinsa bane sace Jannart din.

Abdull ma gaba daya haka yayi wuni jiya ya kwana yau kuwa tun da safe ya gayawa Yah Azeez abin da ake ciki.
Abinda yayi masifar tada hankalin Azeez kenan. saboda b’atan ƙanaartasa ya daki zuciyarsa sosai.
Chapter 76 · 0% Book details