← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 180

Sashe 153

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guyson da ya fi kowa tsantsara kwalliya a cikinsu yana kwance saman doguwar sofa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin, ita ma Sharifat tana cikin room É—inta tana tsantsara nata kwalliyar, ita kam sai murna take yi za'a yi walima.

Baki a ɗauke da sallama Ummie ta shigo cikin parlourn nasu. Dr Raj ne ya amsa mata sallamar. Cikin parlourn ta ƙariso, a saman sofan da yake fuskantar Bilal ta zauna.

"Good evening Ummie". Bilal ya faÉ—a yana kashe hasken screen É—in wayarsa domin ya bata attention É—insa.

"Evening Yah Bilal ya hanya ya kuma aiki? Hope komai normal".

Da yes normal ya amsa mata, sannan ya yi shiru.

"Ya baku fita zuwa hall É—in ba? Zaku fara halin naku ba?". Cewar Ummien.

Dr Raj ne ya amsa mata da. "Ummie kema dai kin san bamu son zuwa, tun da Abbie ya yi mana dole kuma sai an kusa tashi zamu je".

"Gaskiya a'a banyarda ba, kawai tun da kun shirya ku je, yana jiranku fa, nima can zan wuce sai na ji motsinku alamar kuna nan baku tafi ba shi ne na shigo, dan haka ku tashi kawai mu jera a tare, kun fa san Abbienku bashi da burin da ya wuce ya ganku a kusa da shi, nasan yanzu haka yana cikin damuwa na rashin zuwanku, yana son ya ganku kusa da shi yana nunawa abokansa ku yana kuma alfaharin yin hakan".

Ransu bai so ba, Dr Raj, Rizwan, Guyson and Bilal ɗin suka miƙe, basu son yin ja in ja da ita ne kawai yasa zasu je, shi kuwa Ramish da tun da ta shigo yake waya bai ko kalli in da take ba, sai da ta miƙe zasu fita ne ta ce mashi idan ya gama wayar ya biyosu fa, kada ya ce zai kwanta yaki zuwa dan tasan halinsa. Kai kawai ya gyaɗa mata alamar to, tare da binsu da waɗan nan dara daran idanun nasa.

Sakata a tsakiya suka yi suka nufi hall É—in. Shi kuwa Ramish ya jima yana magana da King a waya, da kyar suka yi sallama, da alama King É—in bai so su yi sallamar ne, sai dai Ramish É—in ya ce mashi. "Kai daddy gobe fa zamu zo, ka bari idan muka zo sai mu yi ta hiran, yanzu Abbie yana jirana ne fa". Da haka dai ya samu suka yi sallamar da kyar.

Yana kashe wayar ya É—aurata a saman sofa mai zaman mutun biyu, ya kuma ajiye cup É—in cappuccino dake a hannunsa a saman table, sannan ya nufi cikin katafaren room É—insa.

Jim kaÉ—an ya fito sanye da three cuter jeans trousers sky blue, sai wata farar shirt mai karamar hannu maras nauyi mai laushi sosai, ya cire suit É—in jikinsa, da alama ba zai je walimar ba kenan.

Wayarsa dake a saman sofa ya ɗauko ya nufi waje. Kai tsaye babban parlourn ya nufa. A saman sofas set da suke kusa da dining room ya zauna, sannan ya ɗauki wayar dake kusa da wajen na emergency ya kira masu aikin dake kitchen ɗin kasa suna girki. Bugu ɗaya aka yi picking call ɗin, dan already akwai wadda aikinta ne kawai ta zauna kusa da wayar, idan an kira ta ɗauka ta ji me ake buƙata, idan an gaya mata sai ta isarwa da masu aiki a kitchen ɗin saƙon abinda ƴan gida suke da buƙata, nan take su kuma ma'aikatan zasu karɓi umarni su fara aiki, wannan ɗaya ne daga cikin tsarin gidan Abu Abdussalam.

A takaice ya sanar da wadda ta ɗaga kirar cewa yana da buƙatar kayan marmari haɗe da ferfesu mai ruwa ruwa kuma mai zafi yana babban parlour. Already tasan wanda ya kirata, domin aikinta ne dama lallai ta tabbatar da ta riƙe muryar kowa, yana ɗaya daga cikin dokokin aikinta, kuma yau a kallah ta shafi shekaru 7 zuwa 8 tana wannan aiki, so ta san voice na kowa a cikin gidan, shiyasa na gaya maku Abu Abdussalam baya ɗaukar ma'aikata jahilai, sai waɗan da suka yi karatu sosai, dan ba'a saɓa mashi dokokin gidansa, sannan aikin gidansa yana buƙatar masu ilimi ne sosai. Tab irin wannan abu haka.....🤔

Cikin girmamawa ta karɓi umarninsa tare da sanar da masu aiki a kitchen ɗin ga saƙon Ramish nan, kuma jira yake yi, dan haka su yi sauri. Kitchen na gidan Abu Abdussalam kawai abin kallo ne, girmansa ya wuci tunaninku, ma'aikatan da suke aiki a cikinsa kawai zasu kai su 20, girki kala kala ake yi a kowani lokaci, kowacce da kalar abincin da take girkawa kuma da kalar aikin da take yi a cikin kitchen ɗin. Idan mace tana ta ɓangaren gas wata kuma tana ta ɓangaren freezers sai ka yi zaton ba'a waje guda suke ba, saboda girman kitchen ɗin, ratar da yake a tsakaninsu ba kaɗan bane, girma ne da kitchen ɗin sosai, tsakanin wajen jera pots da kuma wajen su baker ovens ma ba karamar rata bace ba, girman kitchen ɗin ya kai girman gidan wani ko in ce ya kai girman fili plot guda. emergency phones har guda biyar ne a kowani ɓangare na cikin kitchen ɗin, duk domin saƙon ƴan gida su faɗi abin da suke da buƙata a girka a kawo masu, abin fa ba sauki bane, Daular gidan Abu Abdussalam ya wuci tunaninku, maƙudan dukiya suke narkawa, albashin ma'aikin gidan a kowani wata ma kawai abin a saki baki ana kallo ne. Da yake dukka ƴan gidan manyan kai ne, duk shaggun masu maƙudan dukiya ne, hakan yasa suke pacaka son ransu, ga jiga jigan masu kuɗi su Ramish duk suna nan ai dole su more rayuwa son ransu...... Allah ka yi mana arziki mai albarka.

Ajiye wayar ya yi bayan ya isar masu da saƙonsa, sannan ya jingina kansa da jikin head na sofar, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa kamar mai jin barci. A can cikin hall kuwa sai jiransa su Bilal suke yi, kowa ya dake a saman nasa haɗaɗɗen sofa da aka kawata da kwalliya na alfarma kuma mai tsada, an tanadi waɗan na sofas ɗin ne domin family, sauran bakin da suka halarci walimar kuwa kowanne yana saman nasa sofar, sofas da aka tanadawa family a saman stage suke, na baki kuma a ƙasa.

Hall ɗin a cikin gidan yake, Abu Abdussalam yasa aka gina mashi ita domin yin walima ko wani taro nasa kamar dai yau, ba karamar dukiya aka narka wajen haɗa wannan hall ɗin ba, kamar ba za'a mutu ba, tsadaddun sofa set da ya zuba a cikin hall ɗin kawai kuɗinsu ya isa ya riƙe wani har karshen rayuwasa shi da iyalansa, amma duk shi a kan sofa kawai ya karar da kuɗin, ga kayan alatu da aka zuba domin kara ƙawata hall ɗin, kowani abu idan ka gani a cikin hall ɗin nan aka gaya maka kuɗinsa sai ka saki baki, gabaɗaya bangon hall ɗin ma na glass ne, abin dai sai wanda ya gani, dan faɗar tsaruwar hall ɗin nan da baki ma ba zai yiwu ba.

Sosai Leesharh tasha kwalliyarta cikin wasu dogon wando da riga, dama na gaya maku ita ma abokiyar son wando da riga ne, malesian dress ne, wandon yana da faɗi sosai kamar palazo, rigar kuma ya fitar mata da shape ɗinta, rigar zuwa gwiwanta ya tsaya, sai ɗan ƙaramin veils ɗinsa, sannan rigar yana da igiya ta wajen cikinta, ta ɗaure igiyar a baya hakan yasa rigar ta kara fito mata da shape ɗinta sosai, flat tummyn nan nata shape nasa ya bayyana sosai. Ɗaura veil ɗin a kanta ta yi ɗauri mai kyau, da yake chocolate color ce ita sai launin kayan da suka kasance red color ya yi mata kyau sosai.

Fitowa ta yi daga part ɗinsu domin ta je wajen walimar su rabawa baki drinks da abubuwan da suka da ce, already an shirya glass cups masu tarin yawa da za'ayi amfani da su a wajen, masu zuba lemuka a cikin glass cup's ɗin ma har sun fara aikinsu, masu jera glass cups ɗin a try bayan an zuba drinks ma suna nasu aikin, so su Leesharh kuma aikinsu kawai su ɗauka su rinƙa rabawa waɗan da suke zaune shiru basa motsa baki.

Kamar zata nufi ƙasa, sai kuma ta tuna to ai ita bata san ma a ina hall ɗin yake ba a cikin gidan, bata san ta wani bangare yake ba, hakan yasa ta yanke shawarar tunkarar room ɗin Sharifat ko zata sameta sai su tafi a tare, sai zuba daddaɗar kamshi take yi.

Kasancewar tasan babu kowa a cikin babbar parlourn ne yasa ta yi sallama a ƙasa ƙasa, kai tsaye room ɗin Sharifat ta nufa, sam bata lura da shi a parlourn ba, kasancewar tsakaninsu akwai rata sosai, sai dai kuma tasha madarar mamakin jin ƙamshi parlourn ya sauya daga yadda ta saba ji, kamshin perfume ɗinsa ya rinjayi na parlourn saboda karfin da perfume ɗin nasa yake da shi. Amma bata kawo komai a ranta ba ta wuce wajen Sharifat kai tsaye.

Tana tura kofar room É—in Sharifat, ita kuma Sharifat É—in tana sanyo kai zata fito kenan suka yi karo, gwara kansu suka yi ta yadda har sai da dukkansu suka furta wash da É—an karfi.

Baya kaÉ—an Sharifat É—in ta yi tana murje goshinta da Leesharh ta gwara mata kai. A É—an ruÉ—e Leesharh ta yi mata sannu tare da ja da baya ita ma.

Ba komai Sharifat É—in ta ce mata sannan ta É—aura da cewa. "Kin yi kyau sosai Leesharh, ke kam kowani kaya kika sanya sai sun yi maki kyau, wajen walima zaki je ko?".

Kai ta gyaÉ—a mata tare da faÉ—in. "E can zanje mu rabawa mutane drinks, sai dai ban san a ina wajen yake ba, kafin na gama shirina kuma su Radia sun tafi, shi ne nazo tambayarki wajen".

Nisawa ta yi kafin ta ce. "Can zan je nima, muje a tare". Ta kai karshen maganar tare da sanyo kai ta fito, tasha kwalliya sosai cikin abaya, ta yi rolling gyalen a kanta, ta fita É—as da ita abinta, launin navy blue ya yi mata kyau sosai dan tana da hasken fata.
Chapter 153 · 0% Book details