← Book details Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 180

Sashe 127

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan zaro idanu maman Zainab ta yi tana kallon Hauwar da mamaki a saman face É—inta, shi kam baban Zainab ko gezau, bai ma É—aga idanu ya kallesu ba.

Maman Hanif wato kanwar maman Haidar ita ce ta ce. "Ke kuma wacece? Daga ina kuma?".

Kallon uku saura kwata Hauwa ta watsa masu kafin ta buÉ—e baki zata yi magana maman Haidar ta rigata da cewa. "Ke maman Hanif ai da baki bata amsa da baki ba, buge bakin shegiya ya kamata ki yi har sai ya fitar da jini, an gaya mata mu sha'anin yinta ne da zata nemi ta gaya mana magana ko ta yi mana rashin kunya?".

A walaƙance Hauwa ta basu amsa, dan dama a kule take da su har wuya, musamman ma maman Haidar, ta tsani matar sosai, tasan labarinsu dukka a bakin maman Zainab, tasan duk irin cin kashin da suke yi wa maman Zee ɗin, shiyasa ita ta ɗaura ɗamarar cin ubansu one by one, da gangan kuma dama ta zagesu daga shigowarsu, dan tana son su fara gwabzawa ne da su tun daga yanzu, duk sai ta saita masu zama tun da su basu da lissafi.

"Ke tsohuwar kokon giya dallah ki rufewa mutane baki, kada ki sake sanya mun baki a maganata, an gaya maki ni Aisha maman Zainab ce? Ba zan É—auki iskancin ku ba, yanzun zan sanya mata ta san matsayinta, bani da mutunci ko miskala zarratin kuma ban san hanyar in da mutunci take ba, dubeki wata a koÉ—e dake futu futu kin yi tsufar kokon giya, wlh na zabga maki mari idan baki mai da hankalinki ba, an gaya maki ruwa sa'ar kwando ce? Ke baki ga kalar ba? Na yi kala da waddan tsofaffin kokon giya zasu kawowa wargi ne? Yanzu zan sa ki gane annabi ya faku". Cewar Hauwa.
Yadda take magana tamkar wadda ake karantowa tana faÉ—a ko kuma wadda aka sanyawa battery, daga ji kasan wannan dama tun ainahi Æ´ar tijara ce, bala'i da masifa ya jima da samun matsuguni a wajenta.

Tsit maman Haidar ta nutsu, dama tsoron bala'i ke gareta, kawai dan sun rena maman Zainab ne yasa suke cin mutuncinta dai'dai gwargwado, amma banda haka mugayen matsorata ne, to yau dai sun sami dai'dai da su.

Maman Zainab kam sake baki ta yi tana ganin ikon god, ashe dama akwai abin da zai sanya maman Haidar yin shiru a duniyar nan? Wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta, duk iskancinta da balai'nta yau dai ga shi ta nutsu tsit ana kwashe mata albarka ba bakin tankawa. Babbar magana, ana dirama a cikin wannan gida.

Haidar dake a tsaye a bakin kofa ne ya yi kanta cikin fushi da nufin dukanta, a cewarsa bai ga dalilin da zai sanya ya tsaya wata ta tsaya tana gayawa mahaifiyarsa maganganu marasa daÉ—i son ranta ba.

Wani irin tsawa ta daga mashi wadda ya sanya shi jan birki babu shi, a walaƙance ta ce. "Dakata ƙaramin maras kunya, ai kai taka rashin kunyar nafila ce tun da iya nan gidan kawai ka iya baje ta, wlh idan ka yi kuskuren sanya hannunka a jikina duk danginka babu mai kwatarka, sai kun yi danasani mafi girma a rayuwarku".

Sai a lokacin baban Zainab ya saka baki a in da ya dakawa Haidar É—in tsawa da ya fita mashi daga cikin parlourn ko kuma yanzun nan ya canza mashi kamanni. Babbar magana, a kan Hauwa fa babu abin da baban Zainab ba zai aikata ba, lallai akwai rikici ba kaÉ—an ba.

Ba ƙaramin kara tsorata su maman Haidar suka yi ba na ganin yadda baban Zainab ɗin ya hayayyako masu dan kawai Haidar ya yi yunƙurin taɓa Hauwa, yana gani Hauwar ta ci masu mutunci bai saka baki ba, amma daga za'a taɓata ya wani hayayyaƙo masu kamar zai cinyesu ɗanye, lallai akwai matsala babba ma kuwa.

Ita kam maman Zee komawa ta yi saman sofa ta yi zamanta tare da buga uban tagumi tana ganin wannan cakwakiya. Tatas baban Zainab da Hauwa suka yi wa su maman Haidar, daga karshe baban Zee ya koresu ma daga cikin gidansa, basu kuma da zaɓin da ya wuce su tafi, dan kuwa a yadda yake ɗin nan tsab zai iya yi wa mace ɗan banzan duka, Allah ma ya rufa asiri basu zo da hajiyarsu ba, abin ya tsaya a iya kansu kawai, ai da anyi ba daɗi.

Haka suka kwashi jiki cikin ruÉ—u tare da mamaki haÉ—e da tunanin baban Zainab kam anya lafiyarsa kuwa, a haka suka bar gidan suka nufi gidan Hajiyarsu, dan su sanar da ita halin da ake ciki.

Ita kuwa Hauwa bata bar wannan gida ba sai da ta tabbatar ta ƙunsawa maman Zainab abin da zai hanata yin barci a yau, sannan ta ce da baban Zainab su tafi. Shi kuwa bawan Allah kamar raƙumi da akala haka ya bita zalau zalau suka bar gidan kamar yadda suka zo.

Suna fita maman Zee ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tun daga saman kujera ta zubo kasa saman gwiwowinta tana kuka, Khadija dake zaune komai ya faru a kan idanunta ne ta zo ta rungumeta tana rarrashinta ita ma kuma tana nata hawayen, abin gwanin ban tausayi.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Idan muka waiwaya Dubai kuwai.

GIDAN ABU ABDUSSALAM BIN BADEEN🔥🌼

Lest cut the story, tsawon wata guda Leesharh tana aiki a cikin wannan gida, amma kuma ko kusa ko alama bata samu ganin wanda ta zo aiki a kansa ba, wato Ramish kenan, bayan Ummie and Sharifa ma sai su Radia babu wani bakon fuska da ta sake gani a cikin gidan, abin ya ɗaure mata kai, ji take yi kamar ta tambayi su Radia ina Ramish yake kuma wanenen shi? Amma da yake bata saki jiki da su ba, bata shiga cikinsu, kuma tana tsoron su zargeta a kan wannan tambaya yasa ta ja bakinta ta yi shiru, kawai ta zubawa sarautar Allah idanu, amma kullum da wannan tunani take kwana, da shi kuma take tashi, ga wayar da aka bata kullum a kunne yake, amma babu wanda ya taɓa kiranta ko ya turo mata saƙo, waɗan da suka bata wannan aiki da alama sun san da cewa ganin Ramish da ido ma kawai ba ƙaramin aiki bane, shi ne yasa basu nemetaba tukunnan, da alama suna samun information a kan wani hali take ciki sosai ba tare da saninta ba, amma su waye masu basu information a kanta? Allah masani. ita dai a yanzu bata san a wani matsaya ma take ba baiwar Allah.

A bangaren shi kuwa Ramish yana nan a cikin gidan, sai dai samin damar ganinsa ne ba kowa ba, ko ita kanta Ummie tana fin sati biyu bata sanya shi a idanunta ba, ba wai kuma dan baya nan ba, no a cikin gidan yake kwana yake tashi, sai dai yadda kuka san wani aljani haka yake, tamkar yasan akwai mayunwatan kuraye dake farautar rayuwarsa a cikin gidan, bawan Allah nan baya tashi dawowa sai tsakar dare yake shigowa cikin gidan, duk balainka da nacinka baka isa kasan lokacin da Ramish yake fita ko yake dawowa ba, zaka iya zaman shekara guda a cikin wannan gida baka haÉ—u da shi ba, shi É—in ba kamar sauran mutane yake ba, and kuma ba shi kaÉ—ai bane, matasa ne su huÉ—u wadda dukkansu babu wanda ya kai 30 years a duniya, cikinsu kuma harda Rizwan yayan Yah Jawad, first born É—in uncle Abbas kenan, amma fa dukkansu kafin ka samu damar ganinsu wlh kana iya fin shekara a cikin wannan gida, su É—in ba mutane ne kamar kowa ba na gaya maku.

Wai wanenen Ramish? Bari mu É—an ji wanenen shi kaÉ—an wata kila zamu iya fahimtar dalilin da yasa ake nemar rayuwarsa ruwa a jallo.

Ramish dai ɗan King Zuhair ne ba ɗan Abu Abdussalam bin Badeen bane, yayan gimbiya Aneesa ƴar mamace uwarsu ɗaya, wato ɗan mama ne shi kenan. Ramish fa Special weapons and tactics. Wato SWAT, kuma shi ne operation lieutenant ɗinsu gabakiɗaya. Special weapons and tactics, ku daga jin sunan special kun san they're special ɗin ne da gasken gaske, su ɗin wasu irin jami'ai ne da ake basu horo na musamman fiye da duk sauran jami'ai da kuka sani, saboda su idan ka gansu a waje ma to fa abu ya lalace, sai special waje ake turasu aiki, ba kamar jami'an air force, jami'an soja, jami'an ƴan'sanda da sauran masu kaki suke ba, no su they're very special, da farko kasar America ce ta fara kaddamar da Special weapons and tactics, daga baya sauran manyan ƙasashe ta duniya suka kwaikwayesu suma suka kaddamar da su, aiki suke yi kamar agogo, ga ɗan banzan fikira dake garesu, ga zafin nama, cikin ƙanƙanin lokaci suke aiwatar da duk abin da zasu yi, ba iya karfin dantse ne kawai suke da shi dan an basu horo na musamman ba, no su ɗin aiki suke yi da kwakwalensu cikin kwarewa tare da tunani mai zurfi, duk fa idan suka yanke hukunci a kan abu to ko gwamnati bata ja da su, domin ansan gaskiya ce, suna da uban tarin makiya ta gabas da yamma kudu da arewa, saboda sun yi aiki tukuru, sun kashe iyayen wasu, sun kuma jefa iyayen wasu gidan prison, su fa har manya manyan ƙusoshin gwamnati basu bari ba, duk wanda ya keto ta cikin aikinsu to ba makawa zai jisa a in da sai ya yi danasanin zuwansa duniya, wannan takaitaccen bayani ne a kan wanene Ramish, sauran bayanai ya biyo daga baya, kada ku manta shi ɗin jinin Modarawa ne, ɗa ne ga King Zuhair. To amma meyasa ake farautar rayuwarsu har haka? Lokaci ne zai nuna mana komai.
Chapter 127 · 0% Book details