Sashe 180
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Macen cikinsun lafiyayyar mace ce wadda da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ta karɓi horo iya horo bana wasa ba, macece amma damtsen hannunta kamar na Assistant commander wato HOORAIN, daga ganin wannan mayakiya ce ko dai wani abin makamancin hakan. Macen ce ta matso ta ɗauki Sweetie cak ta saɓa a saman shoulder ɗinta, da alama nemanta ne ya kawosu cikin wannan daji, duk yadda aka yi sun san face ɗin Sweetien kuma ita suke nema, dan suna ganinta babu wata wata suka nufeta, duk yadda aka yi ita ce dalilin zuwansu wannan dajin. (Da alama Sweetie ce zata kai mu ga RAWANIN ZALINCI)
Gaba da ita macen ta yi, waÉ—an nan zaratan mazan suka rufa mata baya, da alama itace shugabansu, kuma itace karama a cikinsu, duk sun fita shekaru, amma yadda suke yi mata biyaya sun yi mubaya'a zaka gane e lallai duk yadda aka yi ta fisu matsayi. Gata jajircecciya, daga gani jininta a tafashe yake.
Tafiya suka yi da Sweetien ta hanyar da suka fito, sai sambatu take yi tana kiran sunan Kamran da kuma Pretty, Allah sarki bata ma san wanene ya ɗauketa ba. Su kuma sam babu wanda ya ce mata ko sannu a cikinsu, kuma ba kayan mayaƙa ne a jikinsu ba bare muce mayakan da suke nemansu su da mum ɗinsu ne suka kamata, ko dai su ne suka sake yin ɓadda kama da fararen suit? To lokaci ne zai nuna mana koma su wanene.
A ɓangaren Pretty kuwa, tana tsaka da tikar gudu wannan damisa ta daka wani uban tsalle da nufin ta sauka a kanta, sai dai bata kai ga yin hakan ba Kamran ya shiga tsakaninsu, dan kuwa hanyar da Pretty ta biyo hanyar kogonsu ne, yana zaune a saman dutsen a waje suna hira da Mammarsa ya jiyo ihu tun daga nesa, ko ba'a gaya mashi ba yasan ita ce, dan muryarta hadda ya yi mata. A ɗari ya miƙe Mamma na kiransa amma ina, ko kallonta bai yi ba, da gudun gaske ya nufi in da ake ihu, to kun ji yadda aka yi.
Ai kuwa yana shiga tsakaninsu damisar ta sauka a kansa, rigizib ya zube ƙasa. Habawa hayke mashi damisar ta yi, kokawa da ita ya fara yi yana ƙoƙarin kwatar kansa, ita kuma damisar da waɗan nan shegun faratu nan nata duk ta farfashe mashi fuska, so take ta damki maƙogwaransa ta tsinketa ta kashe shi.
Ita kuwa Pretty da bata san ma da cewa Kamran ya zo ba, cigaba da tikar gudunta kawai ta yi tana ihu, a tunaninta damisar na binta, gudu take yi sosai har ta bar yankin mai gabaÉ—aya, ta yi nisan kiwo.
Kamran kuma gabaɗaya damisar ta gama da shi, ko motsin kirki baya yi, duk ta farfashe mashi fiska jini na malala, tana ƙoƙarin capko wuyarsa da bakinta dan ta ƙarisa kashe shi kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ɗaga kai sama ta kurma wani irin gurnanin azaba sakamakon wani irin kaifaffen wuƙa da Mamma ta caka mata a ciki.
Wani irin gurnani ta saki take da girgiza jikinta. Mamma dake tsaye a dake kamar wata commander mayaka ta fara kalla.
Ko alamar tsoro babu a fuskar Mamma, tana tsaye cikin jarumta, ko shakkar damisar bata ji ba, zuciyarta tafasa yake yi, wani irin bakinciki ta ji na jiwa É—anta ciwo da damisar ta yi, burinta kawai ta zo su gwabza ta kashe banza, dan ita ba yau ta fara faÉ—a da damisun dake cikin wannan dajin ba, kafin Kamran ya girma ta sha gwagwar maya kafin su shafa mata lafiya, so Mamma ta wuce tunaninku, ita kaÉ—ai tasan wacece ita kuma me yake ranta.
Kanta damisar ta yi cikin zafin nama. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta sunkuya ƙasa tare da daba mata wata kaifaffiyar wukar a wuya wajen maƙogwaranta. Kun san damisa da zaki taurin rai ne da su, basu mutuwa ta daɗi, dan haka suka fara kokawa da Mamma babu kakkautawa.
Ganin haka yasa Kamran ya lallaɓa da kyar da makyarkyata ya miƙe, yana ta layi ya fara nufar hanyar da take ta kudu domin neman Pretty, bawan Allah shi bama ta rayuwarsa yake yi ba, Pretty ce kawai a ransa. Ita kuma Pretty gabas ta yi, Mamma kuma na faɗa da damisa tana ƙoƙarin ƙarisa kashe ta, yau Rocky baya nan, su suke kwatar kansu da kansu, Allah sarki ga Sweetie dai an tafi da ita, ko su wanene?............ Wai yau ina wannan jarumin mai irin idon su Pretty wanda yake kawo masu ɗauki kullum ne?😥💔
To wannan shi ne sanadiyar rabuwar waɗan nan bayin Allah da suka shafi tsawon lokaci a tare, Sweetie, Pretty, Kamran, shin zasu sake haɗuwa? Ya Kamran zai yi idan aka ce yau babu Pretty? Anya zai iya cigaba da rayuwa? Kun san kaunar da take a tsakaninsu fa! Shin Kamran zai je neman babansa? Wanenen ma shi? Wacece Mamma? Ina mum twins ta tafi ta barsu a cikin wannan dajin? Su waye su Pretty? Suwaye suke neman rayuwarsu? Su waye suka biyo mamansu time da take da cikinsu? Meyasa su kaɗai ake da buƙata ban da mamarsu? Meyasa lokacin da aka biyota waɗan da suka biyota cikin nata kawai suke da buƙata? Ina babansu? Ina baban Kamran? Waye wannan jarumi mai irin idon Prettyn?
DUBAI. Menene makomar Leesharh? Shin asirinta zai tonu? Maganin me Ramish ya sha? Shin zai cutu da gaske?. Idan Allah yasa Leesharh ta gama aiki shin masu nikaf zasu cika alkawarin da suka É—aukar mata na haÉ—ata da babanta kuma su mayar da ita kasarsu? Shin da gaske Leesharh ita ta kashe mahaifiyarta? Idan ita ce menene dalili? Wacece ita ma? Ya makomar tsakaninta da Obaid a yanzu?
GIDANSU KHADIJAH. Menene makomar maman Zainab? Baban Zainab ya mutu? Ina Hauwa? Idan baban Zainab ya mutu ya maman Zainab zata yi? Zata tsira kuwa? Kisan kai ta yi kenan? Hukuma zasu barta?.
KINGDOM OF POWER. Nan ba sai na yi magana ba, cakwakiyar dake ciki ya wuce tunaninku, abin ya wuce zatonku.
Shin da gaske Sweetie ce zata kaimu ga RAWANIN ZALINCI? Suwanene waÉ—an da suka É—auketa? Ina kuma zasu kaita?.
Amsoshinku yana step two, yanzu zamu afka cikin labarinmu, kada ki bari a baki labari, labari ne da yazo da salo na daban, zalinci, cin amana, hainci, cutarwa, zanba cikin aminci, tauye yarda, tauye hakki, cin hakki, cin zarafi, mugunta, keta, da kuma zazzafar soyayya mai cike da kaddarori haɗi da nasarori da kuma fafutukan cikar buri. 500 Naira kacal kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI from step one to end, da 500 naki zaki cigaba da karatunsa cikin aminci da kwanciyar hankali, trust me ba zaki taɓa yin danasanin karanta littafin RAWANIN ZALINCI ba, zaki ilmantu matuƙa, zaki nishaɗantu matuka, zaki wa'azantu matuƙa, ku kunsan yadda alƙalamina yake, akwai tarin abubuwa a tattare da shi, ba sai na ɓata bakina wajen sake gaya maku ba.
Duk wadda ta shirya biyan kuÉ—in karatun littafin RAWANIN ZALINCI zata tura kuÉ—inta ta wannan account É—in 1882812910 Musa Fatima Zahra access bank. Sai ta tura mun shaidar biya ta nan. 08161390581, kina biya zaki afka cikin tafiyar nan, ayita dake, kada ki yarda a baki labari!!.
TAÆA KA LASHE STEP TWO🔥💔😥
KAMRAN AND MAMMA.
"Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza".
"But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tunkaresa!! Na kusancesa!!".
Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka mutu kamar dabba! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!".
"Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!".
Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!.
SWEETIE.🔥
"ÆŠago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki".
Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko É—igo.
"Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan.
Su waye su? Meyasa suka É—auketa? Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?.
Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?".
A fusace Delisha ta É—aga wannan katakon hannu nata zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!.
Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katakon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba.
Yar karar azaba ta saki kafin ta furta.............
Kai kai kai taɓa ka lashen ya isa haka my people's, sai dai mun haɗu a step two kawai, akwai cakwakiya over. Hanzarta ki biya kuɗin karatu dan ki morewa ganin wannan cakwakiyar!.🤸💃💃
Ƴan Niger kuma ban barku a baya ba, ku mun magana ta wannan numberta ɗin dan na gaya maku ta yadda zaku yi naku payment ɗin. 08161390581
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤