← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 81

Sashe 58

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Hakan ba wata matsala bace ai, Domin bani da yakinin cewa yin hakan zai tauye musu hakkinsu”.
Da sauri ta kuma cewa.
“Toh kuma kake bada shawara a rushe asibitocin?”.
Wani irin kallo ya ɗan watsa mata.
Sabida ta mishi tambayar cikin gajin haƙuri irin nasu na ƴan jaridu.
Dan bata tsaya taji ya dasa Ayaba.
Koda yake haka suke.
Yan jaridun suna jin daɗin jefowa mutun tambaya kamar sauƙawar aradu ko kuma titsiye.

Cikin tsare fuska yace. “Dama meyake sawa su bude nasu asibitotin?”.
Ya mata tayarma tare da tsareta da ido.
Yar-yar haka taji tsikar jikinta na tashi.
Haka yasa da sauri ta kauda kanta gefe.
Shi kuwa kai ya jin jina tare da cewa.
“Baki sani bako?
To bari in gaya miki...”
Ya kare mgnar yana mata hararan ƙasan ido kana yaci gaba da cewa.
“Dama rashin samun isasshen abunda zasu rufawa kawunansu asirine, saboda sometimes acikin asibitotin Gwamnatin, gwamnati bata biyansu al'bashi akan kari, baya ga haka kuma bata basu isassun al'bashin da zasu dauki nauyin iyalansu sabida gwamnatin tayiwa malaman jinya dana makarantu riƙon sakainar kashi Alhamdulillah gwarama wannan gwamnati da muke ciki.
Duk da haka ana buƙatar ƙari.
Domin duk lokacin da Gwamnati ta fara biyansu isassun al'bashi, To ba wani abu da zaisa suje su bude privet Hospital toh ko sunje sun buɗewama wa zai je musu in dai asibitocin gwamnatin nada inkanci , Domin ak’asarnan ba yawan asibiti muke da bukata ba, ingancinsu kawai shine abun buk’atar mu, tayanda talaka da maikudi da fulanin daji zasu samu gamsashshiyar kulawa, batare da nuna wani banbanci ba!!!.”

Ajiyar zuciya Jannart ta sauk’e, kana kuma cikin yanayin nutsuwa tace.

“Mungode sosai Dr. inafatan kuma Gwamnati zataji shawarar daka bada kuma tayi aiki dashi, yanzu kuma zamu shiga babi na biyu. wanda ya shafi b’angaren kasuwanci kafin mu dawo nan a likitance.

Yah Salam shine abinda ya faɗa a ransa.
Sabida ya lura yau bakinshi sai yayi tsami sabida magantuwa da wannan fitinenneyar yarinyar take sashi.
Kamar a tsakiyar kanshi yaji ta kuma cillo mushi tambaya.
“Shin Dakta wacce irin shawara zaka bayar, agame da yanda sha’anin saye da sayarwa ya zama acikin k’asarnan, misali ta yanda ayanzu kayan abinci yayi tsada sosai, akullum wasu daga cikin yan kasuwa k’ara farashin kayansu suke, rayuwa tayiwa talaka tsada, manyan y’an kasuwa da kamfanoni sun had’e kai da baki waje daya, Koda yaushe farashin kaya hauhawa yake, tayaya ne za’a samawa al’umma sauk’i, musamman manoma, wanda sune ma suke noma abincin amma kuma Idan ya shigo kasuwa sai yazo yafi karfinsu, shin wacce shawara zaka iya bawa manoma?.”

Numfashi ya dan fesar ta bakinsa, saboda yanda yaji labbansa sun soma gajiya da yawan motsasu da yake.

Hakanne kuma yasa batare daya dago ya kalli ko cameran ba, saidai atausashe yace.

“Shawarar da zan iya bawa Manoma itace, duk wani manomi Idan har ya noma abunda zaici, To kada yayi gangancin saidawa, har sai ya tabbatar daya ware ishashshen abincin da zai isheshi, har na tsawon wata shekarar da zai sake noma wani abincin, kafun nan sai yazo ya saida wanda zai sayar, saboda gudun kada ayi gaban mai haƙar rijiya. kai ka noma ka gama shan wahala, sannan kuma ka tattara ka sai dashi lokacin da yake araha, bayan y’an wasu watanni sai yayi tsada, ga kuma wanda kake dashi ya riga ya k’are ga damuna ta sako sama ruwa ƙasa ruwa, fita nemowar ma wata rana sai ya gagara, kaga kenan nakan daka saida shi zaka sake zuwa ka saya, akan farashi mai masifar tsada, kenan Kai Manomi kaine ka wahala a banza.
Sannan kuma ya kamata manyan kamfanoni su dinga tausayawa talakawa, su daina yi musu irin wannan hawan k’awaran, zuwa su sai abincin manoma tun yana gona basu shigo dashi gari ba su kuma manoma ku farga da wannan sagegeduwar da akeyi muku.
Sannan kuma su manoman kansu, su daina sayarwa masu manyan kamfanoni abincinsu tun yana gona, saboda wasu tun abunda suka noma yana yabanya suke saida shi, atunaninsu ko da ace abun da suka noma din baiyi kyau ba ko sanadin fari ko tsuntsaye ko kwari ko tsutsa, su dai sun samu kudi, da yawan mutane basu san al'barkar dake cikin kayan gonansu ba, saboda haka yana da kyau, ka dinga girbe abunka kana gyarawa da kanka, ka kididdige abinda ka samu ka ware na buƙatunka kafun ka mik’ashi ga wasu, sannan kuma duk wani manomi yayi kokarin saida abincin daya noma, akan farashi mai kyau, saboda ko yaya guminsa ya keci.
Domin shi kadai yasan wahalar daya sha wajen noma ta, sannan yanzu Idan akayi dubi, gaba daya manoma da talakawa su suke shan wahala, musamman Idan aka shiga cikin damuna, haka komin ruwa da iska zasu tsaya neman abunda zasu rufawa kansu asiri suyi noma dan ciyar da al'umma duk kudinka fa, in manomi baiyi noma koda kuɗin ka bazaka samu abincin ba, shin zakaci kuɗin naka ne!!!?. Sannan ku kuma y’an kasuwa da kamfanoni masu karawa kayan abincinsu kudi, ba komai kuke ciba face *RIBA* haramtacciya, wanda kuma kowa yasan hakan ba abubane mai kyau bane, ga wanda suke sayan abinci su b’oye sai yayi tsada su fito dashi, suma duk Allah naganinku, kuma Allah da kansa baya tausayawa wanda baya tausayin na kasa dashi.”

Kai gaba daya mutanen dake boye abayan cameras din suka jinjina, hatta MD da kansa shima ya samu cikakkiyar gamsuwa da bayanan da suka fito daga bakin Dr. Rayyern din.

Ba kuma a iya cikin tv station din ba, har acikin gaba daya k’asar tamu, mutane da yawa dake Kallon Live Program din sun samu cikakkiyar gamsuwa, Yayinda kalaman Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya ratsa zuk’atansu, ciki kuwa harda mafiya yawan manoma da suke kallon shirin, sabida Tashar Arewa 24 TV tayi zarran birni da ƙaune suna kallonta maza da mata manya da yara.

Adai-dai lokacin kuma Abba Kabir zaune yake agaban tv yana Kallon shirin, shi kansa ya gamsu da kalaman Dr. Rayyern din, saidai kuma sosai zuciyarsa ta cika da tsananin mamakin, ganin da wanda Jannart din ke hira yau.

Acan babban falon gidansu Jannart din kuwa, Alhaji Idi Sale Dakata, Dr. Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa ne, zaune sun zubawa babban TV plasma din dake cikin falon idanu.

Wanda kuma yanzun akayi musu kira na musamman, akan su kunna tashar Arewa24 Dan Ganin hirar da akeyi da Dr.Rayyern din.
Hakance kuma ta kasan a wurare da dama yadda wasu ke kiran wasu manyan ƙasar suna shaida musu su kunna tv tashar Arewa 24 TV suga program ɗin da akeyi da Dr Rayyern Mai-nasara.

Jin abubuwan da Rayyern din ya fad’ane kuma, yasa Alhaji Abdu Tababa yin k’wafa, kana cikin takaici yace.

“Amma dai wannan yaron anyi d’an iska, mai tsaurin ido, kujifa abunda yake fad’a, wai gwamnati ta rushe asibotin kudi ta inganta nata, Lallai yaron nan bashi da tsoro.”

“To shi nashi asibitin na uban meyene, shegen yaro mai jajayen kunnuwa.”

Cewar Dr. Lukman da yakejin kansa kamar ya kurma ihu yayi fiffige yaje ya shaƙo wannan yaron.

Yayinda Alhaji Idi Sale Dakata kuwa ya rumste idanunsa, saboda shi ayanzu ko son Ganin yaron bayayi, hasalima gaba daya tunaninsa ya tafi ne akan yanda zai ga bayan Rayyern din, saboda al'ƙawari ne da yayiwa kansa cewar saiya b’atar da yaron daga Doron k’asa.

Acan cikin tashar ta Arewa24 kuwa, Jannart ce ta sake gyara zamanta, batare kuma da ita ma ta d’ago kanta ta kalli Dr. Rayyern MAI-NASARA dinba tace.

“Toh Doctor mu dan koma baya.
Kaba da shawara akan cewar aduk’ar da asibitotin kudi, a tada na Gwamnati, ta hanyar zuba ingantattun likitoti da kuma kayan aiki, To irinku fa masu asibitotin kudi yaya zakuyi kaida ire-iren ka masu privet Hospital's, kodai kuma zaku dawo aiki a asibitotin Gwamnati ne! Ku watsar da naku asibitocin!!?.”
Cikin gamsuwa da yarda da kai yace.
“Kwarai kuwa, saboda ai hakan bawai gazawa bace, Indai muka had’e hannu da Gwamnati dan musamar da ingantaccen kulawa ga al’umma, To mu hakan kamar alkhairi ne agaremu, ba kuma najin hakan zai tauyemu ko ya ragemu da wani abu.”

Ya fad’a atak’aice saboda ya fara gajiya da amsa tambayoyin yarinyar mai shegen baki cai-cai surutu tuni yawun bakinsa sun kafe.
Hannunshi yasa ya ɗan shafa sajenshi har zuwa kan lips ɗinshi sabida ji yayi kamar bakinshin yayi tsawo ne da surutu.

Jannart kuwa, again cikin sanin makamar aikinta tace.

“Amma kamar baka goyon bayan duk wani privet hospital, in na fahimceka.
Kuma naga kaima kana da naka hospital din, wanda kuma bana gwamnati bane, ya akayi to hakan ta kasance? meyasa baka had’a hannu da Gwamnatinba!? kun ingata Koda asibiti daya ne!!!?”.

Wannan Tambayar ta saka duk magautan
Dr. Rayyern Mai-nasara dake Kallon tv suka saki Murmushin mugunta, saboda atunaninsu yarinyar ta kawosa makura inda bazai iya amsa tambayoyin nata ba Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.
Saida yaji tamkar ya shiga TV ya goya ɗiyar tasa Jannart, sai yakeji kamar dan su tayi mishi wanna tambayar dan ta kure musushi.
Dr Lukman kuwa hannunshi ya dunƙule tare da jinjinawa Jannart harda yimata alamar kiss dan masifar daɗi.

Ita kuwa Jannart batama san sunayi ba, kuma bada wata manufa tayi tambayarba sai dan dacewar hakan tunda tasan yanada asibitin.

Shikuwa Rayyern ko ajikinsa baiji wani abu ajikinsa dangane da tambayar da Jannart din tayi masa ba, hasalima Dan gyara zamansa yayi, cikin kuma kwarin guiwan da ako yaushe yake tare dashi yace.
“Banyi karatun likita Dan yin aiki akarkashin wani ba, asali Tubalin karatuna shine Idan na kammala na raya asibitin, dake gine tun kan zuwata duniya.
saboda amfanar al’umma, bawai iya mai kudi ba kawai harda talakawa, saboda babu wani wanda, asibitin Mai-nasara Hospital yafi karfin zuwansa, koda kuwa bashi da karfi, Mai-nasara Hospital muna da foundation na taimakawa marassa karfi dashi mukeyin dukkan taimakon daya dace, sannan kuma Mai-nasara Hospital bawai irin asibitotin nan ne da kowa ya sani ba, Ina da confidence akan Hospital dina, ako ina kuma zan fada batare dajin na fadi ba daidai ba!!!.”
Chapter 58 · 0% Book details