Sashe 139
Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya yi a cikin ransa yana faɗin Jawad ka cika cin zali sosai, dan kawai tana ɗaukar hoto sai ka kwace mata waya?. A fili kuma sai cewa ya yi. "Tom shikenan idan ya dawo maki da wayar sai ki karɓi numberta a hannunsa ko a hannun auta ki kirani da numberki".
Okey ta amsa mashi da shi tare da tambayarsa ina su Yah Bilal.
Cikin zolaya ya ce mata. "Bilal kawai kika sani ba?".
Da sauri ta fara girgiza mashi kai tare da cewa. "A'a nasan su Yah Ramish mana, nasanku dukkanku ai".
Nufar hanyar fita daga cikin room ɗin ya yi, jikinsa na sanye da farar arab jallabiya, dukkansu dai kalar Akka ɗin ne, kyawawan gaske, soft skin kamar madara, sai ka rantse da Allah basu fita waje, saboda yadda skit ɗinsu yake sun ji hutu sun ƙoshi.
Cikin zolaya ya sake cewa. "A'a baki sanmu ba kam, Bilal kawai kika sani, dan ga shi shi kaɗai kika tambayi ina yake? To ya baya ƙasar ya yi tafiya".
Murmushi kawai ta sakar mashi, dan tasan zolayanta yake yi, ai babu bambanci a tsakanin Æ´aÆ´an King, duk da cewa iyayensu basa shiri, to su dai basa faÉ—a, dan haka ita da yayanta Bilal da su Ramish Æ´aÆ´an mama duk É—aya ne a wajenta.
"Aunty Chuchu kizo mu tafi mana, Yah Rizwan kai da ka ce mun aiki kake yi É—azun shi ne kuma ka sake biyewa Aunty Chuchu ko? Idan ka biye mata ba zata barka ka yi aiki ba". Cewar auta dake dake a saman mirror chair ta gama gyara kwalliyarta, ita dai kafarta na mata kaikayi, su tafi kawai, burinta taga sun je wannan yawon.
"Auta ai chuchu ta rigada ta hanani yin aikin ma, baki ga ma na fito waje na bar aikin ba? Sai kuma dare zan ƙarisa, yanzu dai bari mu ɗan yi hira da ita ko my sister?". Ya faɗa yana tsare Chuchun da waɗan nan idanun nasa wanda da ka gansu ba tambaya kasan tsatso ɗaya suka fito da Jawad, dan kuwa wlh idanunsu iri ɗaya sak, kamar Akka ta samu sabo ta basu tsoho..........😅
Murmushi ta sakar mashi tana ƙoƙarin yin magana auta ta rigata da cewa. "Ni gaskiya Yah Rizwan ban yarda ba, nifa nagama shirina tafiya kawai zamu yi kace zaku yi hira? Wlh idan ba so kuke na fara kuka na kai karanku wajen daddy ba Allah ku bar hiran sai mun dawo".
"Wai ina zaku je nema?". Rizwan ya tambaya.
Chuchu ce ta bashi amsa da. "Nima dai ban sani ba, kawai Yah Jawad ya ce mu shirya mu same shi a part É—in Aunty MieMie....."
Katseta auta ta yi da cewa. "Wai dama Yah Jawad ya ce mu same shi a wajen Aunty MieMie ne kika zauna a nan ban sani ba, baki gaya mun ba, to ni dai na tafi". Tana kai karshen maganar ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga room ɗin mayafin kayan na jan ƙasa, ta tattaro ƙasan sket ɗin da hannunta ɗaya kamar dole.
Da sauri ita ma Chuchun ta miƙe tana faɗin. "Yah Rizwan in tafi ko?".
Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai tsareta da ido yana ta kallonta. Katse kiran ta yi ba tare da ta sake yi mashi magana ba. A hanzarce ta rufawa auta baya tana murmushi.
Kai tsaye ƙasa suka yi tare da nufar part ɗin Aunty MieMie, suna tafiya suna hira, kamar wasu taurari. A kan hanyarsu na tafiya ta wajen tsakanin part ɗin uncle Abbas da part ɗinsu suka ci karo da commander ZAFAR tare da Sadauki Hoorain da kuma wani jarumin mayaki ɗaya suna tsaye suna tattaunawa, da alama magana mai mahimmanci suke yi.
Cikin girmamawa Sadauki Hoorain da wannan mayaki suka ɗan dukar da kansu ƙasa tare da yi masu sannu, shi kuma commander Zafar bai duka masu ba, amma cikin mutunci ya yi masu sannu tare da tambayar ina zasu je?.
Chuchu ce ta basu amsa da cewa part É—in Aunty MieMie zasu je, ita kuwa Auta tuni hankalinta ya koma kan mutuminta wato Sadauki Hoorain, ta tsaya ne ma tana tambayarsa wai ina yake shiga ne kwana biyun nan bata ganinsa sosai?.
Cikin girmamawa ya yi ƙasa da kai, da wannan sanyayyar muryar tasa ya amsa mata da cewa. "Kece kika dai'na fitowa lambu ranki shidaɗe, shiyasa baki ganina, amma ina nan".
Kallon commander Zafar ta yi kafin ta ce. "Abbu kai ma fa na dai'na ganinka sosai".
Duk cikin masarautar kowa da commander Zafar yake kiransa, É—ansa Hoorain ne kawai yake kiransa da Abbu, sai kuma auta da take bin bakin Hoorain É—in, ita kaÉ—ai take bashi wannan darajar, shiyasa yake kaunar yarinyar, shiyasa shi ma Hoorain yake kula da ita sosai, tana da girmama manya.
"Gimbiya ina nan, kamar yadda Hoorain ya gaya maki ne, muna nan kece baki fitowa yasa baki ganinmu".
Hannunta Chuchu ta ja tana faÉ—in. "Ke idan mutun ya biye maki sai ki kwana a nan, wuce mu tafi, ke kowa kika gani sai kin tsaya tambayarsa ina ya shiga kwana biyu? Bayan kina kule a cikin room ta ina zaki gansu dama?".
Da kallo kawai su commander suka bisu da shi, auta tana son tsayawa ta ɗan yi magana da Hoorain and commander, amma Chuchu ta hanata, haka ta hakura ta bi bayan Chuchun suka nufi ɓangaren Aunty MieMie da mijinta kenan.
A babban parlourn kasa suka isko Aunty MieMie zaune a tare da Jawad suna tattaunawa. Aunty MieMie tana shirye cikin kayan sarauta kusan kamar kullum, ga alkyabbarta dake jan ƙasa a jikinta.
Suna shigowa suka haye jikin Aunty MieMie, har suna rige rigen kwanciya a kafarta.
"Ni ku tashi kada ku karyani, yanzu kun zama Æ´an'mata har ma kun kusa zama matan wasu". Cewar Aunty MieMie. Ta yi maganar tana kallon Jawad, da alama akwai abin da ya gaya mata dangane da chuchun, shiyasa da ta yi maganar sun kusa zama matar wasu sai ta É—ago tana kallonsa.
Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba.
"Ku tashi mu fita ta part ɗin Aunty MieMie nan, bani key ɗin motarki Aunty Babba". Cewar Yah Jawad ɗin, ya yi maganar kuma yana miƙewa tsaye.
"Ni dai ba zan bada key É—in motata ko guda É—aya ba, haka kawai za'a fitarwa da daddyna Æ´an'matansa waje bada saninsa ba, to sai dai a bani cin hanci ko kuma na tona asiri". Cewar Aunty MieMie.
Auta ce ta ce. "Aunty MieMie ni zan baki cin hancin kin ji? Please ki bamu kin motar mana, amma fa idan daddy ya kamaki kina karɓar cin hanci babu ruwana".
"Sarkin son yawo ba, da anyi hutun school ki ce Dubai, yanzu kuma a nan ma zaki fara ko? Bari daddy ya kamaku zaku yi bayani". Aunty MieMie ta faÉ—a tana kallon auta.
Dariya kawai suka yi ita da Chuchu, shi kuwa Jawad ya tsaya yana ta satar kallon Chuchun, a ƙagare yake Aunty MieMie ta basu key su tafi, dan ya fitar da su ya je ya yi ta kallonta a wajen, amma Aunty MieMie kuma ta tsaya tana ta wani ja mashi rai, ya sani da gangan take yi mashi hakan.
Sai da ta ja masu rai sosai sannan ta ɗauko mashi keys dayawa ya zaɓi guda ɗaya. A hanzarce ya wuce gaba yana cewa su zo su tafi.
Da sauri suka miƙe suka bi bayansa suna dariya, sai addu'ar Allah ya dawo da su lafiya Aunty MieMie take yi masu suna amsawa da Amin. Bayan sun shiga cikin motar ne ya tambayesu meyasa suka jima kafin su zo?.
Auta ce ta bashi amsa da cewa. "To ba Aunty Chuchu bace ta tsaya biyewa Yah Rizwan suna ta hira...."
Da sauri Chuchu ta tari numfashinta da cewa. "Waye ya fara yin hira da shi? Ba kece kika shigo mun room da wayar kuna yin video call ba? Ai kece nan kika zauna tun a room ɗinki kika rinƙa hira da shi, ni babu ruwana kada ki yi mun sharri, ina gaisawa kawai muka yi, kuma bai wuci 5 mins ba muka gama......".
Auta ta buÉ—e baki zata yi magana. Katsesu ya yi da cewa. "To dai shikenan ya isa haka, yanzu dai kusa seat belt É—inku zamu tafi".
Dukkansu gidan gaba suka shiga, da kansa zai ja su kenan. Ba ɓata lokaci ya tada motar bayan sun sanya seat belt ɗin, kai tsaye ya nufi tampatsetsan gate da zai fitar da shi daga ɓangaren Aunty MieMie, suka ratsa ta bangaren uncle Abbas sannan suka nufi katafaren gate one na kingdom ɗin.
Sai daÉ—i su auta suke ji kamar me, ya ji daÉ—i sosai shi ma na ganin suna a cikin farinciki har haka.
Suna fita daga masarautar Jaish ya kira shi a wayarsa dake hannun Chuchun. Miƙa mashi ta yi, kamar ba zai ɗauki kiran ba, sai kuma dai ya ɗauka. Daga ɗayan ɓangaren Jaish ɗin ya ce mashi ina yake ne?.
Shiru ya É—an yi kafin ya bashi amsa da baya nan kuma ya É—an yi nisa, uncle Abbas ne ya aikesa, amma ba zai jima sosai ba zai dawo.
Sosai Jaish ya yi mamakin jin hakan, domin ya gano karya yau Jawad ya yi mashi, daga yanayin maganarsa ya fahimci ba gaskiya ya faÉ—a ba, yasan halinsa sarai, tare suka taso.
"Jawad me kake ɓoye mun?". Cewar Jaish.
"Mekuma zan ɓoyemaka Jaish? Babu komai, amma meyasa ka ce na ɓoye maka wani abin".
Shiru Jaish ɗin ya yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Saboda ba gaskiya ka gaya mun ba shiyasa na ce me kake ɓoye mun? Kai kanka kasan ba gaskiya ka faɗa ba, kawai ka gaya mun ina kake?".
"Kai my blood kana saurin gane abubuwa, na É—an je wani waje ne to, but idan na dawo zamu yi magana".