← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 180

Sashe 176

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyata ba zata iya jurar ganin tashin hankalin da waɗan nan ahalin suke ciki ba, bari dai na leƙa Dubai muga me yake faruwa a can, my people's yanzu littafin RAWANIN ZALINCI zai fara ɗaukar 🔥 dan yafi karfin ɗaukar zafi sai dai wuta, mun dai kusa isa ga RAWANIN ZALINCI da gaske!.

Second to the last page of book 1 my people's. 💘🔥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________52🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

A karo na biyu ma wahala Leesharh ta sha sosai wajen neman mai kai abinci, sai dai kuma bata ci nasara ba har yanzu, sake dawowa cikin É—akinta ta yi, a bakin gado ta zauna, uban tagumi ta buga tana tunanin mafita, mahaifinta ne kawai a ranta, shi kaÉ—ai take tunawa, ta ci burin yau ta yi magana da shi.

Sallamar Sharifat a cikin room É—in ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Da kallo ta bita, ta kasa iya amsa mata sallamar, dan hankalinta baya a jikinta, duk ta yi la'asar.

Kusa da ita Sharifat ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Leesharh Yah Guyson ya gaya mun kin yi kuka a kan wani abin ya shiga maki cikin ido ko?".

Kai ta gyaÉ—a mata alamar e haka ne. "Eyya sorry, amma kuma dan wani abin ya shiga cikin idanun ki hakan doesn't mean sakacin masu aiki ne, i told Yah Guyson kada ya ce laifinsu ne, kada a hukuntasu, be cause yau rana ce ta taro, baki dayawa sun zo, a wajen shige da fice ma za'a iya samin kwari ai".

Da sauri ta amsa mata da. "Yauwa Sharifat, even me abin da na gani kenan, please ki rarrasheshi kada ya ce za'a hukunta masu aikin nan, please ya yafe masu".

"Leesharh tell me the truth, what's wrong with you? I already saw many problems in your eyes, so please feel free and tell me!".

Tsuru tsuru ta yi da idanu, yanzu me zata ce da Sharifat? Ta tambayi kanta da kanta.

"Leesharh from which country you came here?". Ta sake jefa mata tambaya, Sharifat tana zargin ko Leesharh tana kewar iyayenta ne yasa take shiga damuwa haka, kamar dai yadda Guyson ya yi hasashe É—azun, suna ganin yarintarta sosai, suna ganin bata kai a rabata da iyayenta ba, shiyasa suke yawan tambayarta ko tana kewar iyayenta ne, basu ma san ita Leesharh ai ta jima rabonta da iyayenta ba, idan da sabo yanzu ta saba da kaÉ—aicinsu.

"Am from Nigeria". Ta bata amsa a takaice, ta yi maganar kuma kanta na'a ƙasa tana kallon ƴatsun hannunta. "Do you mean Nigeria African?". Ta faɗa tana zaro idanu alamar mamaki.

Kai ta gyaÉ—a mata alamar tabbatarwa daga Nigeria take. "From Nigeria you came here because of work? Kai dole ki yi missing na parents naki, dole ki shiga damuwa, but why your parents zasu yarda su barki ki zo nan aiki? Su ba zasu ji kewarki bane? And su basu ga akwai nisa bane?". Tana maganar still mamaki ne sosai a saman face É—inta.

Shiru ta ɗan yi mata, kamar zata fashe da kuka take ji, zuciyarta na yi mata zafi, Sharifat ta taɓo mata in da yake yi mata kaikayi, ta tuna mata da iyayenta, duk sai ta ji wani irin.

"Sorry ko Leesharh, dole ki rinƙa kuka na kewar parents ɗinki, in saya maki waya ki rinƙa magana da su dan ki rage damuwa da kewa?".

Sai a lokacin ta zaro nata idanunta da suka girmewa na Sharifat a girma, idan ta zarosu kamar ka ruga a guje. Ko me ta tuna sai kuma ta ɗan yi ƙasa da kai.

"Leesharh meyasameki kuma? Is there any problem again?".

Kai ta girgiza alama a'a babu komai. "Leesharh talk to me now! should I buy phone for you? Saboda ki rinƙa kiran parents ɗinki, I don't want to see you always crying and worried".

A takaice Leesharh ta ce mata. "I don't have anyone in my life, I don't have a mother and i don't have a father, they're not alive, they're all dead". Ta faÉ—a kamar zata yi kuka, kuma ta gaya mata hakan domin Sharifat É—in ta rabu da ita da zancen saya mata wayar nan, kada ta zo ta saya mata waya hakan ya zame wa babanta babbar baraza, dan masu nikaf basu bata damar yin amfani da wata waya ba bayan wanda suka bata, shi ma kunji sun gargaÉ—eta a kan kada ta kuskura ta kira kowa da shi, so hakan yasa ta ce bata da har da uba, ni da ku mun san iya mamanta ce kawai bata raye, amma ta haÉ—a harda babanta dan tsira daga wajen Sharifat kada ta saya mata waya. Tasan cewa duk abin da zata aikata a kan mahaifinta masu nikaf zasu É—auki fansa, idan ta yi kuskure babanta ne zai ji a jikinsa! Hakan yasa take taka tsantsan sosai!.

Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Sharifat ɗin na jin cewa bata da iyaye, Allah sarki duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ji ta yi zata yi ƙoƙari ta ɗauketa kamar yar uwarta dan ta rage mata raɗaɗin rashin iyaye, da yake ita da Guyson akwaisu da zuciyar zinari na tausayi sosai, ga hakuri kamar damo, basu da faɗa kuma basu son hayaniya, kowa ya zauna da su sai ya ji yana tsananin kaunarsu, saboda kyawawan halayensu.

ÆŠan matsowa ta yi ta rungumeta tana yi mata sannu a kan rashin iyaye. "As from today i am your sister kin ji? Sorry ko?". Ta faÉ—a tana mai kara jin tausayinta sosai.

Ita ma Leesharh ɗin duk jikinta ya yi sanyi, tana jin kaunar Sharifat ɗin tamkar ƴar uwarta na jini, saboda kauna da ta nuna ma, duk sai ta ji bai kamata ace ta yi abu komai ƙanƙantarsa dan ta cutar da bayin Allah nan ba, ita tama rasa a wani matsayi zata ajiye Sharifat da Guyson, babu ruwansu da girman kai, mahaifinsu yana da murya mai karfin faɗa aji kuma dole ayi abin da ya ce a faɗin ƙasar, ga ɗimbin dukiya da shi kansa bai san adadinsu, ga matsayi a siyasance, sannan ga matsayi a sarauce, ga tarin masu kaki kala kala a ƙarƙashinsa, duk wata kaki a faɗin ƙasar bata isa ta motsa ba ba tare da izininsa ba, karfin iko gare shi ba kaɗan ba, amma su Sharifat duk basu ɗauki hakan a bakin komai ba, abin duniya bata damesu ba, basu ɗaurawa kansu girman kai ba, Guyson kam ma ai shi ta ko'ina ma jinin mulki ne yake gudana a jikinsa, ta sama da ta ƙasa, amma babu ruwansa da girman kai ko kyamar talaka, yana son kowa da zuciya ɗaya.

A can wajen walima kuwa. Tun da suka je wajen Guyson yake ta ƙoƙarin dannar twins Obaid and Omaid, shi Omaid ma ya hakura ya barwa cikinsa abin da yake tunani dan gane da Leesharh, dama shi kun san ya iya takunsa. Obaid kuwa sarkin bakar zuciya, sai cika yake yana batsewa, shi lallai lallai dole sai Guyson ya yarda Leesharh criminal ce, har da wani cewa su basa hasashen abu kuma ya zama karya. Shi kuma Guyson ya ce sam ba zai yarda a kan ita mai laifi bace kuma abin zargi, saboda shi baiga laifin da ta yi masu ba, kuma shi ba zai yarda ya zargeta ba, ya kafe masu a kan lallai ita ɗin mai gaskiya ce, sune kawai basu sonta.

Tun da suka shigo wajen yayyun nasu suke yi masu kallon tuhuma except Abu Abdussalam da ya buƙaci su zo kusa da shi su zauna ya yi kewarsu, Abu Abdussalam yana bala'in kaunar Momma da King Zuhair, shiyasa yake kaunar ƴaƴan nasu.

Kusa da shi suka zauna cikin manya manyan ministoci da ƴan majalisu, Guyson yana ta gefen damansa, su kuma ta gefen hagu suka zauna, basu taɓa raba wajen zama, duk in da ka gansu a tare suke, kai su basu raba komai ma ba wajen zama kawai ba, in dai ba zaka basu abu a tare ba gara ma ka barshi, dan ɗaya ba zai karɓa ya bar ɗaya ba.

Abbie ne ya ce. "Guyson where's Ramish?" Ya yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinsa, yare biyu Abu Abdussalam yake ji a duniya, daga turanci sai larabci.

Cikin sanyin murya haÉ—e da nutsuwa ya ce. "Abbie wai kansa na yi mashi ciwo, he can't come here, dan kara mashi ciwon kai za'ayi da surutu, so ya kwanta".

Kallon Bilal Abbie ya yi. "Jeka duba mun shi, Dr Raj ka kula da lafiyarsa sosai".

Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su nufi hanyar fita. Tun da suka miƙe maza da mata kallonsu suke yi, ba dai haɗuwa ba kam, sun fito ba'a magana, kyau iya kyau. Shi kuwa Rizwan ya kafa kansa a kan waya yana chatting da Chuchu, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, ita kuma sai narke mashi take yi!.

Bayan anci an sha, kowa yasan da cewa lallai yau Abu Abdussalam empire ya zo, biki aka yi na girma da girmamawa, rakuma har biyar ma'aikata suka gasa, nama kamar hauka, da nama na magana yau da ya yi a gidan Abu Abdussalam, drinks da ruwa suma da sai sun yi magana, abinci kala kala, a yau ba wata ma'aikaciya ko ma'aikacin masu yin girki waÉ—an da basu ji a jikinsu ba, yau sun sha aiki sun kuma wahala, jiki duk ya yi tsami.
Chapter 176 · 0% Book details