← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 81

Sashe 40

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Riyyam nsra ya saka, Yayinda ita kuma Rayhanna ta sanya mayafinta ta rufe fuskarta, wanda tayi hakanne kuma saboda Sam bazata iya jurewa, irin Kallon da Ramadan din keyi mata ba, Domin kallone da yake bayyana tsananin kauna da soyayyarsa agareta.

Baki Ramadan din ya bud’e da niyar cewa wani abu, amma kuma sai k’aran wayansa dake tashi, acikin aljihun rigarsa, ya hanashi furta komai.

Zaro wayartasa yayi, ganin sunan Abba na yawo akan screen din wayar ne, kuma yasa shi d’agawa da sauri.

Daga can b’angaren kuwa Abba dake tsaye agefen Rayyern ne yace.

“Ramadan, Rayyern! Rayyern ciwon kansa ya tashi!”

Idanu Ramadan din ya dan zazzaro tare kuma da, mik’ewa tsaye cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki yace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Abba maiya samu Hamma Rayyern din, yaushe kuma ciwon kan nasa ya tashi?”
Ya tambayi Abban cikin tashin hankali, gami da tsananin damuwa.

“Bansani ba Ramadan, Domin yanzu dawowanshi gida, yanzu haka gashinan a kwance sai faman rike kan na yakeyi.
Maza Ramadan kabar duk abunda kakeyi ka dawo gida, sannan ka biya ta pharmacy ka had’o masa magunguna.”

Abban ya fad’i hakan, cikin muryar dake bayyana cewa, kwarai yana cikin damuwa.

Ramadan kuwa idanunsa da suka ciko da k’walla, saboda tausayin dan uwannasa yad’an lumshe, kana cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.

“Shikenan Abba ganinan zuwa.”

Yana gama fadan hakanne kuma Abba ya katse kiran.

Riyyam-nsra da tun d’azun shima ya mik’e tsaye hankalinsa atashe matuka, yace.

“Hamma Ramadan mai yasamu Hamma Rayyern? Dan Allah karkacemin wani abu na cutarwa ne ya sameshi.”

Idanu Ramadan din ya bud’e, cikin yanayin sanyi yace.

“Ba abunda ya sameshi Riyyam, kawai dai ciwon kansa ne ya tashi, wanda dama kuma yana dashi, saidai bai cika tashi ba, harsai da dalili, Idan ciwon kannan ya tashi Riyyam, Hamma Rayyern yana shan wahala, saidai duk da haka gwara ciwon kan, akan matsanancin ciwon cikin da yake tashi mishi, awasu mabanbanta lokuta.”

D’an rank’wafowa yayi ya kalli Rayhanna, da itama gaba daya damuwa ta bayyana akan fuskarta, saboda tasan matsayin Dr Rayyern din awajen Ramadan, tasan yanda Ramadan ya dauki Rayyern, da kuma yanda yake girmama duk wani abu daya shafesa, haka kuma tasan yanda Ramadan din ke daukan duk wata matsala ko damuwar yayansa, Domin sauda yawan lokaci Ramadan din, kan fad’a mata cewar Hamma Rayyern dinshi, shine duk wani Garkuwa’rsa, shine kuma wanda ya tsaya masa akan jindadi da farincikinsa.

“Hanna zantafi, Hamma Rayyern bashi da lafiya, zamuyi waya later.”

Ramadan din ya fada murya asanyaye.

Mik’ewa tsaye Rayhanan tayi, tare da cewa.
“Shikenan badamuwa, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, yasa zakkan jikine.”

Da “Ameen.” Ya amsa, har wajen da motarsa kirar Benz ke fake kuma Rayhanan ta rakosu, inda tayiwa Riyyam-nsra sallama.

Saida taga ficewarsu daga cikin compound d’in gidan nasu, kuwa kafun ta koma ciki.
Duk zuciyarta babu dadi, saboda duk wata damuwa da tagani akan fuskar Ramadan to ta shafeta.

Ramadan kuwa suna ficewa daga cikin gidansu Rayhannan, wani irin gudu ya soma shararawa akan titi, wanda hakan yasa cikin mintuna kadan suka iso, babban pharmacy dinsu.

Ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, haka ya fito ya shiga cikin pharmacy din, duk wasu magunguna da yasan Rayyern din zai buk’ata ya had’a, tare da fitowa agurguje yaja motar suka nufo gida kaitsaye.

Isowarsu bakin gate din gidanne kuma yasa, Ramadan soma danna horn.

Wannan yasa cikin sauri Baba Maud’o dake zaune abakin gate din, yayi jigum, yazo ya bud’e musu, gaba d’aya bayajin dadi acikin zuciyarsa, saboda sai ayanzunne ma yake tunawa da cewar, halan ciwon kai din Rayyern dinne ya tashi, saboda aduk cikin gidan babu wanda baisan da cewar, Rayyern na fama da ciwon kai dana ciki ba.

Ramadan kuwa yana shigowa cikin gidan yayi parking motar, cikin sauri kuma shida Riyyam suka fito, kowannensu fuskarsa dauke da matsanancin damuwa suka shige cikin gidan.
Tunkafun su karasa shiga cikin babban falon gidan kuma, Ramadan ya soma b’abb’alle magungunan da zai bawa Rayyern din.

Wanda hakan yasa suna shiga cikin falon, direct Riyyam-nsra ya k’arasa gaban deep freezer, tare da dauko bottle water marar sanyi kasan cewar ba'a jima da sasuba.

Koda ya dawo goran ruwan ya mik’awa, Ramadan wanda zuwa lokacin harya gama b’are magungunan, inda da kansa ya tallafo Hamman nasa, tare da zuba masa magungunan, kana ya had’a masa da ruwan faro.

Atake kuwa Rayyern ya had’iye magungunan, saidai kuma cikin radadin ciwon kan nasa da yakeji, ya sake komawa ya kwanta, Yayinda sannu Ahankali yake ci gaba da d’an jujjuyawa kan nasa.

Idanu duk suka zuba masa, kana cike da tsananin tausayawa sukeyi mishi sannu, Riyyam-nsra kuwa zama yayi dab’as ak’asa, idanunsa da suka cicciko da hawaye ya zubawa Hamma Rayyern d’in, acikin ransa kuwa yana me addu’a, da fatan Allah Ya bawa hamma Rayyern dinnasu lafiya.

Rayyern kuwa dake kwance kannasa ya sake rikewa, tare da lumshe idanunsa, wanda sukayi jazur, saboda tsabar wahalan da yakeji kuwa, hatta jijiyoyin dake kwance akan goshinsa saida suka fito rud’u rud’u.

*Dan girman Allah masu sayan littattafai dan su fitar su watsashi kuyi hakuri kada ku saya littafina dan Allah nace in kin saya kuma ki gaya min in meda miki kuɗinki*

Bayan kaman mintuna 15 dashan maganin nasa ne kuma, ya soma sauke wani irin wahalalliyar ajiyar zuciya.
Yayinda sannu ahankali yakejin relief nad’an saukar masa.

In a 20mn kuwa batare da zato ko tsammani ba, bacci mai nauyi ya daukesa.

Jin yanda numfashinsa ke fita da d’an fusga ne kuma, yasa su Abba gane cewar yayi bacci, ajiyar zuciya suka sauk’e dukansu, Yayinda Abba kuwa ya d’an rankwafa tare da gyarawa Rayyern din kwanciya.

Bayan ya koma ya zauna akan kujera ne kuma yasa hannunshi duka biyu yayi tagumi cikin alamun tarin fargaba, tashin hankali, so, da tarin tausayin d’an nasa .
Ido Ramadan ya ɗan zuba mishi kana a hankali yace.
“Abba ba komai fa in sha Allah zai samu lfy”.
Numfashi ya ɗan sauƙe a hankali kana murya asanyaye yace.

“Hakika yanzu aduniya babu wani abu da yake, damuna da kuma matuk’ar d’agamin hankali sama da ciwon Rayyern.
Ciwon Rayyern yana damuna, musamman ciwon cikinsa da Idan ya tashi masa, yakeyin kamar zai rabamu dashi, Tabbas Ina matuk’ar tsoron ranan da ciwon nasa zai tashi, Ina fargaban hakan akoda yaushe, Ina mai kuma addu’a da fatan, Allah ya yayemishi wannan ciwon kai da ciwon cikin, Domin kuwa aduk sanda d’aya daga cikinsu ya tashi, shi kad’ai yasan wani irin zafi da yakeji tunda har yake fidda shi hayyacinsa.”

Abban ya kai k’arshen maganan nasa, cikin raunatacciyar murya, Yayinda idanunsa kuma suka cicciko da hawaye.

Ganin hawaye a idanun Abban ne kuma, yasa Mamy, Ramadan, Riyyam duk sukaji jikinsu yayi sanyi, take kuma idanun Mamayn ma duk suka cicciko da hawaye, kasancewar ta Mace ne kuma, yasa ta kasa controlling hawayen nata, harsaida suka sauk’o kan fuskarta, batare kuma da ta bari kowa yaga hawayen nata ba, ta share da sauri.

Dai-dai lokacin kuwa Baba Maud’o dake tsaye abakin k’ofar shigowa falon, ya d’an d’aga muryarsa wajen yin sallama.

Jin muryar Baba Maud’o dinne kuma yasa, Ramadan mikewa ya k’arasa tare da bud’e kofar, Cikin kulawa yace.

“Baba Maud’o bismillah ka shigo mana.”

Kai Baba Maud’on ya girgiza, tare da cewa.
“A’a basai na shigo ba Ramadan, dama nazo ne na tambaya naji ya jikin Rayyanu.”

Ajiyar zuciya Ramadan ya sauk’e, cikin kuma son kwantarwa da Baba Maud’on hankali yace.

“Jikinsa da sauki sosai Baba Maud’o, yasha magani kuma yanzu haka ma bacci yake, Insha Allah kuma Idan ya tashi daga baccin, zai ji saukin ciwon kan.”

Kai Baba Maud’on ya jinjina, cike kuma da gamsuwa yace.

“Masha Allah! Allah Ubangiji ya k’ara masa lafiya da Nisan kwana mai amfani.”

Da “Ameen.” Ramadan ya amsa, ganin Baba Maud’on ya juya ya tafi ne kuma, yasa shima komawa cikin falon.

Baba Maud’o kuwa Koda ya nufi dakinsa dake cikin gidan, hannayensa yasanya ahankali ya share hawayen da suka gangaro daga Cikin idanunsa, wanda kuma yayi imani cewa, da ace bai bar wajen Ramadan din da wuri ba, To da akan idanun Ramadan hawayen nasa zasu zubo.

_Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki karanta cikin salama special Group 1k ƙaramin group 500 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp_

Acan b’angaren su Barrister Kabir kuwa, da wani irin speed suka shiga cikin asibitin.

Wanda kuma suna shiga ko gama parking ba suyiba, aka turo wasu nurses da gado irin maitayannan, su dakansu nurses din suka d’aura Jannart akan gadon, tare da kutsawa da ita cikin asibitin, kaitsaye zuwa emergency.

Suna shigar da ita emergency din kuwa, Dr. Sulaiman, da kuma Dr. Imran, kana da Dr. Fatymah, suka shiga emergency din, tare da duk’ufa akanta, cikin sauri suka soma bata taimakon gaggawa.

Yayinda acan waje kuwa, hankali atashe Barrister Kabir ya karasa receiption na, Hospital din dan bud’ewa Jannart din folder.

Koda yaje kuwa baiwani dau lokaci ba layi ya iso kanshi.

Mai bud’e folder dinne ya dago kansa ya kalli Barrister Kabir tare da cewa.
“Sir me sunan patient din?.”

D’anjim Barrister Kabir yayi, natsawon wasu mintuna, kafun ya dago kai, cikin aminta da abunda zuciyarsa ta yanke yace.

“Sunanta *Jannart Abdulkarim Saleh Dakata.”*

Kai mai bud’e folder’n ya jinjina, tare da maida kansa k’asa ya rubuta abunda yaji mutumin ya fad’a masa.
Yan cike cike yayi cikin abunda bai wuce 5mn ba kuwa, ya bud’ewa Jannart folder acikin Hospital din.

Barrister Kabir kuwa ganin komai ya kammala ne, yasa shi komawa bakin emergency room din ya zauna, tare da sanya hannayensa akan fuskarsa ya zuba tagumi, Tabbas a yanzun abubuwa da yawa ne ke damunsa, amma babban burinsa shine farfadowar Jannart da kuma dawowa cikin hayyacinta.

Acan cikin Emergency room din kuwa, sosai su Dr. Sulaiman suka duk’ufa akan Jannart don ceto rayuwarta, saidai kuma duk yanda suka dauki abun ya wuce nan.
Chapter 40 · 0% Book details