← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 180

Sashe 158

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙoƙarin kara mata wani marin Obaid sarkin saurin hawa ya yi, dai'dai lokacin Guyson ya iso wajen, ya fito daga cikin gida wajen Yah Ramish.

"Kai Obaid me ta yi maka zaka mareta?". Guyson ya jefa masu tambaya, while shi kuma Omaid ya riƙe hannun Obaid ɗin dan kada ya kara mata wani marin, yasan idan ya barshi ya kara mata to fa sai dai a kwasheta ranga ranga bayan ta zuba kashi da fitsari a wando.

"Yah Omar who's she?". Cewar Omaid. Omaid fa da kuke ganin nan ya iya takunsa, ya fi Obaid iya tsiya, sai dai shi yana danne zuciyarsa baya saurin hawa, baya yarda ransa ta ɓaci har zuciya tasa ya fita hayyacinsa, sarai yasan me yake yi, da ƙwaƙwalwarsa yake aiki over, ya iya takunsa sanka sanka, yanzu dai kunga shi Obaid har ya arzuƙa, dan sun yi magana bata amsa masu ba har ya fusata ya mareta, shi kuwa Omaid kun ga kamar ma bai san ana yi ba, saboda tsabar iya taku da basaja.

"Ayya she's our new house girl, sabuwar maaikaciya ce fa, kuma innocent girl ce, bata da hayaniya, kawar Lil sister ce ma fa". Cewar Guyson.

Kawar da kansa Obaid ya yi tare da sauke hannunsa daga yunƙurin kara mata marin da ya yi niyar yi Omaid ya tare, cikin ɓacin rai ya ce. "Wannan ba house girl bane ba, criminal ce maras gaskiya, she looks like green snake under green grass".

Omaid zai yi magana Guyson ya riga shi da cewa. "Anyway, koma dai menene kuzo mu tafi cikin hall, wai bama kunce ba zaku zo ba? Ya aka yi kuma kuka zo?".

Guyson bawan Allah, yasan da cewa halin kannen nasa sai su, shi sam bai ɗauki zancensu da wani mahimmanci ba na kiran Leesharh da green snake under green grass da suka yi, dan yasan su fa yaran nan sam sam basu son zaman lafiya, idan basu kaunar mutun ba kalar sharrin da ba zasu yi mashi ba, dan haka sai ya ɗauki abin a zaman cewa basu kaunar Leesharh ce kawai yasa suka laƙa mata wannan suna. Bai san sun fishi gaskiya ba, su fa jami'ai ne, yau tsawon almost shekaru 8 suna a special weapons and tactics academy, a matsayin horon da suke yanzu zasu iya gane ɓarawo cikin dubbannin mutane, horo mai rai da lafiya suke samu, ba makarantace ta kananan kai ba, kun san su kuma da basira, hakan yasa makarantar take alfahari da su sosai da sosai, su ɗin su kaɗai ne tamkar ya dubu a cikin school ɗin nasu. Shi kuwa Guyson da yake karatun computer engineering ina zai gane hakan? Ai babu wannan magana, ba abin da zai gane, su kam sun san duk wasu lago na mutun maras gaskiya.

Da kyar Guyson É—in ya iya jansu suka bar wajen, har suka bar wajen kuma Leesharh bata dawo cikin hayyacinta ba, ta maru kam ba karya, duk da take chocolate color sai da shatin yatsu biyar É—in Obaid ya fito ruÉ—u ruÉ—u a face É—in tata, ta ji hannun manya, wannan ma dan ba marin Omaid ta sha ba, da na shi ne ina ga suma zata yi ko mutuwa mai gabaÉ—aya, dan Omaid ya fi Obaid sanin gurbin mugunta, dama kunsan ko da twin's É—in a mahaifa guda suka fito ba daban daban ba dole É—aya yana fin É—aya wasu abubuwa, to Omaid dai ya fi Obaid wayo, iya shege, iya taku, zafin zuciya, iya sarrafa zuciyarsa, kai da komai ma.

Ta jima sosai a wajen kafin ta fara jin kamshin dawowa cikin hayyacinta. Sai a lokacin kuma ta iya durkushewa kasa a saman gwiwowinta a wajen ta saki wani marayar kuka, wani irin zogi da azaba ne yake ratsa kashi da ɓargon jikinta, har yanzu kuma ta kasa iya tantance wai Obaid da Omaid mutun biyu ne ko dai mutun ɗaya ta gani?.

Ta ɗauki a kallah tsawon good 30 mins s wajen kafin nan ta iya miƙewa tsaye, tana sharar kwallah ta nufi cikin gida. Allah sarki Jasra mai cewa Leesharh bata da saurin kuka to yau ta zo taga Leesharh na sharɓar kwallah kamar ruwan fanfo aka buɗe.

Elevator ta haye ta nufi sama, sai goge kwallar take yi amma yaki dakatawa daga zuba, zogin wannan mari nasa yaki sakinta, tunani take yi su waye su Obaid kuma?. Can zancen wannan matashiyar mata mai nikaf ɗin ya faɗo mata a ranta in da take cewa. "Akwai wasu twin's a gidan, kada ki yarda ki haɗa hanya da su, kada ki takalesu ko wata gardama ta haɗaku, saboda kaifin ƙwaƙwalwarsu zasu iya harbo jirginki". Tuna tattaunawarta da matar yasa ta fara zargin to ko sune waɗan da aka yi mata gargaɗi a kansu? In kuwa sune to ai ta kwaɓe aiki, dan kuwa ga shi dai gardama ce ta fara haɗasu, kuma tun da suka fara cewa suna zarginta to da wuya su kyaleta, idan ma basu fara yin practical na aikinsu a kanta ba... Akwai cakwakiya kam.

Tana haurawa sama ta nufi hanyar da zai sadata da part ɗinsu, tana tafiya zalo zalo kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Ramish da tun da ta ji ta sau ɗaya ɗazun ya tsaya mata a ranta. Waya yake yi cikin harshen turanci, da alama kuma da abokan aikinsa yake wayar, yana tsaye a gabanta in da take tunkara kenan, sai dai bata ƙarisa wajen ba, da alama wayar ce ta fito da shi daga babbar parlourn izuwa wannan waje.

Cikin hanzari ta ɗan ja da baya kaɗan ta laɓe wajen wani ɗan lungu na kusa da babban parlourn, tattara dukkan nutsuwanta ta yi ta kasa kunne tana sauraron abin da yake faɗa, ba wani gane turancin sosai take yi ba, amma Allah yasa yana maganar yana haɗawa da larabci, hakan yasa tana fahimtar abin da yake faɗa sosai da sosai, ta fahimci ina maganar tasa ta dosa.

NI KAM NA CE LEESHARH FA TA FARA AIKINTA KENAN, TO KAFIN MU JI ME RAMISH YAKE FAƊE BARI MU LEƘA SABON GIDAN BABAN KHADIJA MUGA ME AKE AIKATAWA SAI MU DAWO.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________47🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Ana dirama a wannan gida dai'dai gwargwado, domin kuwa Hauwa fa ita ce ta bawa maman Zainab É—akin da zata zauna, gini ne da baban Zainab ya yi ta gabaÉ—aya rufi É—aya, manya manyan bedrooms guda huÉ—u ne a cikin ginin, kowanne da toilet É—insa daga ciki, sai parlor a tsakiyarsu, akwai katafaren kitchen a cikin, kofar kitchen É—in yana ta wajen dining area. Daga waje ta baya kuma akwai Bq, ginin dai ya tsaru sosai, gini ne na zamani, kasa tiles sama pop, ga manya manyan Ac a parlourn da kowa room na gidan. Kitchen É—in ma already anyi fixing na komai, drawers É—in duk an yi fixing É—insu, harta gas da komai da komai an sanya.

Hauwa da kanta ta zaɓawa maman Zainab ɗakin da yake ta kusa da dining area, wai shi ne ɗakinta, sannan ta bawa su Zainab ɗakin da yake kusa da na mamar tasu wai shi ne nasu, sura room guda biyun kuma ta ce ɗaya nata ita da baban Zainab, ɗayan kuma a bar mata shi zata yi amfani da shi ba yanzu ba.

Nan fa maman Zainab ta ce bata isa ba, dan bata ga dalilin da zai sa ace Hauwa ce zata zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, kunsan mu fa mata haka halinmu yake, mun tsani muga wata macen tana nuna mana ta fimu iko da abin da muka san mu muka sha wahala a kansa, da farko maman Zainab ta ce zata danne zuciyarta ta hakura kome Hauwar zata yi ba zata kulata ba, zata kawar da kai, amma ina ba zata iya yin hakan ba, domin kuwa mu mata bamu da karfin zuciyar jurar ganin kishiya ta nuna ta fimu iko da komai na gida.........😌🙃🌝

Hakan yasa maman Zainab ta ce ina wlh Hauwa bata isa ta zaɓa mata ɗakin da zata zauna ba, ta gama shan wahalar baban Zainab ɗin, su juri wahala a baya domin su gina kansu rana tsaka kawai wata banza ta zo ta ce zata nuna mata ta fita iko da wannan ribar wahala da suka sha? Wlh wannan ne kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba.

Ita kuwa Hauwa ta ce yama yiwu ya gama. Baban Zainab wanda tun da suka shigo gidan ya kama hanya ya wuce room É—insa bai ma san me ake ciki ba, ya barosu a parlourn ne suna ta dirama. Cikin gatse Hauwa ta fara gaya mata magana.

"Wannan ɗakin shi na zaɓa maku, kuma a cikinsa zaku zauna, idan ba haka ba sai dai ku kwana a waje, dan ba zaku kwana mun a parlour bama, saboda wani lokaci tsakar dare ina fitowa mu ɗan yi hira da mijina idan barci yaki zuwa, so ba zaki kwana mun a parlour mu fito hira mu sameku ba, dan haka in baki son ɗakin da na baki ki san abin yi, ke bari ki ji ko shi kansa mai gidan idan na ga dama yau a waje zai kwana, kuma haka dole zai kwana babu yadda ya iya da ni, ni fa babu yadda kuka iya da ni, na zame maku ƙashin wuya, na fi karfinku sai gani sai hange daga nesa".
Chapter 158 · 0% Book details