← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 81

Sashe 46

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can MAI-NASARA Hospital kuwa.
Ma'aikatan Arewa 24 TV ne, kusan su shida ke cikin ɗakin da Jannart ke konce.
A hankali ta kalli Aisha Lawal dake ta gyara mata gashin kanta dake kan kafaɗunta.
Salman ta ɗan kalla cikin nitsuwa tace.
“Yah kiraka kuwa?”.
Cikin yanayin tausayawa yace.
“Keda baki da lfy me ruwanki da kiran wani”.
Hajia Rabi'ah ce ta ɗan yi murmushi tare da cewa.
“Yoh keda ma gaki a asibitinsa”.
Aunty Fauziyya D Sulaiman kuwa cikin kula da nagarta ta ɗan shafa goshinta tare da cewa.
“Ai dukkan uzuri bayan lfy yake, kada ki damu kinjiko Jannart MD da kansa yace a gaidaki da jiki”.
Cikin jin daɗi ta kalli Fauziyya D Sulaiman tare da cewa.
“Ngd matuƙa My Aunty”.
Mom kam dake gefe sai godiya takeyi musu.
Sun jima anan kana suka ajiye ledodin Fruits da suka kawo mata,
Kana suka fita.
Har sunje bakin ƙofar fita Salman ya juyo jin tana cewa.
“Salman kada ka manta fa saura kwana biyar kacal”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“In dai ina raye to kisa a ranki kinada GARKUWA”.
Yana faɗin haka suka fita.

Kasan cewar yau jumma'a haji babbar ranace yasa, dukkan Al'ummar musulmai suke cikin yanayi na musamman duk kan maza nata shirin zuwa sallan jumma'a tako ina.

Sha biyu da rabi dai-dai haka take a gidansu Dr Rayyern Mai-nasara ma.

Yayinda hakama Barrister Kabir kasan cewar duk a Nassarawa G.R.A suke yasa gaba ɗaya masallacin Al'furƙan suke da niyar zuwa.

A hankali ya kalli Mamy dake ce mishi.
“Toh Rayyern me kake so in dafa maka ne? Ni bana son zamanka da yunwar nan fa”?.
Yana mai haurawa saman yace.
“Mamy yanzu lokacin jumma'a ya ƙara to, bari inje inyi shirin salla in na dawo zanci abincin”.
Da ido kawai ta bishi ganin tuni ma ya haura sama.

A hankali ya ɗan juyo ya kalli ƙofar Bedroom din Ramadan jiyo muryarsa shida Riyyam-nsra alamun suma shirin tafiya jumma'a sukeyi.
Dan yana jiyo muryar Riyyam-nsra na cewa.
"Nima fa mai gare zaka bani in saka Hamma Ramadan”.
Kai kawai ya jinjina ya wuce Bedroom ɗinsa.
Kai tsaye Bathroom ya wuce.

Bayan 15mn ya fito ɗaure da towel.
Gaban dreesing mirror'nsa ya nufa cikin yanayin sauri-sauri ya busar da sumar kanshi tare da shafa mai kana ya miƙe ya nufi gaban ƴar ƙaramar Driver'n'shi na glass dake gefen babban durowar.

A hankali ya buɗe, ido ya ɗan zubawa ƙananan kayanshi dake kimtse a ciki.
Wata tattausan boxer and single ya zaro masu ɗan karen taushi.
A hankali ya meda marfin ya rufe, sauri-sauri yasasu kana ya zare towel din ya cilla gefe ganin ɗaya ta kusa cika.

Babbar durowar ya buɗe,
Wasu kayan ya zaro Getzner fara ƙal mai masifar kyau da sheƙin maiƙo.
Riga da wondo.
Sauri-sauri ya saka su.
Kana ya koma gaban Driver'n'shi na glass din hula damanga ya zaro Royal blue kalan zaren surfanin da akayi wa Getzner aikin rigar.
Sunkuyowa ya ɗanyi toms masu masifar kyau samfarin Italy ya zaro suma Royal blue.
Kana ya dawo gaban dreesing mirror'nsa.
Kafa hular yayi irin kafin nan da matasa ke cewa.
Babu ruwanka da duniya.
Wato ya ɗan ture hular ta koma baya kaɗan hakan yasa tattausar sumarshi ta fito tana zuba sheƙi sajenshi ya kwanta lib sai sheƙi yake siraran lips dinsa suma suna sheƙin taushi.
Sai kuma ya sunkuyo yasa fararen sawunsa cikin takalman.

Agogon Daimond dake kan mirror'n ya saka.
Turarensa Oud Zauji mai masifar daɗin shaƙa ya fesa.
Kana ya zari car key ɗinsa Dan lokacin ya ɗan so ƙure mishi.

Da sassarfa ya sauƙo kan steps din har yana takawa bibbiyu.

Ba kowa a falon yasa da sauri yasa kai ya fita, ko su Baba Mauɗo duk sun tafi sai Ari.

Haka yasa ya buɗe mishi gate kana Suka tafi tare haka nan yake ta jin tsinkewan zuciya da faduwan gaba.

Numfashi ya ɗan fesar lokacin daya shiga cikin masalacin sabida har yanzu huduba akeyi.

Inda ake hudubar akan illar cin riba.

Sosai aka nitsu, bayan an ida hudubar ne kuma aka kabbarta sallan...

Bayan sunyi raka'a biyun, an zauna zaman tahita.
Sun ida zasuyi sallama sunyi gefen dama sun juyo hagu.
Kenan Barrister Kabir ne dake gefen daman Rayyern ɗin ne ya ɗan leƙo fuskar Dr Rayyern bayan ya sallame.

Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da ɗaga hannunshi sama ya fara yiwa ubangiji kirari cikin zuciyarsa yana ƙara neman zaɓin Allah kan manufarsa da addu'a in al'khairi ne Allah ya nufeshi da ida nufinsa a wannan lokacin.
Yayinda shima Rayyern da mafi akasarin mutane hakan sukeyi.
Bayan an idar da salla ne, Dr Rayyern na fita yaji an riƙo hannunsa tare da ce masa.
“Assalamu alaikum”.
Da sauri ya juyo tare da cewa.
“Wa alaikassalam”. Fuskarshi ya ɗan yamutsa alamun tunani kana a hankali yace.
“Lfy”.
“Lfy lau Alhamdulillah Dakta”.
Barrister Kabir ya faɗa yana mai jawo hannun Dr Rayyern ya nufi can kan titi wurin motarsa.

Ba tare da ya ƙara mgna ba yabi bayansh.
Suna zuwa ya buɗe suka shiga....!

Anan asibitin kuwa, da Yamma Dr Sulaiman ya bawa Barrister Kabir takardar sallama, sabida sosai jikin Jannart yayi sauƙin.

Ya ƙara da cewa.
“Idan an barku kun ƙara kwana tofa sai ranar Monday za'a sallameku. Toh kuma tunda jikin da sauƙi gwara kuje gida zaifi”.
Dr Sulaiman yayi mgnar bisa bin umarnin da Dr Rayyern ya kidanya mishi a waya.

Cikin jin daɗin samun lafiyar nata Barrister Kabir yace.
“Toh Alhamdulillah Dr Sulaiman mun gode matuƙa Allah ya bar zumunci”.
Amin Amin yace tare da juyawa ya fita.

Su kuwa biyar dai-dai Barrister Kabir ɗin ya ɗauki Jannart da Mom ya nufi gida dasu.
Suna kan hanya ne Daddy ya kirasu yazo bai samezu ba.
Nan yake ce mishi ai an sallamesu gasu a hanyar gida.

Nan dai suka koma gida Barrister Kabir ya bawa Mom magungunan tare da cewa ta kula da Jannart da shan mgnin.
Ba tare da yayiwa yayan nasa mgnar Junaid ba ya sallamesu ya tafi.

Toh a hankali dai abubuwa ke juyawa suna wakana.
Yau Monday kwana biyu kenan da sallamo Jannart Alhamdulillah kuma jiki yayi sauƙi sosai.
Junaid kuma har yau bai zo gidaba.

Barrister Kabir kuwa duk cikin kwanakin nan bashi da zama yana yawan zirga-zirgan da Aunty Dijat ta gaza gane na menene.

Yau Monday misalin biyar na yamma.
Dr Rayyern Mai-nasara ne dake zaune a yar barandarsa balcony dake sama can jikin Bedroom ɗin sa.
Sanye yake da wasu tattausan riga da wondon iya guiwa rigar kuma irin mara hannun nance.

System ɗinshi ne bisa stoll ɗin dake gabansa sai plate da chocolate sai Bootle water a gefenshi.
Sosai ya dugufa kan aikin da yakeyi.

A hankali ya ɗago kansa cikin tarin gajiya ya juyo ya kalli farfajiyar gidan nasu can bakin gate.
Wani irin juyowa yaye tare da tashi tsaye da masifar fargaba ya zubawa fuskar Barr....!

*TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama Da Allah.*

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.
Chapter 46 · 0% Book details