← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 81

Sashe 56

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda suka hau titi haka takejin zuciyarta, na wani irin bugawa, Yayinda aduk bayan kowanni minti fargaba ke sake lullubeta.

Ahaka dai suka isa cikin tv station din nasu.

Koda ta fito daga cikin mota, gaba daya kallon jama’ar dake waje Kanta ya dawo, Domin sosai kwalliyar tata ta dauki hankalinsu.

Itakuwa Jannart kaitsaye cikin wajen da zasu gudanar da program dinnasu ta nufa.

Wanda kuma tuntuni Salman, Aisha Lawal. Aunty Fauziya D Sulaiman da kuma Aunty Rabi da wasu sauran abokan aiki ke jiran zuwan ta.

Shigowarta cikin wajen ne kuwa yasa duk suka dago suka kalleta.

Yayinda Salman dake gefe kuwa, kyawun da yaga tayi yaudin ya kusan kashesa azaune.

Karasowa tayi, cikin kuma danne tarin fargaban dake zuciyarta, ta fadada Murmushin dake kan fuskarta, kana tabi kowannensu suka gaisa daya bayan daya.

Dai dai lokacin ne kuma MD yazo wucewa, ganinsu da yayi a zaune a harabar wurin ne kuma yasa shi, cewa.

“Yadai naganku duk waje ɗaya harda Shugabar marubuta.
haka, lafiya kuwa?”
Ya kare mgnar yana kallon Aunty Fauziyya X Sulaiman
“Sir Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara muke jira.”

Salman ya fad’a yana me Dan satan Kallon Jannart din.
Yayinda Aunty Fauziyya D Sulaiman kuwa take ɗan murmushin sunan da MD ya kirata dashi.

MD kuwa kansa yadan jinjina cike da yaba kwazonsu yace.

“To Allah Ya kawosa lafiya, amma Idan har bai samu zuwaba Jannart kada ki tashi hankalin ki, saboda akwai wani sauran chance da kike dashi.”

Kai Jannart din ta jinjina, kana asanyaye tace.

“Nagode Sir, amma anyi mana al'k’awarin cewa zaizo yaudin, shiyasa nasa hope dina akan zuwan nasa yau.”

“To shikenan Jannart badamuwa, nima bari Nafasa fitan da zanyi, Idan dai zaizo da gaske, zan zauna saboda nima kaina inason na sake ganinsa bare kuma a wurin aikinmu.”

Idanu Jannart tadan zaro cikin yanayin mamaki kuma tace.

“Laa Sir dama kasanshi ne?”

“Kwarai kuwa na tab’a haduwa dashi acikin jirgi, lokacin zanje France, amma abun ya Dan kwan biyu, duk da haka kuma Idan na ganshi na tabbata zan ganeshi to kwanaki naki ce muku na taɓa ganinshi kada kuyi ta damuna da ya kamanninsa yake.

Ajiyar zuciya duk mutanen wajen suka sauk’e, musamman Jannart da ayanzu zuciyarta ke dukan uku uku.

Saidai kuma wani abun daya kara rugurguza zuciyar Jannart din shine Ganin har 4:30 pm tayi amma babu alaman bak’on nasu zaizo.

Lokaci daya taji wani irin karyewar zuciya, wanda hakan yasa dole ta d’an janye jikinta gefe, tare da matsawa gefen had’add’un shuke shuken flowers din dake wajen.

Duk abunda takeyi kuwa Salman na lure da ita.

Yayinda Asiya kuwa taketa murmushi jin daɗi tunda itama ta rasa dama suna Allah yasa su rasa.
Wato irin a mutu har liman din nan

Suna tsaitsaye awajenne kuma.

Suka hango shigowar wata masifeffiyar mota had’add’iyar BMW bak’a mai matukar kyaun gaske da tsada.

Wani irin bugawa Jannart taji zuciyarta tayi, lokaci daya kuma duk suka kakkafe motor da ido hardai aka gama dai-dai-ta parking.

Bayan motor ta tsayane kuma, wani mai bakaken kaya ya fito cikin hanzari, inda ya zagaya ya bud’e murfin motar Usman P.A Kenan wanda shine yaja motar ma.

Ahankali ya zuro da k’afafunsa wanda sukasha tsadaddun bakaken takalma waje, lokaci daya kuma shima ya fito waje.

Yayinda ajikinsa yake sanye da royal blue suit masu masifar kyau.

Idanu Jannart ta zazzaro waje, Yayinda takejin tsanantawan da bugun zuciyarta yayi.

Amatuk’ar rud’e take binshi da kallo, lokaci daya kuma ta kwab’e fuska kaman zatayi kuka.

Cikin hanzari kuma ta nufi inda yake tsaye.

Matsowa tayi gab dashi, batare kuma dako lura da hakan da tayi ba, tace.

“Kai kuma, ya haka?
Toh ina yake Ina Dr. din? Bakace zaka zo dashi ba, Meyasa To zaka zo Kai daya kuma me zakayi mana? Kai me zanyi da kai”

Idanunsa yadan zuba mata.

Dai-dai lokacin ne kuma MD yakaraso wajen da matukar sauri.
Yace.

“Masha Allah sannu da zuwa.
Sir Sannu da zuwa, Mara ba da zuwa gidan tv’n mu, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara!!”

Dammmmmm haka zuciyar Jannart ta buga, alokacin da taji abunda MD din nasu ya fad’a.

Idanunta ta zazzaro waje tana me Kallon mutumin da taji ankira da Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.

Shikuwa Rayyern hannu ya mikawa MD n suka gaisa cike da mutuntaka.

Ganin hakanne kuma yasa duk sauran ma’aikatan dake wajen suka karaso, fuskarsu dauke da matsanancin farinciki sukeyi mishi sannu da zuwa cikin iya aikinsu da karrama manyan baƙinsu na musamman ne.
8Kusan irin karramar da za'ayiwa Dr Rayyern Mai-nasara.
In AYSHA ALIYU GARKUWA taje ba irinshi za'ayimata ba. Kunsan ace tuwon girma miyansa nama)
Da matukar girmamawa kuwa MD'n Yayi masa iso zuwa, cikin wani babban dakin tarban baki dake sashin.

Salman da Jannart kuwa kasa Koda motsawa sukayi, saboda tsananin mamakin da suke ciki.

Kallon Salman Jannart din tayi, cike da tsananin mamaki tace.

“Wai gizo idanuna keyi ne Salman ko kuwa gaskiya ne?”

Salman da shima ya shiga shock sosai, Kai ya Dan girgiza tare da cewa.

“Ko d’aya Jannart ba gizo idanunki keyi miki ba, shidinne dai, amma muje saboda mu sake tabbatarwa.”

Saurin jinjina masa Kai Jannart din tayi, tare da bin bayan Salman din suka shiga ciki.

Yayinda acan cikin kuwa, gaba daya MD ya rude da tsananin farincikin ganin Dr. Rayyern din mutumin da duk kafafen sada lbaran kasar Nigeria'n ke nema ganawa dashi basu samu. Sai su a yau ai yana cikin farin ciki.

Hakan yasa da kansa ya shiga debo masa drinks yana Jerawa akan babban table din dake tsakiyar dakin cike da mutuntaka.

Still kuma har yanzu bakinsa baiyi shiru ba, sannu da zuwa kawai yaketa Jerowa su Rayyern d’in.

Yayinda shikuwa Rayyern ke dan sakin murmushi, saboda yawan magana ba al’adarsa bace.

MD kuwa saida ya cika gaban su Rayyern din da kayan ciye ciyen fruit kala kala.

Cikin kuma sakin fuskan, dake bayyan tsananin jin dadinsa yace.

“Bismillah Dr ka sha ruwa, Domin yanzu saura mintuna 5 a fara shirin, kasamu kadan taba wani abu.”

Kai Rayyern din yadan girgiza, Cikin kuma muryarsa dake bayyana ajinsa akoda yaushe aji irin na mutunta kai ba girman kai.
A mutunce yace.

“Alhamdulillah Nagode, saidai kuma bani da ishashshen time, Ko zamu iya wucewa inda za’a haska shirin kaitsaye?”

Kai MD ya jinjina da sauri, cikin jin dadi da murna yace.

“Mezai hana ai muje kawai, mu zuwanka ayanzu ya fiye mana komai.”

Mikewa sukayi inda MD din ya shige gaba da sassarfa dan nunawa Rayyern din dakin da za’a haska shirin.

Inda tuntuni Jannart ta shiga cikin babban hall din ta zauna, gaba daya hall din cike yake da cameras, da kuma abubuwan daukan sauti da sauran na'urorin daukar hoto da sauti kai tsaye.

Yayinda aka shirya camera's sukayi layi, Yayinda duk suka zaku da son Ganin bakonna su.
Ba kuma ga iyasuba harda sauran ma’aikatan dake gidan TV, da kuma mutanen cikin ƙasar mu Nigeria kasancewar Tashar Arewa 24 TV tashece mai inkantattun kayan aiki da haziƙan mahaikata.
Kasancewar shirin live ne kaitsaye za’a haska shi wa duniya alokacin da ake tsaka da daukanshi.

Jannart kuwa da take zaune akan kujerar dake tsakiyan wajen.
Yayinda can gefe kuwa kujerune a jere.
Inda wasu daga cikin ma'aikatan ke zazzaune

Jannart kuwa.
Shiru tayi tana me mamakin yanda al’amarin ke shirin kasancewa.
Yayinda Salman dake can gefe shidinma zallar mamakin faruwar hakan yake.

Shigowar Dr. Rayyern da kuma MD wajen yayi dai-dai da cikar lokacin da za’a fara shirin.

Wannan yasa tun kafun Dr. Rayyern din ya karaso kan babban stage din da mazauninsa yake suka fara dauka.

Yayinda Rayyern kuwa ganin wace zatayi masa tambayoyin, yasa ya d’an hade rai.
Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Kenan karya sukamin itace zata gudanar da shirin, bawai wancan namijin ba.”

Azahiri kuwa karasowa kan stage din yayi, tare da zama akan kujerar dake fuskantar na Jannart din.

Yayinda Jannart kuwa ta danne duk wani tunani dake ranta, juyawa tayi ta kalli camera hade da cewa.
“B....!

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Chapter 56 · 0% Book details