← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 81

Sashe 77

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kuma yau ɗin ma gari na wayewa Alhaji Idi Sale Dakata ya fita, da kansa ya dinga zaga gari waiko zai samu wani labari amma Ina.
Daga karshe dai haka ya dawo gida zuciyarsa duk ba dadi.
Har dare kuwa babu wani labari akan Jannart din.

Yayinda Barrister Kabir kuwa ya buwayesu da zurya da tashin hankali.

Acan gidansu Rayyern kuwa ana idar da sallan isha'i Ramadan da Riyyam suke dawowa gida.
Mamy kuwa bayan ta kammala dinner, har d’aki ta kaiwa Jannart nata zaune ta sameta bisa sallaya tasa hannunta duka biyu ta tallabe h...!

By
*GARKUWAR FULANI*

Habarta tana lallatsa wayarta.
Cikin sauri ta ɗago kanta jin motsin Mamy.

Ita kuwa Mamy ajiye mata tray'n tayi gefenta tare da cewa.
“Ki ajeyi wayarnan haka, kizo kici abinci.
Ga tea kisha da zafinsa mgnin wannan sanyin da akeyi mana”.
Cikin girmamawa tace.
“Toh Mamy sannu ngd”.
Kai ta jinjina kana juya ta fita.

Kasancewar kuma yanayin garin ana busa sanyi mai masifar ratsa jikine, yasa su Mamyn ma basu wani jima afalon ba, suna kammala diner din, kowannensu ya wuce dakinsa.

Rayyern kuwa dama ko saukowa k’asan baiyi ba, abincinsa ma sai Mamy ne tasa Riyyam ya Kai masa daga nan ya zauna gefenshi yanata zuba mishi surutu.
Nan ma baiwani ci sosai ba sabida ya rigada yaci Chocolate ɗinsa shi yasa Riyyam din ya fita dashi.

Duk da cewar yanajin bacci kuwa, bai kwanta ba harsaida ya motsa jikinsa, na kusan tsaeon 1 hour kafun ya kwanta.
Cikin yan mintuna kadan kuwa bacci ya daukesa, saboda duk garin ya dauki sanyi sosai.

Acan b’angaren Jannart ma, da wuri ta kwanta, tare da shigewa cikin lallausan blanket dinta, tana rik’e da wayarta kuwa bacci ya dauke ta.

Washegari.

Kamar kullum kuma Koda yaushe, dukansu atare suka dawo daga sallan Asuba.

Inda suna shigowa kuwa Mamy ta tarbesu da hadin Coffee dinta, mai dadi.

Bayan sunsha ne kuma duk suka miƙe suka wuce sama dan sake kwanciya, Mamy kuwa kaitsaye kitchine ta wuce.

Tare da soma shirye shiryen had’a musu breakfast.

Tana cikin aikin nata ne kuma, Jannart ta fito zuwa main falon.

Sanye take da Hijab ajikinta, Jin motsi acikin kitchine dinne kuma yasa ta, nufar kitchine din kaitsaye saboda tana da tabbacin cewa Mamy ne.

Mamy kuwa dake tsaye, Jin alaman tafiyan mutum ne yasa ta Juyowa da sauri, dai-dai lokacin ne kuma Jannart din ta k’araso bakin kofar kitchine din riƙe da mug din coffee da Mamy ta kai mata.

Murmushi Mamy tayi, tare da fadada fara’ar dake kan fuskarta, atausashe tace.

“A'a Jannart da sanyin safiyar nan me kika fito yi?.”

Kai Jannart din ta jinjina, cikin girmamawa kuwa tace.

“Mamy aikin zamuyi.”

“Da wannan sanyin, a jeki kwanta?”
Mamyn ta fada tana murmushi.

“A'a Mamy aiki da yawa ai bari na tayaki.”
Jannart din ta fad’a tana me k’arasa shigowa cikin kitchine din.

“A’a Jannart ki bar aikin nan ba damuwa, jekiyi kwanciyarki kinga ana sanyi, kuma yau dinma bawani aiki mai wahala zanyi ba, abinci mai sauki zan dafa.”
Mamyn ta fada mata haka cikin kulawa.

Hakanne kuma yasa Jannart din ta d’an langwabar da kai, murya asanyaye tace.

“Dan Allah Mamy ki bari na tayaki, banajin bacci shiyasa.”

Murmushi Mamyn tayi, Ganin kuma Jannart din ta dage ne yasa ta, matsawa gefe tare da cewa.

“To ga Irish patatoes nan ki fere, ni bari na k’arasa had’a wannan farfesun, Idan kika gama saiki soya mana chips ko.”

Kai Jannart din ta jinjina, alaman to, Cikin nutsuwa kuma ta d’auki abun fere dankalin ta somayi.

Cikin abunda bai wuce mintuna kad’an ba kuwa ta kammala, da kanta ta kunna gas, tare da soma soya chips din, suna dan hira da Mamy harta gama.

Wanda zuwa lokacin tuni Mamy ta gama had’a ferfesun, harta fara soya kidney sauce din da za’aci chips din dashi.

Ganin hakane kuma yasa Jannart, had’a musu had’adden sandwich, sai kuma green apple juice wanda acikin mintuna 15 kwata kwata ta kammala had’a shi.

Sosai Mamy taji wani irin farinciki ya cika mata zuciya, musamman saboda yanda taga Jannart din na taimaka mata da ayyuka batare da ganda ba, aikin da zatayi acikin 2hour sai gashi, da taimakon Jannart sunyi shi, acikin awa daya da yan mintuna.

Bayan sun kammala had’a breakfast dinne kuma, Jannart da kanta ta kwashe abincin ta jeresu akan dining table, Yayinda Mamy kuwa ta kwashi food flask din da aka sawa Abba abincin aciki Ta kai masa zuwa sashinsa, sai kuma nasu Baba Maud’o, wanda sai gari yayi haske za’a Kai musu.

Duk wani abu da suka b’ata kuwa saida Jannart din ta wanke, bayan ta gama kimtsa komai ne kuma Mamy ta kalleta, murya atausashe tace.

“Allah Ya miki albarka Jannart, yanzu kije kiyi wanka saiki zo muyi breakfast ko.”

“To Mamy.”
Jannart din ta amsa, kana anutse ta juya ta nufi part dinta.

Koda ta shiga cikin bedroom dinta, kayan dake jikinta ta cire, wani sabon towel ta daura, kaitsaye kuma ta shige Bathroom tayi wanka da ruwa mai ɗan karen ɗumi sabida yanayin ciwonta yafi tashi a irin lokutan sanyin haka.

Koda ta fito feshe jikinta tayi da turare mai sanyin kamshi, bayan ta murzawa jikinta mai ne kuma, ta shafawa fuskarta powder, sai kuma wani brown lipstick da ta gogashi sama sama akan labb’anta, dama kuma ba al’adarta bane yawan kwalliya.

Wani dogon riga mai kaman Kimono ta zaro, tare da sakawa ajikinta, d’as rigan ya mata ajiki, kasancewarsa Maroon color kuma shiya kara bayyana kyau da hasken fatarta.

Dogon gashinta ta tubke atsakiyar kanta, tare kuma da d’aukan mayafin rigar ta yafa akanta, wanda ya sauko harzuwa kan kirjinta.

Alokacin da ta kalli madubi kuwa, murmushi tayi saboda ita kanta tasan tayi kyau.

Agogo ta kalla, wanda yake nuna mata karfe Takwas harda wasu mintuna.

Wasu lallausan takalma flat ta saka ak’afafunta, cikin yanayinta na nutsuwa kuma ta bud’e kofar dakin ta fice wayarta na rik’e a hannunta.

Kaitsaye Falon Mamyn ta fito, fitowar nata kuwa yayi dai-dai da fitowar su Ramadan da Riyyam.

Riyyam ne ya kalleta tare da k’arasowa, inda take Cikin sakin fuska yace.

“Barka da safiya my kyakkyawar Aunty na, gaskiya Hamma Rayyern yayi dace, Yah Allah Nima kabani kyakkyawa mata.”

Lallausan murmushi ta sakar masa, tare da yin k’asa da kanta, cikin dakekkiyar murya tace.

“Barka da safiya Tiktoker Riyyam.”

Dariya Riyyam din yayi, Yayinda Ramadan da sai yanzu yake k’arasowa, shima fadada fara’ar dake kan fuskarsa yayi, cikin kulawa yace.

“Barka da safiya Aunty Jannart fatan kin tashi lafiya.”

D’agowa tayi fuskarta dauke da murmushi ta kalli Ramadan din, kamar yanda yayi mata magana a mutunce kuwa haka itama ta mayar masa.

Dai-dai lokacin kuwa Mamy ta fito daga sashin Abba.

Riyyam kuwa Wayarsa ya zaro, tare da Kallon Jannart din, cikin kulawa yace.

“Hamma Ramadan Aunty Jannart kuzo na d’aga mana selfie, Mamy kema ki shigo.”

Murmushi duk sukayi, Mamy kuwa Kanta ta girgiza, fuskarta dauke da dariya tace.

“A’a nikam kudai kuyi selfien ku.”

Tsayuwa sukayi inda suka saka, Jannart din atsakiyarsu, Riyyam din kuwa shiya d’aga musu wayar yayi musu selfie, har kala uku.

Bayan sun gama ne kuma Mamy tace.

“To saiku zo muyi breakfast ko.”

Kai suka jinjina dukansu, tare da karasawa dining table din suka zazzauna, Jannart da kanta tayi saving nasu.

Bayan sun fara cin abincinne kuma, Riyyam-nsra ya ciro Wayarsa tare, da turawa Mamynsa hotunansu da sukayi yanzun, Ganin Mammyn bata online ne kuma yasa shi danna voice, batare kuma daya gama cinye abincin dake bakinsa ba yace

“Good morning Mammyna, ga amaryar Hamma Rayyern dina kiganta, she’s so cute Mammy kisa mata al'barka, kiyi musu addu'a'n zaman lafiya da samun yan tagwayen yara.”

Yana gama fadin haka yayi sending voice din, tare da ajiye wayartasa ya cigaba da cin abinci.

Mamy da Ramadan kuwa murmushi kawai sukayi, saboda sun San yanda Riyyam yake matukar kaunar mahaifiyarsa sun fahimci duk motsinshi sai ya sanar mata.

Jannart kuwa jin abunda Riyyam din ya fad’ane yasa ta sunkuyar da Kanta k’asa, acikin zuciyarta kuwa ta maimaita abunda Riyyam din ya fad’a.

“Amaryar Hamma Rayyern kiyi musu addu'a'n samun yan tagwaye.”

Ya tabbata kenan cewa, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne mijinta.
Saboda shine kad’ai Rayyern din da tasani acikin gidan, shi dinne kuma wanda suke cewa Hamma Rayyern shine kuma mutumin da baimin mgn in na gaidashi ma bai amsawa ko yaushe fuskarshi kamar ta Yah Junaid.

Share duk wani tunanin dake zuciyar nata tayi, tare da ci gaba da tsakalan abincinta tana ci.

Mamy kuwa ganin Rayyern baisauko ba, yasa tayin tunanin ko bacci yakeyi, shiyasa bata tura ankirasa ba.

Atsanake haka suka kammala breakfast din, dukansu kuma cikin falon suka dawo suka zauna.

Inda Riyyam-nsra keta basu labarai kala-kala, wanda duk mafi yawansu akan TIKTOK ne.

Acan b’angaren Abba kuwa yana kammala yin breakfast d’insa, ya kimtsa tare da bud’e kofar falon nasa ta bangaren baya ya fice, hannunsa rike da key din mota, saboda akwai inda zasuje da Baba Maud’o.

Fitowarsa compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da shigowar motar Barrister Kabir.

Ganin motar Barrister Kabir dinne kuma, yasa Abba sakin murmushi, tare da dan tsayawa.

Barrister Kabir kuwa yana gama dai-dai-ta parking din motar ya bud’e murfin ya fito, Fuskarsa dauke da murmushi.

Karasowa yayi tare da bawa Abban Hannu suka gaisa.

Cikin sakin fuska Abban yace.

“Barrister ashe kana tafe, sannu da zuwa, mu isa daga ciki.”

Kai Barrister Kabir ya jinjina, tare da cewa.
“To bari na gaisa da Baba Maud’o.”

Ya k’are maganan yana me mik’awa Baba Maud’o hannu sukayi musabaha.

Bayan sun gaisa da Baba Maud’on ne kuma Abba Yayi masa jagora zuwa cikin gidan.

Ta babban kofar falon kuwa suka shiga, wanda dai-dai lokacin kuwa su Jannart duk suna zaune akan sofa, ita dasu Ramadan.

Da Sallama abakinsu suka kutsa Kai Cikin falon.
Jin sautin muryar Barrister Kabir ne kuma yasa Jannart saurin d’ago kanta.

Ganinsa dinne kuma yasa Murmushin jin dadi bayyana kan fuskarta.

Shima Barrister Kabir din murmushi yayi, tare da karasowa cikin falon ya zauna.

Mamy kuwa da murmushi akan Fuskarta tace.
Chapter 77 · 0% Book details