← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 81

Sashe 44

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*WANNAN PAGE D’IN SHINE K’ARSHEN FREE PAGE, DAGASHI BABU WANI FREE PAGE IN KIN GANSHI A WOJEMA TO SATA PAGE NE daga wannan PAGE 18 na gama free PAGE, dan sonku da Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina 1k ko 500 da kika bada bawai yana nufin kin biya kin mallakeshi bane kuɗin karantawa ne, dan Allah nace ba don niba, in Zaki saya ga ac no 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da damar tura ta account ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo minshi ta WhatsApp 09097853276.*

_Masu karanta Audio books kuyiwa girman Allah ku kiyaye min littafina domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki, ga number birjik a pages idan ki/kana so ki/kayi min mgn mu dai-dai ta masu posting a wasu shafukan kuyi girman Allah ku barmin books na, 09097853276_

Shiru Jannart tayi tare da zuba mishi idanu, tana mai nanata kalmar daya suffanta Daddy'nta dashi.
“Hankaka!!!?”. Ta faɗa can ƙasan zuciyarta tana mai son nazartar ma'ana da tushen kalmar a hausan ce.

Gyara zama Abba yayi tare da fuskantar ta da kyau cikin tsananin kulawa, tausayi ƙauna, jinƙai.
Murya a sanyaye yaci gaba da cewa.
“Bazaki fahimta ba Jannart kada ki tsauwalawa kanki tafiya nazari ko tunanin sarƙaƙiyar dake cikin rayuwarki.
Bazaki ganeba sai an ganar dake, ina cikin matuƙar damuwa mai tarin yawa.
Na yadda zan samu in zama GARKUWAR ki, ina tunanin kamar yarda da kikayi min tana da rauni bazan samu amincin da nake buƙata daga garekiba. Na amsar umarni na sawa ko hanawa!!!”.
Hawayen dake kwaranya bisa fuskarta tasa hannun ta ta share kana a take wasu suka kwaranyo.
Hakan kuma baya rasa nasaba ne da yadda taga idanun ƙanin mahaifin nata yana kwaranyo da hawaye.
Tana hango tsananin tausayinta cikin kwayar idanunshi.
Numfashi ta fesar a hankali tare da danne shessheƙan kukan dake son kumbce mata cikin aminci da dukkan yarda da yaƙini murya na rawa tace.
“Abba kana da ƙarfin iko a kaina.
Ni ɗiyace a gareka, kuma zan zamo mai biyayya akan dukkan umarninka, zan kuma nitsu in fahimci abun da kakeso in fahimta bani da wani katanga jigo majingini sai kai, Abba inada kekkyawan yaƙini kaine TUBALIN farin cikina”.
Wani zazzafan numfashi Barrister Kabir ya fesar kana ya ƙara jawo kujerar ta matso kusa da ita, cikin sanyi ya kama tafin hannunta murya can ƙasa yace.
"Yadda na riƙe hannunki haka.
Ana haifoki mahaifiyarki ta damƙa min amanarki.
Tana mai jaddada min cewa in zama Garkuwanki inyi miki zaɓi mijin na gari wanda naga ya dace dake, in gaya miki ke marainiyace tace in faɗawa duk wanda zan bawa aureki cewa ke marainiyace dan ya duba maraicinki.”
Ina shessheƙan kuka wanda yake tafe da zazzafan tsohon dafi mai ciwo a zuciyarsa ya danne mgnar.
Itama kukan ta farayi.
Wanda Har Aunty Dijat dake woje ta fara jiyo sautinsu.
Cikin tsananin rauni ya kalleta murya na rawa yace.
“Jannart in nayi miki zaɓi da miji kamar yadda mahaifiyarki ta roƙa, zaki amince dashi, zaki yarda da duk tsarin da zan zo miki dashi dan mu cika fatan mahaifiyarki!!! In Kuma samar miki ƴanci!?”.
Cikin kukan ta gyaɗa mishi kai.
Hannunshi yasa ya sharce hawayen sa kana ya tsareta da ido tare da cewa.
“Zaki iya amincewa in ɓoyeki, in bada ajiyarki a killataccen wurin da zaki tsira da ranki da lfyarki tun kafin wa'adin da suka tsara a kanki ya cika”.
Zuwa yanzu kanta ya ƙara ɗaurewa, duk da ta saba jin waɗannan zantukan a bakin ƙanin mahaifin nata, amman har yau ta gaza samar musu muhallin ajiyewa.
Cikin rashin fahimta tace.
“Abba na amince”.
Kai ya gyaɗa kana yayi ƙasa da murya yace.
“Har Daddynki fa zaki bari bazaki kuma sanar mishi komaiba, bazai san inda kikeba”.
Hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da zaro ido kana tace.
“Abba in na dawo Yah Junaid zai kasheni, kuma Daddy na zai shiga tashin hankali!”.
Numfashi ya fesar kana a hankali yace.
“Lokacin da zaki dawo, zaki dawo da encinki mai ƙarfi, Junaid ko farcenki bazai taɓa ba, Daddy kuwa kunya zata makantar da idanunshi sabida ya gaza zama uba kuma Garkuwa a kanki.
Sai dai hakan bazai faruba sai da amincewarki da sahalewarki.
Kuma sai haka ta faru zaki gane kurman baƙin dake cikin rayuwarki.
Shin kin amince!!!?”.
Cikin zulimi tace.
“Abba har na tsawon wani lokacin zaka ɓoyeni? Kuma ina zaka ɓoyenin?”.
Da sauri yace.
“Bana tantance lokacin ba, amman zan ƙiyasta wata takwas zuwa shekara ɗaya.
Sannan inda zan ɓoye ki kuma shine ban gama tantancewa ba, amman ki aminta dani GARKUWA zan nema miki”.
Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe kana a hankali tace.
“Abba na aminta da kai nasan baza cutar dani ba”.
Da sauri yace.
“Toh ki adana wannan mgnar amanace tsakaninmu kada ki gayawa kowa, duk faɗin duniyar nan.
Nan kusa kuma zan samu wurin adanaki mai inƙanci”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Toh Abba”.
Shigowar Aunty Dijat ce yasa suka katse zancen.

*Wannan shine PAGE na karshe a FREE PAGE in ki. Kuma ganin ci gabama to na satane baiwar Allah in kinaso ki saya, in bazaki iyaba babu dole ga littatafai da dama na kyauta, special Group 1 karamin group 500 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU*

A nan gidan nasu kuwa.
Mom na komawa ta shiga Kitchen aikin ta farayi yayinda Abdul ke gefenta yana tayata kana yana mgna, da Yah Azeez ɗinshi wanda.
Kwanan ya koma Macsow kasan cewar acan yake aiki.
“A jikin da sauƙin Yah Azeez yanzuma Mom ta dawo anjima in munje zan haɗaku a waya”.
Abdul ya bawa Azeez amsa.
Cikin tausayawa Azeez yace.
"Toh shi kuma wawan ina yake”.
Mom ce ta ɗan ja tsaki tare da cewa.
“Yoh waya sani tun jiya da abin ya faru daya fita bai dawo ba”.
Kwaffa yayi tare da cewa.
“Allah zai saka mata”.
Daga nan dai sukaci gaba da mgnar suna aikinsu.
Saida suka gama aikin ta shiga Bathroom Dan yin wonka.

_Dan Allah daga wannan PAGE din kada a fidda wani_

A can Gidansu Dr Rayyern Mai-nasara kuwa kasan cewar yau jumma'a.
Basu dawo masallaci da wuriba,
Sai kusan ƙarfe takwas suka shigo
A jere da ma'aikatan gidan baki ɗayansu.

Yayinda suka gaggaisawa suna tambayar jikin Rayyern.
A hankali ya kalli Baba Mauɗo tare da cewa.
"Alhamdulillah Baba Mauɗo na saumu sauƙi banjin komai sai baccin da nake ji bai isheni ba”.
Cikin jin daɗi Baba Mauɗo yace.
"Alhamdulillah Allah ya ƙara mana lfy”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Abba ne ya ɗan kalli Ramadan dake cewa.
“Eh kasan mgnin ne zai ɗan saka jin bacci”.
Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa.

Dai-dai lokacin da suka shiga falon ne Riyyam-nsra ya lumshe idonshi sabuda sabida ƙamshin masar da Mamy ke toyawa wanda duk ranar jumma'a take yinshi bisa umarnin Rayyern za'a cika manya-manyan kuloli kana ta dama kunun gyaɗa suna kaiwa tsangayar al'majirai”.

Da sauri ya nufi Kitchen din yana cewa.
“Mamy Barka da safiya”.
Murmushi tayi tare da sauƙe kaskon tuyan dan tun ƙarfe huɗu take farawa in lokacin salla yayi sai taje tayi kana tazo taci gaba.
So yanzu ta gama.
“Barka dai Riyyam-nsra kun dawo ko”.
Kai ya gyaɗa mata yana kallon tukunyar ferfesun data sauƙe.
Shaƙan zazzafan ƙamshi yayi tare da cewa.
"Wow special Mamy girkinki da daɗi”.
Juyowa tayi ta da sauri jin ƙamshin turaren Rayyern.
Ƙarasowa yayi cikin Kitchen din.
Gefenta ya ɗan tsaya, tare da buɗe manyan kulolin.
Ita kuwa foodflask ɗin da ta zuba musu breakfast ɗinsu a ciki ta nunawa Riyyam-nsra tare da cewa.
“Kai manasu Dinning”.
Da sauri yace to kana ya ɗauka ya fita.

Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
“Rayyern ya jikin naka?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Na worke”.
Cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah, Allah ya ƙara mana lfy”.
Amin Amin suka amsa shida Riyyam-nsra.

Ramadan kuwa da Abba suna can falo, da alamu mgnar aure Ramadan keyiwa Abba duk ya marairaice.
Cikin haɗe fuska Abba yace.
"Kai da Allah tafi daga nan, Yayanka ma baiyi aureba sai kai ai dole dai ka jira sai yayi ko”.
Fuska ya kwaɓe tare da longobar da kai kana cikin girmamawa yace.
“Toh Abba”.
Yana faɗin hakan kuma ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin.
Da ido ya bishi yana mai jin zafin tsawar daya daka mishin a ransa Allah ya sani baya son yin abinda zai b’atawa yaranshi rai more especially Rayyern.

```Special people group 1k ne karamin group kuma 500 BABBANCINSU a yawan posting ne```

Rayyern kuwa dake gefen Mamy cikin nitsuwa yace.
“Mamy kada Ramadan ya kai masar tsangayar malam Babayo.
Ya bari yau tsanƙayar Malam Mai-nasara zan kaishi, in Abba ya amince”.
Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Toh Allah yasa ya amincen”.
Amin yace yana mai bin bayanta suka fito.
A Dinning area Suka haɗu da Ramadan da yayi fuskar tausayi,
Ɗan zuba mishi ido yayi kana ya kauda kanshi ya nufi tsakiyar falon.

Mamy kuwa gefen Ramadan da Riyyam-nsra da suka zauna bisa Dinning table tayi kana ta kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Baka kaiwa su Baba Mauɗo nasuba”.
Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tare da cewa.
“Toh”.

Kana ya ɗauko kulolin da plate cups and spoons. Ya wuce.

Shi kuwa Rayyern a nitse ya zauna gefen Abban nasa, cikin sanyi yace.
“Abba”.
Numfashi ya ɗan fesar kana yace.
“Na'am Rayyern, ya akayi”.
Yayi mgnar cikin tsananin kulawa.
Cikin yanayin neman al'farma yace.
“Abba sadakan nane nace, dan Allah yau ka amince mu kaishi tsangayar Mai-nasara”.
Ga mmkinsa sai yaji Abba yace.
“Toh Allah ya bada ladan”.
Cike da mmki yake kallonsa yana kuma muƙewa,
Numfashi ya fesar fahimtar Abba yana cikin zurfin tunanine shiyasa ya amsa a sauƙaƙe.
Hakan yasa da sauri ya dawo Dinning area.
Cikin bada umarni ya kalli Ramadan da Riyyam-nsra da ya shigo yanzu yace.
“Yauwa taso maza ku ɗauki womas ɗinan ku kai min cikin mota”.
To sukace kana suka fara ɗauƙa.

Shi kuwa da sauri ya haura sama ya ɗauko car key ɗin nasa.

Koda ya sauƙo a hankali yace.
“Toh Abba na tafi”.
“Sai ka dawo”.
Ya bashi amsa da alamun har yanzu yana cikin nazari ne.
Chapter 44 · 0% Book details