← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 180

Sashe 34

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cire mata karfen rigar ya yi tare da karisa saukar mata da rigar a jikinta, sannan ya sanya kyawawan hannayensa yana mai ja mata zip ɗin rigar sama kafin ya kama wannan ɗan karfen da ya saƙalo mata gashin kan nata ya haɗa shi da ɗan uwansa ya mannesu, dama kamar botir suke.

Da sauri ta juyo dan jin kamshin perfume nasa bai yi kama dana auta ba, bugu da kari kuma ba a amsa mata maganar da ta yi ba, da auta ce to tabbas zata amsa mata maganar tata.

Tana juyowa suka yi ido huÉ—u da Jawad, tsayayyen namiji mai jini a jika, matashi mai 25 years a duniya, É—a ne ga uncle Abbas, shi ne second born nasa, kyakkyawa ne sosai, ba sai na sake gaya maku ba, gabaÉ—aya Æ´aÆ´an Akka wato mahaifiyar king Zuhair, Æ´aÆ´anta kyawawane, haka zalika ma jikokinta, cikakkun larabawane jinin Modarawa, hakan yasa suke da kyau sosai kamar su suka yi kansu, sai dai wannan yafi wannan kyau, wannan kuma ya fi wannan haske, haka suke!.

Ɗan kasa kaɗan ta yi da kanta tana ƴan kame kame, dan duk a tunaninta auta ce, da ta san shi ne ba zata yarda ya saka mata kayan ba, wani tunani ne ya faɗo mata cikin ranta, yanzu shikenan Yah Jawad ya kalleta daga ita sai towel? Waye ma yasan tun yaushe yake wajen? Kila tun da karfen ya riƙe mata gashi yake kalleta.

Shiru ya tsaya yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, sai ma zura hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon suit dake a jikinsa, da alama daga office ya fito, dan shigar zuwa wajen aiki ne a jikinsa, white suit ce mai bala'in kyau, sai white cover shoe masu bala'in tsada a kafafunsa, daga ta ciki kuma safa ce baka, kyakkyawar bakin gashin kansan nan a kwance luf, ta gaba har gaban goshinsa, ta baya kuma har bayan wuyarsa, sai sheki gashin yake yi, ha sha gyara, ga wani daddaÉ—ar kamshin da yake zubawa.

Daga Akka har marigayi King ABDUL MALIK duk suna da tsawo sosai, hakan yasa daga Æ´aÆ´ansu har jikokinsu suke da tsawo sosai, so haka shi ma Jawad yake da tsawo, ga cikar kirar karfi na lafiyayyun maza.

"Yah Jawad ina wuni?".
Ta faÉ—a murya na kerma, dan ita tsoronsa ma take ji, saboda bashi da wasa da yara, kuma bashi da yawan magana, haka zalika sam bashi da fara'a ko kaÉ—an, wannan dalilin yasa suke jin tsoronsa.

Nisawa ya yi ba tare da ya amsa mata gaisuwar tata ba, sai cewa ya ya yi.

"Meyasa baki rufe kofar É—akin ba?". Kasa kasa ya yi maganar.

Cigaba da muzurai ta yi tana wani Æ´an kame kame, sam bata san lokacin da ta fara murza Æ´an yatsun hannunta ba, dan bata da abin yin da ya wuce haka.

"Am.... In... Dama na manta ne.... Kuma dama muna tare da auta ce, ta ce mun tana zuwa ne ta fita, shiyasa ban rufe kofar ba, dan ina tunanin zata dawo".
Yadda take magana muryarta na rawa, words ɗinta suna rarrabewa, hakan zai kara tabbatar maka da ba ƙaramin tsoronsa suke ji ba, dan fa da gaske ne bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa.

"Lafiyarki kam ko?". Ya tambaya yana mai cigaba da kallonta, ya ji ne sai famar in'ina take yi mashi a magana, sai ka ce ya ce zai zaneta ko wani abin, duk ta bi ta ruÉ—e mashi.

"Lafiya lou".

Ta bashi amsa still voice nata na kerma.

"Ina zaki je haka? And ina Akka? Dan na shiga É—akinta bata nan?".

Sai a lokacin ta É—an É—ago da dara daran idanuwanta a hankali dan ta saci kallonsa, jin bai yi mata tsawa ba, ya yi magana cikin sanyi murya, kuma bai ce ta yi laifi ba, sai hakan yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Ajiyar zuciyar da ta sauke sai da yasa shi ya É—an kara kwanto da kansa kaÉ—an yana kallon face nata, ya fita tsawo sosai, so a yadda ya tsaya a gabanta É—in baya samun damar ganin face nata da kyau, sai dai tsakiyar kyakkyawar bakin gashinta yake kallo.

"Akka ni ban san in da ta yi ba, É—azun dai na barta a cikin bedroom nata".
Ta bashi amsa tana lallaɓawa a hankali tana ɗago idanunta dan ta saci kallonsa, tana son ganin yanayin face nasa.

"Ke kuma nace ina zaki je haka?". Ya yi maganar yana É—an ja baya daga kusa da ita, saboda ya sami damar ganin face nata da kyau.

"Part na Mammie zan je, uncle Abbas zan je gani".
Ta bashi amsa dai'dai lokacin da take É—ago idanu zata saci kallonsa. Kash bata san cewa kallon face nata shi ma yake yi ba, hakan yasa tana É—ago kai suka yi ido huÉ—u da shi, karaf suka kalli juna cikin ido.

Da sauri ita ta yi ƙasa da nata idanun, shi kuma still dai yana kallonta bai cire idonsa ba, ga idanun nasa kamar na Akka, manya manya kamar ball.

"Bani wayarki". Ya faÉ—a tare da ciro hannunsa guda É—aya daga cikin aljihun wandon nasa.

A hanzarce ta miƙo mashi wayar, dama tana rike da wayar idan baku manta ba.

A hankali ya dawo da kallonsa a kan wayar da ta miƙo mashi. Ganin yadda hannun nata yake kerma ne yasa ya mayar da kallonsa a saman fuskarta.

"Lafiya kike kuwa?". Da mamaki É—auke a saman fuskarsa ya wurga mata wannan tambayar, dan yaga yadda hannun nata yake ta famar kerma.

"Lafiya lou nake wlh Yah Jawad".

Shiru bai sake magana ba, ya kai hannu ya karɓi wayar tata tare da juyawa cikin nutsuwa ya nufi waje da wayar.

Yana fita ta faɗa saman katafaren bed ɗin dake a ɗakin tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, hannunta dukka biyu tasa ta dafe kirjinta dake ta faman harba mata fat, fat, fat, saboda tsoro, sai ajiyar zuciya take saukewa, tamkar wadda ta sha gudu ta ƙoshi.

Ta É—an jima a haka kafin ta furta. "Ko me kuma zaka yi da wayata Yah Jawad?".

Auta ce ta shigo cikin É—akin bakinta a É—auke da sallama. Da sauri ta kariso ciki tare da hayewa saman bed É—in tana faÉ—in.

"Aunty Chuchu tashi kiji me daddy da uncle Abbas suka ce".

Miƙewa zaune ta yi tana faɗin. "Rabu dani auta, kada ma ki gaya mun abin da suka ce, dan yanzu ma zuciyata a kusa take, kina gaya mun wani abin na tsoro suma zan yi, yanzun nan Yah Jawad ya fita daga cikin ɗakin nan, ba jiya Aunty Sarina ta ce ya kwace mata waya ba? To nima yau ya kwace mun tawa, sai dai ni bai mun faɗa ba, ita kuma Aunty Sarina kin ji ta ce ya yi mata faɗa sosai a kan wayar".

Cikin halin nuna ko in kula Autar ta bata amsa da cewa.
"To shi Yah Jawad me zai yi da wayoyinku da ya kwace?".

"To ko zaki je ki tambayo mana shi ne me zai yi dasu?". Ta faɗa tana zuro kyawawan kafafunta kasan gadon, dan ta miƙe ta karisa shirinta na zuwa wajen uncle Abbas.

"Kai Aunty Chuchu rufa mun asiri, ni na isa in je in ce mashi me zai yi da wayarku ne? Dama dai uncle Taheer ne ko kuma su Yah Obaid".

"Saboda kin rai'na su Obaid É—in ba?".

Ƴar murmushi ta yi kafin ta ce. "Yah Obaid fa Momma ta ce shekaru biyun da suka bani ma bai cika biyu dai'dai ba, shekara ɗaya ne da wata takwas suka bani, yanzu su basu cika 13 years ba ai, ni kuma na cika 11 years".

Cigaba da yin shirinta ta yi tana faÉ—in. "E lallai auta kin girma, wato ji kike yi kusan É—aya kike da su ko? Wlh bari Omaid ya jiki, kin san halinsa da shegen son girma, ranar har da cewa ya yi wai ya girme ni".

Dariya sosai autar ta yi, Obaid and Omaid akwai shegen son girma kamar me, sai dai kuma kash sun yi rashin sa'a sune kanana, auta kawai suka fi shekaru a gidan, amma sai su dage su ce sun fi su Chuchu shekaru.

Ƙarisa shirinta tsab ta yi, sai ta fito a cikakkiyar jinin sarauta, ta ɗauko wani dankareran alkyabbarta fara tas ta ɗaura a saman doguwar rigar tata, ga rigar launinta baki ne, sai alkyabbar ta zauna sosai, ta yi kyau sosai da sosai. Feshe jikinta da daddaɗar Dubai perfume nata ta yi kafin ta fito da wani kyakkyawar tsadadden cover shoe na ƴaƴan sarakuna ta sanya a fararen kafafunta, cover shoe ɗin launin white color ne kamar alkyabbar jikinta.

Hular alkyabbar ta sanya a kanta kafin ta nufi hanyar fita daga cikin É—akin tana cewa auta ta zo su yafi wajen uncle Abbas.

Da saurin autar ta miƙe ta rufa mata baya. Elevator suka hau zuwa kasa. Suna sauka kasa suka nufi part na uncle Abbas ɗin, part ɗin yana ɗan gefe da nasu ne.

Ƴan'sanda da sojoji ne cike ta ko'ina a arear part ɗin, dan fa uncle Abbas babban ɗan siyasa ne wanda yake a matsayin vice president mai ci a yanzu, mulki a hannunsu take, kasancewar KINGDOM OF POWER tana da manyan ƙusoshin gwamnati da suka fito daga cikinta ne yasa masarautar ta kara karfin iko tare da karfin faɗa aji a duniya, dan babu wani gwamnatin da zai kawo masu wargi, dama can shi King Zuhair gwammati bata ishe shi kallo ba.

Duk in da suka zo wucewa sai sojoji da Æ´an'sandan sun sara masu, saboda kowa yasan su waye ne su É—in.

Kai tsaye cikin part É—in suka nufa, kowani kofa suka je sai É—an'sanda ya buÉ—e masu kofar, a haka har suka isa wajen elevator, nan ma wani É—an'sanda ne tsaye a wajen.
Chapter 34 · 0% Book details