← Book details Tubali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 81

Sashe 17

Tubali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

11:00 am dai-dai na cika kuma Gaba d’aya suka hallara acikin babban hall d’in, da tsaruwarsa ta zarce kwatantuwa, wanda cikin mutanen dake zaune awajen kuwa harda mai girma Govenor kano.

Nanfa bayan kowa ya zauna suka shiga gabatar da taron nasu, inda d’aya bayan d’aya daga cikinsu ke tashi suyi bayani gamsasshiya, wanda kuma hakan tamkar k’arawa junansu sani ne sukeyi.

Alhamdulillah dai sun gudanar da taron nasu yanda ya kamata, inda kowannensu ya fahimci d’an uwansa, bayan anci ansha ne kuma suka rufe taron da addu’a.

Koda suka fito compound na hall d’in, kuwa tsayawa gaggaisawa da junansu sukayi.
Inda ananne kuma Dr. Lukman ya mikawa Rayyern d’in hannu sukayi musabaha.

Bayan sun gaisa d’inne kuma yakeyi masa murnar k’arin nasarar da yake ta samu, da kuma irin cigaban daya samu arayuwa.

Dakai kawai Rayyern din ya iya amsa masa, domin magana bata wani fiye damunsa ba kuma ya gaji matuƙa da doguwar jawabin da yayi a likitance.

Har ya juya zaitafi ne kuma maganar da Dr. Lukman din ke fada ya dakatar dashi.
Inda yaji yana cewa.
“Please Dr.Rayyern Mai-nasara idan babu damuwa, muna gayyatanka wani zama da zamuyi yau a Dakata’s Company Nigeria Limited.”

D’an juyowa Rayyern yayi ya kalleshi, cikin rashin gamsuwa da kuma nuna shakka ako da yaushe yace.

“Ni kuma?”.

Da sauri Dr Lukman ya cire idonsa kan idon Rayyern ɗin tare da shakkarsa yace.
“Eh”.
“Gaskiya bansan da zaman ba, impact ma banida wannan lokacin.”
Ya k’are maganar agajarce yana mai duban agogon dake daure atsintsiyar hannunsa, hakanan yake Sam bayason wasa ko kuma raini.
Tabbas yana kiyaye kansa wanda kuma hakan d’abi’a ce dake cikin jininsa, awaje d’aya ne kawai zakaga murmushi da kuma fara’arsa, shine idan yana tare da Abbansa, Mamy da kuma Ramadan sai Baba Mauɗo, akasin haka kuwa Sam baya da sakewa da sauran wasu mutane, gentle mutum ne shi kuma straighforward, duk abunda ke bakinsa ya kuma san gsky ne shi yake fad’a, in ya ma daɗi ruwanka in kaji ba daɗi ma ruwanka.
Sam arayuwarsa baya ta'ammali da fad’an k’arya ko munafurci, hakan ba d’abi’arsa bace, then ba kuma ya shiga abunda bai shafe sa ba.

Lips Dr.Lukman yad’an cije cikin kuma lallab’awa dayin k’asa da murya, yace.
“Please Dr. dan Allah karkayi rejecting gayyatarmu, domin kuwa zama ne da za’ayi da shuwagabannin companies masu ci ayanzu, ba kuma wani jimawa za’ayi ba only 1hour ma yayi, dan Allah da Manzonsa Dr. Rayyern Mai-sanara ka samu ka halarta, koda ace na tsawon 30mn ne!!!”

Shiru yayi tare da d’an lumshe idanunsa, saboda gaba daya Dr. Lukman din ya kashe masa jiki daya ambaci sunan Allah.
Tabbas akan komai idan ka ambata masa sunan Allah to yakanji zuciyarsa ta sake.
D’an numfasawa yayi tare da bud’e bakinsa ahankali yace.

“Is alright ba damuwa zanje, yaushe ne taron?”

Cikin hanzari da kuma Jin dad’i Dr. Lukman yace.

“Yau ne kuma yanzu nima can na nufa Insha Allah, ko zamu had’a hanya sainayi maka jagora.”

Kansa kawai ya jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, direct ya nufi wajen motarsa, yana shiga kuwa Hadi driver yaja suka fice daga compound din wajen, ganin hakanne kuma yasa Dr.Lukman ma cikin sauri ya shiga motarsa ya rufa musu baya.

Kusan atare kuwa suka iso babban company’n, Dakata wanda yakasance kayan masarufi ake sarrafawa aciki, Tabbas company’n yana da girma kuma yana da kyau ba laifi, saboda ank’awata cikinsa da abubuwa masu kyau.

Saidai kuma ga mamakin Rayyern kwata kwata babu wasu ma’aikatan kirki aciki.

Haka dai Dr.Lukman yayi masa jagora harzuwa babban d’akin da sukeyin taro.
Koda ya shiga gaba d’aya mutanen dake wajen basu wuce su 18 ba, wanda kuma dukkaninsu suna zaune ne akan royal chairs.
Yayinda wani babban dogon table, wanda aka cika samansa da kayan drinks yayiwa gabansu k’awanya.

Akan daya daga cikin kujerun wajen Dr. Rayyern Mai-nasara ya zauna, wacce kuma ta kasance itace take facing na Barrister Kabir Saleh Dakata.

Agefensa kuwa Alhaji idi Sale Dakata ne zaune.

A hankali ya juyo ya kalli wani dattijon daya zauna ɗaya gefen nashi, Alhaji Abdu Tababa kenan.

Numfashi ya ɗan fesar tare da ɗan kallon Barrister Kabir Sake Dakata.
Wanda tun shigowar Rayyern d’in ya kasa d’auke idanu daga kansa, domin hakanan yaji idanuwansa nayiwa Dr. Rayyern d’in Kallon sani, yanaji ajikinsa kamar a wasu shekarun baya masu tsayi ya tab’a sanin the same irin fuskar na, saidai kuma to Fuskar waye? Waya sani mai irin fuskar?
Tambayar da bashi da amsarta, bashi kuma damai amsa masa haka yasa ya gaza janye idanunsa kan fuskar Rayyern yayinda yake motsa lips ɗinshi a hakali.
Shi kuwaRayyern ido ya ɗan zuba mishi a fakaice yana nazarto abinda ke zuciyarsa .

Gaggaisawa sukayi amutumce kafun daga bisani Alhaji Idi Sale Dakata.
Ya d’an muskuta ya gyara zamansa. kana yace.

“Toh Alhamdulillah domin kusan gabaki d’ayanmu munsan abunda ya taramu da kuma musabbabin had’uwar mu anan wajen.
Idan kuma akwai wanda zance baisani ba saidai wannan yaron wanda yazo yanzu.”
Ya fad’i maganar yana nuna Rayyern da hannu, cikin isa da gadarar dake bayyana cewar akwai wani abunda keyi masa suya a zuciya.

Wanda hakanne kuma yasa Rayyern dago kai, ya soma bin kowannensu da idanu, yana mai karantar labarin dake zuciyoyinsu akan fuskokin su cikin hikima, da kuma haɗawa da ɗan lbransu da ya sani.

Shikuwa Alhaji Idi Sale Dakata ci gaba yayi da cewa.

“kamar dai yanda kuka sani munzauna ananne saboda mu tattauna akan kasuwancin mu, sannan Rayyern kaida baka sani ba kasani, munyi wannan taronne nagamayyan manya-manyan company’s, saboda akwai buk’atar had’a kawunan mu, domin mu gudu tare mu kuma tsira tare bi ma’ana, mu had’e kasuwanci’n wuri guda mu haɗa hannu ta yadda zamu tsara farashin kayan abinci da sauransu a yadda mukeso..”
Ya dire ayar mgnar yana mai kallon.
Alhaji Abdu Tababa dake jinjina kai.

Kai Rayyern ya d’an girgiza tare da maida fuskarsa ya tsuketa waje d’aya, domin lokaci guda ya dawo asalin Rayyern Mai-nasara dinshi, hazikin matashin da bayajin shakka ko tsoron duk wani magauci’nsa ya rigada ya gama saninsu in and out yasan kowa yana da cikekken bayani kan kowansu.
Gyara zamanshi yayi tare da maida bayanshi ya jingina da jikin kujera,
Kana ya ɗan juya kanshi hagu da damanshi.
Muskutawa yayi ya maida kujerar baya kaɗan kana ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya sabida zogin da yaji yatsarsa nayi mishi dan toms ɗin dake ƙafarsan ya takure yatsar da Jannart ta fasa mishi, cikin zuba musu ido ya sauƙe sassanyan numfashi, tare da cewa.
"Kuyi haƙuri".
Yayi mgnar cikin mutuntaka da girmama su.
Cikin haɗe fuska Alhaji Yawale yace.
"A kan me? Me kake nufi da muyi haƙuri? Fito fili kayi mgn yadda zamu gane?".
Numfashin mai nauyi ya fesar sabida, sarawar da kansa ya farayi sabida yadda suke mgn da ƙarfi.
Cikin nitsuwa yace.
“Bana buƙatar had’a hannu daku a cikin kasuwanci na!!!".
Ya fad’i hakan in don’t care manner, domin iya gaskiyarsa ya fadi kamar yadda suka nemi ji.

Idanu suka zazzaro gaba dayansu.
Yayinda Dr. Lukman dake gabansa ta gefensa bisa hagu yace.

“Haba Dr.Rayyern ya zaka fad’i haka, agaban mutanen da yawancinsu sun haifeka, at least dai ai ya kamata ka daraja su ko dan sun fika gogewa a harkar tunda tun kan a haifeka suke juya kobo ta zama dubu...”

Wani irin kallo da Rayyern din ya watsawa Dr.Lukman d’inne yasashi saurin rufe bakinsa gum, saboda hatta hantar cikinsa saida yaji ta kad’a.

“Bazan had’a hannu dasu ba, na fad’a na kuma sake maimaitawa Ni DR. RAYYERN BASHEER MUHAMMAD MAI-NASARA bazan had’a hannu dasu ba!!!”
Ya fad’i maganar da muryar dake bayyana iya gaskiya, da kuma zallan rashin tsoro ko shakkar kowa dake wajen.

Gaba dayansu shiru sukayi sai Alhaji Ma’aji wanda yake da company'n Ma’aji and Sons ne ya d’an muskuta, tare da fad’in.

“Meyasa bazaka had’a hannu damu ba?”
Wayarshi ya ɗan zaro cikin aljihunsa kana ya ɗan danna kaɗan sannan ya medata cikin aljunsa tare da cewa.
"Awa ɗaya dana baku cikin ɗaƙiƙun rayuwata da Allah ya aramin, kunci 21mn saura muku 39mn, in kuma kun gamane zan tafi."
Cikin hatsala Alhaji Yawale yace.
"Toh meyasa kace bazaka haɗa hannu da mutane ba".
Juyowa yayi ya ɗan kalleshi kana yace.
“Sabida tafiyata da taku ba iri ɗaya bane.
Muddin muka ce zamu haɗa hannu, dole gefe ɗaya zai rinjayi ɗaya,
ta yiwu ku rinjayeni.
Ku ɓata min kekkyawan TUBALIn da aka ginamin.
Ko kuma Ni in rinjayeni in ruguza muku mummunan TUBALIn da kuka gina tun da daɗewa, in ɗauraku bisa tsarina wanda kuma nasan bazaku lamunci hakaba.
Dan haka muyi tafiyar a rabe shi yafi.
Domin ni dai a atafiyata talaka nake dubawa.
Ku kuma aljihunku kuke dubawa, ni kuma ba haka bace a tawa tafiyar, domin ahar kullum talaka nake dubawa, da rayuwarsu, manoman da suke noma abinci, su yake zuwa ya gagara yafi karfinsu, Yayinda ku kuma kunanan kuna juya abincin da suka noma da wahalarsu, yana zame muku manyan kud’ad’e, Sam baku damu da talakan daya noma abincin ko yaci ya koshi ba, ko bai cika wannan duk ba damuwar ku bace, saboda haka.
Bazan had’a hannu daku aci gaba da cutan talakawa ba, domin sudinma mutanene kamar kowa!!!”.

Wani irin murmushi mai cike da tarin ma'anoni Barrister Kabir Saleh Dakata yakeyi, yana mai kallon Rayyern ido cikin ido cike da alamun so, da kuma tsoro can ƙasan zuciyarsa.
Su kuwa sauran gaba ɗaya a hatsale suke

Cikin yanayi hasala Alhaji Idi Sale Dakata yace.

“Okay wannan dalilin shi yasa ka zagaya gaba d’aya, kan manyan manoman da ƙanana da suke sayar mana da abinci ka hanasu sayar mana, har sai sun gama sun ware wanda zasu ci kafun su kawo mana mu mu saya?.”

“K’warai kuwa hakane, saboda hakkinsu ne kuma guminsu ne, ya zama lallai tilas cutarwar da kukeyi musu ya isa haka, Manoma bawai bayinku bane, domin da ace babusu yau da dukkanku baku kai wannan matakin ba, har yaushe zaku daina ci gaba da cutan mutanen da suke taimakon ku?.”
Ya kai k’arshen maganan nasa, cikin wata irin Muryar dake bayyana, cewa a shirye yake da yayi fito na fito da kowanne daga cikinsu, Sam babu alaman tsoron acikin zuciyarsa.
Chapter 17 · 0% Book details